← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 54

Sashe 7

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa Dr tunda yaga Ameesha ta fito sai ya maida hankalinsa kacokan kan Ameesha yana kallon irin kyau da ta yi, yana jinjina k'ok'ari irin na Meena don yasan aikinta ne wannan. Sosai ya shagala har ya manta a wajen da yake sai da ya ji muryar Alhaji Taheer yana faɗin

"Dr ka tashi mana lokaci fa yana tafiya."

"To." Dr ya faɗa yana mik'ewa.

Gaba daya suma suka mik'e, daret wajen motoci suka nufa kusan duk bakin su dauke da addu'ar samun nasara, kai tsaye babban filin saukar jirgin saman suka ɗauki hanya, cikin mintina ƙalilan suka isa airport.

Ba su wani daɗe ba, suka gama duk wani shiga da fita har komai ya kammala, sai jiran a fara kiran fasinjoji Dr ne ya dubi Abba ya ce

"Abba zamu tafi a yi mana addu'an samun nasara." Cikin ladabi ya yi maganar.

"Allah ya taimaka Dr in sha Allah za'a samu nasara, nan da kwana huɗu zamu zo, Allah dai yasa a yi cikin a." Cikin kwantar da hankali Abba ya yi maganar.

"Allah ya kawo ku lafiya Abba." Dr ya yi maganar dai dai lokacin da aka fara kiran fasinjoji. Addu'a kawai su Ummi suke yi har da hawaye, musamman yadda ita Ameesha bata wani damu da abin da ake ba, ita dai tunda taga da Dr zasu tafi sai ko tada hankali bata yi ba, Dr yana daga masu hannu har suka shiga cikin jirgin.

Meena wani sabon kukan ta fashe da shi a fili take faɗin

"Allah kaba Ameesha lafiya, Ubangiji ka yaye mata wannan lalura." Ta ida maganar wasu hawaye suna zubowa.

"Amin." Su Ummi suka amsa, suna wajen har sai da jirgin ya tashi tukun suka dauki hanyar gida. Dr kuwa ko da suka shiga jirgin zama suka yi, ya dauko wani littafi yana karantawa, jingine Ameesha take da jikinsa har bacci ya kwashe ta, ko da yaga haka sai ya gyara mata kwanciyar, yana shafa sumar kanta wanda yasha gyara sosai Meena ta gyara mata sumar sai kyalli take, tafiya ce mai tsawo suka yi kafin suka isa Egypt.

Lokacin da jirgin ya sauka a *INTERNATIONAL AIRPORT CAIRO* Dr Asmad kallon agogon hannunsa ya yi yaga karfe biyu saura mintina goma sha biyar, akalla sunyi awa biyar da minti ashirin da biyu suna tafiya, yana rike da hannunta suka fito daga jirgin motar da zata ɗauke su a wajen suka sameta, da yake Dr sun yi musayar pic da Dr Ansar basu yi wahalar gane juna ba.

Gaisawa suka yi cikin farin ciki kamar sun daɗe da sanin juna sannan Dr Ansar ya umurce su da su hau mota, suna shiga direba ya ja bai zame da su ko ina ba sai *Steigenberger Hotel El-Tahrir* dake cikin birnin CAIRO, sosai hotel din ya yiwa Dr kyau repretion suka shiga inda aka basu makilin dakin, Dr Ansar har dakin ya raka su

"Dr ku zauna anan idan ku ka huta ku ka ci abinci zuwa 6:30 direba zai zo daukar ku." Cikin turanci yake maganar.

Gyada kai Dr Asmad ya yi tare da cewa "To muna godiya Dr." Murmushi kawai Dr Ansar ya yi ya ja masu kofar ya wuce. Ciki Dr ya shiga inda ya samu Ameesha kwance akan kujera three sitter, idonta lumshe kamar mai jin bacci zama ya yi kusa da ita yana faɗin

"Heartbeat kina Jin yunwa ko? Sorry yanzu za'a kawo mana abinci, tashi ki yi wanka." Ya ida maganar yana latsa wayarsa lambar Nenne ya kira.

"Hello Nennena fatan kina lafiya?"

"Lafiya lau Asmad kun sauka lafiya?"

"Alhamdulillah lafiya muka sauka, gamu a hotel ma."

" Masha Allah! Na ji dadin jin haka, Allah yasa ayi wannan aiki a sa'a ina autar Ummi?"

"Ga ta nan tana jinki Nenne."

"To ai shi kenan Allah ya taimaka."

"Amin." Dr ya amsa sannan suka yi sallama.

Number Abba ya Kira, nan ma sun daɗe suna hira kafin su kai sallama. Ya kira Hafiz Yana sanar masa sun sauka, ya dai yi waya da mutane da yawa.

Ameesha dai buɗe ido ta yi tana kallon sa, bata da alamar tashi, murmushi ya sakar mata tare da sa hannu ya dagota ta faɗa jikinsa, tsam ya rungume ta yana sunsunar wuyar ta, wata duniya Dr ya shiga mai cike da nishaɗi, kwankwasa kofar da ake ne yasa shi dawowa nutsuwarsa, kwantar da ita ya yi sannan ya nufi kofar tare da buɗewa. Abinci ne aka kawo masu, amsa ya yi ya shiga da shi, ajewa ya yi kan dining din dake falon ya matsa inda take kwance cak ya dauketa kamar wata baby bai zame ko ina da ita ba sai toilet, d kansa ya cire mata kayan jikinta ya mata wanka sannan ya fito da ita, shirya ta ya yi, kafin shi ma ya shiga.

Ko da ya fito shiryawa ya yi cikin kaya marasa nauyi, kamar yadda ya sawa Ameesha itama, sallar azahar suka gabatar, rike da hannunta suka nufi falon ya zaunar da ita, abinci ya soma bata sai shagwaɓe masa take a haka har ta koshi bayan ta koshi ya fara ci shima, ko da suka gama toilet ya kaita ya wanke mata baki da suka fito basu zame ko ina ba sai kan gado.

Rungume Ameesha Dr ya yi kamar wani ya ce zai raba su, a haka bacci ya dauketa mai dadi farin ciki ne ya mamaye Dr ganin yau gashi ga Ameesha a gado ɗaya yana rungume da ita, hamdala ya yiwa Allah yana fatan Allah ya nuna masa ranar da zasu kasance tare tana cikin hankalinta, kara manna ta da jikinsa ya yi kafin shima bacci ya kwashe shi.

Ba su farka ba sai shida saura minti goma, da sauri ya sauka a gadon, tashin ta ya fara yi, da kyar ta iya bude ido don har a time ɗin bacci ne a idonta.

Alwala ya yi ya taimaka mata ta yi sannan suka gabatar da la'asar, falo suka koma ya kunna masu t.v suna kallo, karfe shida da minti sha biyar Dr Ansar ya kira wayar Dr yana sanar masa da su sauka kasa motar asibiti tana zuwa, tashi ya yi ya canza kayan dake jikinsu kafin ya ja hannunta suka sauka.

Ko zaman minti biyar basu yiba sai ga motar ta iso, shiga motar suka yi sai asbitin *AS-SALAM INTERNATIONAL HOSPITAL*, cikin mintina ƙalilan suka shiga asbitin babba ne sosai iya haɗawa ya hadu, duk da girman asbitin amma babu wasu mutane dai ɗai ɗaiku, domin dokar asbitin mutane basa zama, ana yin parking kafin su fito har Dr Ansar da wasu likitoci sun iso wajen motar.

Cikin girmamawa da mutunta juna suka tarbe su, cikin asbitin suka shiga, bayan kara gaisawa ne Dr Ansar ya bukaci Dr Asmad ya yi masa bayanin ciwon Ameesha, take ya fito masa da duk wani fayal da ya shafi ciwon, amsa ya yi ya duba, sannan ya dubi Dr Asmad ya ce

"Wannan ciwon yana da saukin warkewa a wajen mu amma da yaddar Allah, yanzu zamu fara mata gwaje gwaje sai musan matsayin da zamu taka."

"Allah ya taimaka ya bamu sa'a."

Dr ya faɗa yana ji cikin zuciyarsa kamar Ameesha ta samu lafiya, Dr Ansar yana gaba su na binsa a baya tare da wasu Nurse har wani daki mai cike da na'urori wani riga aka ba Ameesha ta sanya, da taimakon Dr ta sanya wajen shiga da ita ciki sam taki yadda a dole sai da Dr aka shiga, abin da yasa aka bar Asmad shiga don shima ya kasance likita ne kuma Dr Ansar yasan matsayin Ameesha a wajen Dr Asmad shi ne dalilin barinsa shiga ciki, wasu na'urori aka sanya mata akai ya yin da Dr Ansar ya koma wajen computer dake nuna cikin kan Ameesha. Dr Asmad da wasu manyan likitoci suna kallon computer.

Dai dai kan wani abu, wani ɗan alama ya tsaya sai mutum ya zuba ido da kyau zai iya fahimtar menene a wajen, juyowa Dr Ansar ya yi yana kallon sauran likitocin ya tsaida kansa a kan Dr Asmad.

Ya ce

*Wai wallahi na gaji ku yi hakuri da wannan i hearttttt you all SANGARTA FANS*

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:15 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*33*

"Dr ka kula da menene a wajen ca." Ya yi tambayar idon akan Asmad.

Dr Asmad bai kalli Dr Ansar ba idonsa yana kan computer yana nazarin abin dake k'wak'walwar Ameesha, kusan minti biyu tukun ya sauke a jiyar zuciya ya ce

"Dr duk iya nazari na ban gane ko menene ba." Har a lokacin yana kallon computer.

Murmushi kawai Dr Ansar ya yi yana zomming na pic na photo, sai ga wajen ya fito fes, zaro ido Dr Asmad ya yi cike da mamaki ya ce

"Da fatan yanzu ka ga komai?" Ya yi maganar yana ci gaba da daddana wa.

"Yes! Dr na ga komai har na gane abin da ke wajen."

"Me ka gani kenan?"

"Jini ne kwance a wajen, ga shi nan." Dr ya yi maganar yana nuna cikin computer.

"Tabbas jini ne ka duba da kyau yana motsa wa daf yake da gangarawa cikin k'wak'walwar ta, kuma da zarar ya ida shiga babu tantama haukace wa zata yi."

"What! Dr ya faɗa da karfi.

"Yes! Abin da na faɗa ma gaskiya ne, domin wannan ciwon da kake gani ba karamin illa garshi ba, AMNESIA babban cuta kenan sosai yake mai da mutane mahaukata amma ita nata da sauki kawai manta baya ta yi sakamakon wannan jinin dake cikin k'wak'walwar ta, amma da zarar an cire shi tunaninta zai dawo, sai na yi mamaki da duk fayal din da ka kawo babu mai makamancin irin wannan, mu kuma a binciken farko mun gano asalin inda matsalar ta ɓullo."
Chapter 7 · 0% Book details