Sashe 15
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ZAINAB sunyi candy, ita dai bata samu hutu ba ta fada
kacaniyar bikin ni'ima. Ranar Alhamis akayi
kamu, kuma dije ya cashe musu da kida, ranar
zainab ta ajiye ustazancinta tasha rawa. Da
daddare yunwa ta isheta, gata ba gwanar cin
abinci, daman ga abun ya hade ma da hidimar
biki. Tana cikin kawayen ni'ima da zasuyi kwanan
biki anata hira da ita, kowa sonta yake yi, suna
son hira da ita, don sha'awa take basu. Gata fara
kal kyakyawa, gata da fara'a ga ladabi, don
kowacce aunty take ce mata. Tace yaya ni'ima
nifa yunwa nake ji." tace baga tuwon shinkafa ba
da zafinsa? Tace tuwo yaya ni'ima, ai ba zan iya
ci ba." ta dauki wayarta ta buga, "hello, yayana
yunwa nakeji." ya hauta da fada, "don me zaki
zauna da yunwa? Cikin shagwaba tace, "to yaya
su basuda komai sai tuwo."
mintuna kadan sai gashi a gidan da youghot da
ice-cream, da kaji uku manya ya kawo mata. Ta
bude tana ci, ni'ima tace 'yar gatan yaya kenan."
sakina cikin kawayen ni'ima tace, yarinyar nan
kinaji da gata, irin wannan cima da kikeyi dole
kiyi ta faman kyalli, baki da matsala."
zainab tayi dariyarta mai ban sha'awa tace,
yayana ai shine babata, baya barina cikin
damuwa, suna cin nama da youghot da ice-cream
tana basu labarin yayanta da yanda take tsoron
shi da gudun bacin ransa. Da safe ta shiga gurin
babanta ya bata rubutun tsari da magani a dame
da kindirmo, da tsumi da zuma. Tun tana 'yar
shekara sha uku babanta yake tsumata da
magani, shi tausayinta yake ji, yana ganin tunda
ta rasa uwa ba mai kula da ita ta wannan
bangaren.
Kullum addu'arsa Alah ya bata miji na gari wanda
zai kula da ita, ya tallafi maraicinta. Washe gari
suka tafi gyaran amare, akayi musu dilka da
halwa, jikinsu ya rinka tsantsi da sheki.
Suna gidan kunshi haidar yayo mata waya, "hello
mazaje ya akayi ne? Nifa na matsu zeeytah so
nake kawai na aureki, zainab kaunarki tayi min
yawa, zainab yaushe zamu hadune? Yaushe zamu
ga juna?
Karka damu mazan jiya gobe kazo daurin auren
yayata saimu ga juna." yauwa zeeytah zan zo
miki cikin farar shadda da bakar dara, da farin
takalmi. Zansa babbar riga, zansa farin agogo na
azurfa da farin gilas. Tara da rabi zanzo, sannan
saura rabin awa a daura auren kenan, tunda
goma za a daura.
To naji dadi wallahi sai goben.
Ranar daurin aure zainab tagama tsara
kwalliyarta cikin wata dakakkiyar shadda mai
tsadar gaske da yayanta yayi mata biki, ta nada
dan kwalin kamar nadin gwaggwaro, tayi kyau
sosai.
Haidar yayo mata waya cewar ya iso yana dakin
saukar baki na gidansu, ta kara feshe jikinta da
turare ta fice tayi dakin baki. Tayi sallama cikin
sanyinta, ta hango bayanshi cikakken mutum mai
zati dakyan kira, irin mazan nan masu wahalar
samu. Kamar yanda ya gaya mata zaiyi shigarsa
haka ta gani. Tayi sallama tare da cewa hello,
haidar barka da zuwa.
Yana juyowa hanjin cikinta ya hautsina, nan da
nan ta dabarbarce ta nemi nutsuwarta ta rasa,
bakinta ya dabarbarce. Dakyar ta iya hada
sunansa ta fada, tace, yaya Aliyu!"
ta juya cikin gida aguje ta fada daki tasa kuka
tana jimamin meyake shirin faruwa da ita? Karfe
goma dai-dai taji an daura auren ni'ima da
hamza saurayinta. Dai-dai lokacin da aka sake
daura auren Aliyu da zainab.
Zainab bata karasa jiba ta yanke jiki ta fadi, inda
mansura ta sheko da gudu dakin data ga zainab
ta shiga tana cewa, "ni zaku yaudara ku ciwa
Amana? Yau zainab koni ko ke, saina kasheki
nayi maganin maciya amana." inda ta shaki zainab.
Zainab ta rinka kakari. Sadiya da ni'ima suka yo
dakin da gudu, suka cakumi mansura suka cillar
da ita gefe suna cewa, ke kada kiyi mana hauka,
'yar uwar tamu zaki shaka kina kokarin kashewa?
Umma ta shigo a guje ta dago zainab ta
rungumeta tayi dakin da ita. Mansura ta rinka zage-zage,
"ni za ayiwa rashin mutunci da tozarta na rike yarinya tun
tana 'yar shekara
takwas, sirrina babu wanda bata saniba, na riketa
kamar 'yar cikina, amma cin amanar da zai biyo
baya kenan ku aurawa mijina ita?
Ta rinka deban kayan wajen tana watsi dasu.
Sadiya tace mudai kiyi mana shiru kada ki bata
mana taro." ta kawowa sadiya duka, mutane
suka tare suna bata hakuri, amma tijara take tana
zuba ruwan rashin mutunci. Saida ummi tayi
waya gidansu babarta da yayarta suka shigo
suna tambayar meya faru? Mansura ta fada jikin
babarta tana kuka, tana cewa hajiya kinga
abunda suka yi min, kina kallon irin sakayyar da
sukayi min, du kyakyawan rikon dana ma zainab
yau sunga ta mike ta zama mutum, shine suka
aurawa Aliyu ita." ta karasa tana kuka. Hajiya da
saratu suka saka salati tare da cewar, amma
Aliyu da zainab sunci amanarki sun tozarta ki, sun
wulakantaki, amma kansu sukayi wa, yanda
sukayi miki Allah ya tozartasu, taho mu tafi, aure
ne bakya yi su rike dansu. Bayan zainab su kara
aura masa mata uku su zama hudu.
Daman munafunci daya sa aka kai miki zainab
din don ta gama ganin sirrin gidan, ta riketa
Amana tamkar uwarta, amma sakayyar da zakuyi
mata kenan. Don kanku ku rike Aliyu, Allah ya
bata wanda ya fishi, suka jata suka nufi nasu gidan sunata
sababi.
Tofa Littafi ya canja salo
[9:15AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**5 & 2**6