← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 54

Sashe 14

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya dawo da ke lafiya, amma ki sani karki kuskura ki tuka mota da kanki." Yana maganar ne yana kunna motar, ko kafin Ameesha ta yi magana sai ganin motar Abba suka yi.

Cikin sauri Dr ya fito yana gaida Abba cikin yanayi me nuna alamar jin kunya, Abba ya amsa cikin sakin fuska yana tambayarsa su Bobbo

"Duk suna lafiya." Dr ya bashi amsa, kanshi a kasa.

"Naji daɗin zuwanka domin tun jiya naso kiranka, akan ka fara shiri uwata ta tare a ɗakinta, zamanta haka babu amfani, kamar yaushe kake ganin zata tare ɗin?"

Shiru Dr ya yi, har yanzu kanshi a kasa, bai nuna alamar zai yi magana ba. Duk dai a zuciyarshi
Sosai ya ji dadin maganar Abba, don dama haka yake so kuma ga damar ta samu.

"Ko akwai matsala ne?" Abba ya tambaya gani shirun ya yi yawa

Har yanzu kanshi a kasa yake, yayin da ya kai hannunshi yana shafo kanshi

"To Abba, amma akwai wasu yan gyare-gyaren da zan yiwa bangaren ta, nan da sati biyu zafi kyau." Cikin ladabi ya yi maganar.

"Allah ya kaimu." Daga haka suka yi sallama.

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty*

*39*

Gida kai tsaye Dr ya nufa, bayan ya kira Hafiz ya sanar masa, yadda suka yi da Abba, cikin kwanakin sam Dr baya samun zama domin aikin da akewa sashin Ameesha, suma a bangaren Nenne da Ummi abin haka yake, Ameesha tana ta shan gyara, wata mata aka dauko mata musamman domin ta gyara ta.

Shirye-shiryen biki ya kankama yau saura kwana biyu tarewa, duka gidajen biyu cike yake da mutane wanda suka zo domin taya su murna, sosai Dr ya yi bajinta wajen haɗa mata akwatina. Aneesa kam idan hankalinta ya yi dubu to fa a tashe yake, musamman da taga irin kuɗin da Dr ya kashe wa Ameesha, duk sai ta ji ta raina kanta. Cikin tashin hankali ta dauki waya ta danna Number din Rukky ringing biyu ta dauka

"Hello Rukky! Aneesa ta faɗa cike da tashin hankali.

"K'awata lafiya kuwa na ji muryar ki a haka?"

"Babu lafiya kam domin jibi matar Hamman zata tare, kin ga irin kuɗin da yake kashe mata kuwa?"

"Ina zan sani ina Adamawa kina Kano?" Rukky ta faɗa.

"Wallahi kuwa Rukky, wallahi ina cikin tashin hankali, Please ki bani shawara."

"Kin ga Aneesa kwantar da hankalinki, ki bari ta tare sai asan yadda za'a yi, amma ki fito fili ki nuna masa fushinki."

"Hmmmm! Rukky kenan wai kina ganin Hamman yana wani damuwa ne idan yaga ina fushi?"

"Ko baya damuwa ki nuna masa."

"To shi kenan zan jaraba, zaki ji komai." Daga haka suka yi sallama, ita kam Aneesa ta ci gaba da kai komo tana neman mafita.

Wow gaskiya bangaren da za'a sanya Ameesha ya haɗu sosai, tuni aka kawo kanya daki an daka komai sai jiran zuwan amarya, Dr kam cike yake da farin ciki, ko yaushe fuskarsa ɗauke da murmushi.

Dinner kawai suka shirya, wanda za'a yi ranar tarewar, Dr ya yi gayyata sosai musamman abokansa da abokan aikinsa na kasashe daban daban, ciki har da Dr Ansar wanda ya taso takanas don hidimar bikin Dr Asmad, ya samu tarba mai kyau daga Hafiz domin shi ne ma masaukin baki, kuma babban abokin ango.

Abba, Bobbo da Dr, sai Hafiz angon wata dakakkiyar shadda suka yi, zanenta iri ɗaya da ta su ya Jaheed sai dai kalar ya bambanta, karfe uku aka tashi daga walimar da Bobbo ya haɗa don farin cikin Auren Asmad

Nenne da Bobbo suka zaunar da Dr suna masa nasiha akan ya riki matansa cikin amana da adalci

"Kana jina ko Asmad? Ina so ka sanya hakuri da juriya da kai zuciya nesa a cikin zamantakewar ku, ka kasance mai adalci tsakanin matanka, ka zama tsayayye namiji mai mulkar da adalci."

"In sha Allah Babbo zan yi amfani da duk abin da ka faɗa min."

"Allah ya maka albarka, Ubangiji ya baka zuri'a dayyaba."

"Amin." Dr ya amsa.

Ita ma Nenne haka ta yi masa nasiha mai tsuma zuciya, kafin suka sallame shi. Komawa cikin abokansa ya yi inda aka ci gaba da harkoki.

Ameesha da Dr Asmad yau ranar ta kasance ranar farin ciki ne a gare su, kallon fuskarsu kawai zai baka tabbacin haka, sanye take ciki wani rantsattsen lacce mara nauyi, wanda ya yi mugun amsar jikinta fuskar nan ta sha meka'up har wani kyalli take, duk inda ta gifta sai kamshin turarenta ke tashi, kawaye ta duk sun halarci taron tarewar ta, ciki har da Ni'eema sosai Ameesha ta yi farin cikin ganin ta.

Liyafa sosai aka hada, an ci kuma an sha, an dauki hotuna domin tarihi kai abin dai gwanin sha'awa cikin lafiya da salama aka gudanar da taron, karfe biyar Abba da kansa ya kai Ameesha gida Dr bayan tarin nasihar da tasha a wajen Ummi da Abba, kuka sosai ta yi har idonta ya yi jawur.

Ko time da Abba yasata cikin ɗakinta sai da ya kuma mata nasiha, mai sanyaya zuciya, kafin ya yi mata sallama, shiru ta yi zaune cikin dakin ita ɗaya hawaye suna zubowa daga cikin idonta, maganar Abba ta karshe ita ta kuma sanyaya mata jiki

*"Uwata ki sani ni da kaina na kawoki gidan aurenki, duk ranar da kika fita daga gidan nan da sunan ya ji karki kuskura ki nufo gidana, domin nan shi ne gidanki marufar asirin ki, mutuwa kaɗai nake fatan ta rabaki da gidan nan, Allah ya maki albarka."* Cikin murya mai kamar ta kuka ya gama maganar, don taga lokacin da yasa hannu ya share hawaye.

A fili ta furta "In sha Allah Abba zan yi maka biyayya." Ta yi maganar tana share wasu hawaye da suka zubo. Sai kuma ta tuno nasihar Ummi, kamar yanzu take mata maganar

"Ameesha ki kula da jinsa, ganinsa, da kuma dandanon mijinki,

*1 karki bari ya ji wani abu da daga hankalinsa, ko ta tsaftar jikinki, jikinki ya kasance ko yaushe cikin kamshi na turaruka, haka falonki da ɗakunan baccinku, bakinki da duk wani lungu da sako na jikinki*

*2 ma'ana karki bari yaga wani abu da zai bata ransa akanki, musamman ta bangaren gidanki ko jikinki*

*1 karki kasance kullum cikin girka masa abinci kala ɗaya, a'a ko wacce rana ki yi masa kaloli daban-daban kuma ba guda ɗaya ya ba ki yi hakuri da biyayya, karki kuskura ki bijirewa umarninsa domin aljannarki tana karkashin kafarsa, duk maganar da zaki yi masa ta zama cikin tsusasa murya da nutsuwa, in sha Allah matukar kika lazumci yin haka zaki ci ribar zaman aure.*

Tana cikin wannan tunanin ne ta jiyo motsin mutane kamar a falo, ko kafin ta yi wani kwaukwarar motsi har sun shigo bedroom din, muryar Aunty Saude k'anwar Ummi ta ji, ai da sauri ta daga gyalen ta sauka a gadon tana faɗin

"Sannu Aunty dama yanzu nake tunanin ni kadai a gidan har tsoro ya fara kamani."

"Nima Aunty Halima ta sanyamu zuwa, don ta ce bata son abarki ke ɗaya, nan da wasu awanni idan zaku je dinner zamu koma."

"Ai kam na gode wa Ummina." Hira suka shiga yi da Aunty Saude har lokacin da Dr ya bugo mata waya akan ta shirya, mai mata kwalliya zata shigo don yi mata

"To." Ta amsa tana gyara kwanciya.

Mintina ƙalilan ta ji sallama, lokacin Meena da wasu daga cikin kawayenta sun iso gidan, wanka Meesha ta sake sannan tare da dauro alwala, tana cikin sallah mai mata kwalliya ta iso, bayan ta isar Aunty Teena ta tsantsara mata kwalliya sosai Meesha ta yi kyau, gama kwalliyar babu dadewa motocin su Dr ya iso, cikin rakiyar Meena ta isa wajen motar da Dr ke ciki, cikin sanyin murya ta yi sallama tare da shiga, amsawa ya yi cikin kasalalliyar murya yana lumshe ido, domin kamashin turaren ta ya kashe masa jiki, Meesha kam kasa ta yi da kanta don ji ta yi a takure take.

A haka suka isa wajen, lokacin wajen ya cika sosai da dan adam, suna zuwa aka soma gudanar da shagalin.

Sosai dinner ta yi kyau, anci an sha, Aneesa ma an halarci wajen dinner, sosai ta yi kokarin danne kishinta har aka tashi, karfe goma aka tashi gida Dr da Ameesha kawai suka nufi gidan

Rike da hannunta Dr yake har cikin bedroom ɗinta, akan gadon ta ya yi mata masauki, yana faɗin

"Heartbeat ki zauna ki huta ina zuwa." Ya yi maganar yana buɗe gyalen ta.

Saurin rintse ido ta yi, domin yadda yake mata wani irin kallo, da kyar ta iya daga kai ta amsa, domin gaba daya jinta take kamar a daure, murmushi ya saki sannan ya bar dakin.

Mota ya dauka bai dade da fita ba ya dawo, hannunsa dauke da manyan ledoji, falon Ameesha ya shiga ya aje, sannan ya nufi bangaren Aneesa, a falo ya iskota ta zuba uban tagumi, zama ya yi kusa da ita yana faɗin

"My Anne baki kwanta ba?"

"Yanzu nake son kwanciyar." Ta bashi amsa tana mik'ewa.

"Ok ga wannan bari." Ya yi maganar yana mik'a mata."

Ko kallonsa bata tsaya yi ba, ta yi shigewarta idonta taf da hawaye, tsaye Dr ya yi cikin mamaki halin Aneesa, sai kuma ya nufi bedroom ɗinta tunawa da ya yi da Ameesha ita ɗaya.

A kan gado ya ga ta zube tana aikin kuka, da kyar ya lallasheta ya nufi bangaren Ameesha, tana ganin ya fita ta kuma sakin wani kukan, Dr kam ko da ya koma bed din Ameesha a kwance ya sameta.

"Heartbeat ba dai har kin yi bacci ba?"

"Zan yi dai." Ta bashi amsa.

"Oya tashi ba zaki kwanta da yunwa ba."

"Dr nifa na koshi."

"No! Maryam tashi ki ci."

Tashi ta yi tana turo baki, falo ya koma ya dauko plet, juye masu lafiyayyen kasashen kaji ya yi, ya tsiyaya masu fresh milk a glass cup, lallaɓata ya yi ta ci kadan ta ce ta koshi

"Je ki yi brosh sai ki kwanta nasan kin gaji da yawa."
Chapter 14 · 0% Book details