Sashe 11
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
kidan, babban kawar amarya tazo ta yi addu'a tareda yiwa bakin da suka zo barka da zuwa. Daga nan ango da marya suka tashi suka ja zugar kawaye da abokai suna biye da bayansu har wajen masu sabis. Kowa shiyake sabis din kansa. Zainab duk inda tyi idon mutane ne akanta, ita kallon ya isheta, don bata saba da irin wannan shiga ba, ta saba kullum tana hijabi, to ita abunda yafi damunta ma sha daya har tayi, tana jin soron yaya fa. Amma yaya sadiya da mijinta sunce har dakinta zasu rakata su bawa yaya hakuri.. Wata kawarta tazo taja hannunta, dole saita yi rawa. A hankali take juyawa, kusan maza hudu ne suka rufa kanta suna mata liki. Kamar daga sama yaya Aliyu ya diro wajen, saiji tayi an damki hannunta. Ta juyo a tsorace dan ta razana, ganin yayanta ya hade rai kamar wanda bai taba dariya, saita firgice ta tsorata. Ya funciki hannunta yayi waje da ita, ya bude mota ya turata ciki shima ya shiga. Ta takure a tsorace take, saboda tasan halin yayanta sarai, akwai zafin zuciya. Aliyu ransa ya baci sosai ganin maza suna yiwa zainab liki, ba dai sonta suke yi ba? Wani abu ya soki kirjinsa, ya rinka ganin bibbiyu a idonsa, yayin da motar ta fara tangal-tangal kamar zata kifa. Zainab ta fara salati ta baro kujerarta ta rungume Aliyu tana ihu tana salati. Tirkashi! Mu hadu a littafi na biyu, waishin menene ya soki zuciyar Aliyu? via #Justice_Hamzat [9:14AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**1 & 2**2