← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 44

Sashe 18

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bazan taba mantawa ba bayan mamanki ta haifi sadik da
faruk, tana so ta haifi 'ya mace, ita da Aliyu har nafilan dare
sun sha yi da rokon Allah ya bata 'ya mace mai hankali da
nutsuwa da hakuri da baiwar ilimi.
Saboda tunda na auri mamanku Allah ya hada jininsu da
Aliyu, komai nasa a gurinta yake.
Shawararsu daya bakinsu daya. Lokacin da mamanki ta
samu ciki kusan tare sukayi laulayin cikin nan, idan tayi
amai shi zai kwashe ya gyara
wajen, du abunda take son ci shine dan aiken
sayowa.
Ranar da aka haifeki kuwa kiri-kiri Aliyu ya hana
daukanki wai kada asa miki datti da ciwon jiki, du
sanda akace Aliyu ya samu hutu bashida wajen
tarewa sai wajen mamanki yana rainonki. Kina da
shekara daya ya shirya miki birthday. Kina kan
kafadarsa yana yawo dake. Lokacin da ya yanka
cake din yasa miki abaki aka dau tafi, yace Allah
yasa na miki na aurenmu watarana."
mamanki tace, "haba Aliyu, yaushe zakayi jiran
karamar yarinya haka? Yace wallahi mama tun
ranar da aka haifi zainab Allah ya dasa min
kaunarta araina, ni dai dan Allah mama inaso
kimin Alkawari zaki auramin zainab inta girma."
mamanki tace na dau alkawari, in dai har Allah
yayi kai mijinta ne, to ba mai aurenta sai kai, na
baka zainab tundaga yanzu ta zama taka.
To kinji yanda mahaifiyarki ta bawa Aliyu ke, tun
kina 'yar shekara daya. Abunda ya tashi aurenku
kuwa yanzu, yazo mana ne ransa a bace yace
"shidai dan Allah a taso da alkawarin mamanki a
aura masa ke, don yana tsoron samarin da suke
yi miki tururuwa, yaga har kin fara zance. Shiyasa
ya nemi alfarma a hade aurenku data ni'ima.
To yanzu mahaifiyarki tana karkashin kasa ta
rasu, baza kiyi kokari ki cika mata alkawarin data
dauka ba, kinfi so kita barinta da nauyi akanta?
Ta dago kanta tana kuka tace, daddy ko wane
irin alkawari mamana ta dauka akaina zan iya
cika mata shi, na hakura daddy. Kayi hakuri ka
yafe min bata maka da nayi." yace bakomai
zainab, tsakanina dake kullum sai albarka."
***** ****** ****
kwananta uku a asibiti aka sallameta, don taji
sauki. Amma du shigowar da Aliyu zaiyi tana
asibiti nan bata iya dago kanta ta kalle shi bare
tace zatayi masa magana kota gaisheshi,
kunyarsa take ji sosai. Bama inta tuna haidar
shine Aliyu, du tes din kalamomin soyayyar da ya
rinka turo mata da wayar da suka rinka yi ashe
du yayanta ne Aliyu, ita ya zata yi da wannan
abun kunya?
Ita kuwa mansura data ji zainab tana asibiti,
addu'a ta rinka yi Allah isa kada taji sauki a fasa
aurenta da Aliyu.
Da Aliyu yaje dadadare gidansu mansura zai
dauketa su tafi gida, sai tace ai ita ta gama
zaman gidansa, mayaudari maci amana, Allah ya
isa tsakanina dakai! Tunda kaci amanata."
abun ya konawa Aliyu rai, yace ni kike gayawa
wannan maganar? Tace ana gaya maka din
azzalumi! Yace to ya isheki, kada ki sake bakinki
ya kuskure ki zageni, zaman gidanku kuwa kiyi
tayi, randa kika gaji kya dawo." yaja motarsa ya
tafi ya barta nan tsaye.
Saboda kwanciyar zainab a asibiti, an fasa bikin
da kaisu acikin wannan satin sai asabar mai
zuwa za'ayi wuni akaisu dakin mazajensu.
Zainab ta zamo bata da sakewa ko yawan
magana, ko yaushe ka ganta tayi shiru tana
tunane-tunane. Aliyu daya fuskanci kunyarsa take
ji sosai, saiya daina shigowa inda take. Sai dai da
safe d daddare yayo mata tes yace kici abinci fa,
kinsan bana son zama da yunwa.
Ya karashe mata tes din da kalaman soyayya
masu sanyaya zuciya. Takan girgiza kai tace, "kai
namiji, ba ruwanshi da kunyar abunda yake so.
Wai yayanta Aliyu shine yake mata irin wannan
kalaman soyayyan, baya jin nauyinta bare
kunyarta.
Yaita aiko mata da cimarta ko yaushe, abubawa
da yasan tafi so,
suna zaune a falo ita da ni'ima, wayarta tayi
kara, ta duba ta gani saita kyaleta taita burarinta
harta gaji ta tsinke don kanta, amma sai aka
sake bugowa.
Ni'ima ta dago kai ta kalleta, tace ki dauka mana
dan Allah, nasan bazai wuce yaya ba." ta girgiza
kai tace bashi bane." ni'ima tace to ki dauka
mana."
ai ban san mezan ce masa bane.
Ni'ima tace ki gaya masa abunda ya faru kawai
kada yaga kin yaudareshi."
tana daf da katsewa ta dauka, a sanyaye tace
"hello! Daga can nura yace ai dole kiki daga
wayata, kunya ma ai ta isheki.
Wato zainab ina ganinki simi-simi kamar ma
hankali, ashe azzaluma ce ke, kin yaudareni.
Kinsan saurayinki ne aurenki zaiyi kika binneni a
cewar yayanki ne a hannunsa kike, ashe
masoyinki ne.
Zainab idonta ya fara zubar da hawaye, tace ba
haka bane, don Allah nura ka saurareni kaji.
Karaf a kunnen Aliyu daya shigo dakin a yanzu,
tuni hanjin cikin zainab ya hautsina, tuni ta rikice
ta kasa cewa komai, wayar tana manne a
kunnenta tanaji nura yana gaya mata
maganganu.
Aliyu ransa ya baci, ya rinka wani huci ya karaso
inda hankalinra ya tashi, ta rintse idonta tana
jiran saukar mari. Yasa hannunsa akan nata
hannun da yake kange a kunnenta, ya zare wayar
, ya daka masa tsawa kai wawa shasha! Kana
sane da matar aure kake waya? Wallahi kayi na
farko kayi na karshe...

Bakwa comments ko likes don haka zanyi daina wahalar da kaina may be littafin bai muku bane shiyasa nayi typing kadan ma.
[9:16AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**8, 2**9 & 2**10
Chapter 18 · 0% Book details