Sashe 45
Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai kamar ni ina matsayin mahaifin Najeeb, har zan gindaya masa sharɗa amma ya yi burus da ita, yanzu kawai ina ofis sai ga kiran Taheer yana sanar min wai ya tsayar da ranar auren Najeeb da wannan mahaukaciyar yar tashi, ko uban wa ya ce masa zan haɗa zuri'a da mahaukaciya?"
Wani murmushi ya kubce ma Mummy, ta ce "kai masha Allah da wannan hukunci, amma na yi farin ci..."
Bata ko gama maganar ba, sai ji ka ke kau Alhaji Mansur ya dauketa da mari ya daura da fadin
"Amma ke shashasha ce, ai shi yasa na ce ke kika zuga shi har yake min yadda ya so, to wallahi baki isa ba matukar dai ina numfashi babu wani maganar aure tsakanin su."
Yana gama faɗin haka ya yi bedroom ɗinsa tare da buga kofar ji kake yi bom. Mummy kam nata dawowa daga zafin marin ta girgiza kai, a zuciyarta ta tir da halin mai gidanta.
**************************
Ummi ce ta tasa Ameesha a gaba don ta ci abinci, amma fir taki ci sai ma juya wa Ummi baya da ta yi, a haka Abba ya fito ganin ta juya baya ya sashi saurin matsawa dining din ya ce
"A'a Hajiya lafiya kuwa uwata ta juya wa dining din baya?"
Share hawayen da suka soma sauka akan fuskarta ta yi ta ce
"Alhaji ya zan yi mata? Tun ɗazun nake fama da ita kan ta ci amma fir ta ki, ina tunanin akwai abin da ta ke so, sai dai bata iya faɗa min."
"Ki bar yi mata kuka insha Allah, Auta zata sami lafiya yanzu haka nasa mu labarin wani asbiti a kasar Egypt insha Allah nan da karshen wata lokacin anyi aurenta da Najeeb zasu ta fi."
"Aure! Tayi saurin faɗa tare da ɗago kai, jin ya ambaci aure.
"Eh! Aure zan yi mata domin kuwa ina ga shi ne kawai mafita, nan da kwana ashirin da biyar biki.
"Allah ya kaimu." Ummi ta yi maganar jiki a sanyaye.
Abba yana shirin magana sai ga Abdul ya shigo, ya gaida iyayen sa tare da kallon Ameesha ya ce
"Sis kina dining ne kuna hira da Abba! Sai kuma ya maida hankali kan su Abba ya ce
"Abba Dr ne fa ya zo ganin Ameesha!"
Washe baki Abba da Ummi suka yi a lokaci guda da sauri Abba ya ce
"Shigo da shi maza."
Da sallama suka shiga falon Abba da Ummi wanda suka komo falon suka amsa masa, a kasa suka zauna shi da Hafiz din suna gaida su da tambayar mai jiki.
Ameesha da ke zaune tana jin muryar Dr Asmad da sauri ta taso daga inda take, wani kyakkyawan murmushi ne kwance a fuskarta, shi dai Asmad sai ganin ta ya yi kusa da shi zaune tare da rike masa hannu tana zazzare ido.
Murmushi ya sakar mata ya ce
"Autar Ummi babu magana sai zama kawai?"
Cikin muryarta mai sanyi ta maimaita abin da ya faɗa, shi dai Hafiz kallonsu kawai ya ke yi sun yi mugun da ce wa, gefe ɗaya kuma yana tausayin halin da Ameesha ta samu kanta.
Ummi ta yi murmushin takaici ta " Kai Auta wato ɗazun duk kin wani share maganar mu, har abinci kin ki ci amma daga ganin Dr ki sake, to Allah yasa yazo da allura!"
Bata rai ta yi, don dai bata son allura sam. Shi kam Dr hankalinsa ne ya tashi jin Ameesha bata ci abinci ba, da sauri ya ce "Ummi ina abincin?"
"Yana dining table taki ta ci, tun ɗazun nake fama da ita."
"To Ummi a kawo mata nan kila ta ci!" Dr ya yi maganar yana kallon Ameesha.
Haka kuwa aka yi, inda suke zaune Ummi ta kawo abinci, Dr Asmad da kansa ya dauki abincin ya mikawa Meesha ya ce
"Oya fara ci!
Jijjuya kai ta yi alamar a'a.
Bata rai ya yi ya ce " ok baki ci dai ko? To babu inda zan je da ke dama nazo ɗaukar ki ne, ko ba zaki bini ba...?
Ai tun kafin ya ida maganar ta dauki cokalin tana juya wa alamar dai zata ci, sai dai ta kasa don ta saba Ummi ke bata.
Ummi ce ta matso wajen ta ce
" Bari na bata! Domin bata iya ci da kanta." *SANGARTA* na damun ```MARYERM TAHEER```. inji Yar Mutan Rano. Ummi ta ida maganar tana kama hannun Meesha, aiko babu musu ta bi Ummi har dining, Ummi na bata tana ci, don Dr ya ce zai ta fi da ita.
A falo kuwa Abba ne zaune ya maida hankali kan maganar da suke da Dr. "Alhaji dama ce wa na yi, ya kamata a fita da Ameesha waje domin dai tunda an yi anan babu wani canji sai kawai a fita da ita."
Murmushi Abba ya yi ya ce
"Tuni na yi wannan tunanin har ma nasa mu bayani game da wani asbiti dake Egypt, to insha Allah end of this month zasu ta fi, don ina son su ta fi da mijinta n..."
Wani irin zabura Dr Asmad ya yi jin Abba ya ce mijinta.
"Mijinta" Ya yi maganar har jikinsa yana rawa.
*KUYI HAKURI DA WANNAN PLEASE*🙏
_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*
©
*ZULAYHEART RANO*
*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*
*Page din yau naki ne Badeeyar Adam (Beauty Queen), na baki page din kyauta, dubun gaisuwa inji DR ASMAD DA AMEESHA lol, Allah ya kara maki lafiya mai amfani*😍😍😍
_*Besty Najeeb ya ce yana godiya da son da kike masa zai zo har gida ya kwashi gaisuwa lol*_😻😻😻
```TEAM NAJEEB MANSUR```
*21*
Kallonsa Alhaji Taheer ya yi cike da mamakin yadda hankalinsa ya tashi lokaci ɗaya.
"Dr lafiya kuwa?" Abba ya tambaya.
Gyara zama Dr Asmad ya yi tare da dafe kirjinsa, wanda ke harbawa da sauri da sauri ya kakalo murmushin da iya kacinsa leɓe ya ce
"Babu komai Abba, gani dai na yi a condition din da Ameesha ta ke bai kamata a yi maganar aurenta ba!"
Murmushi Abba ya yi ya ce
"Nima sai da na faɗawa Najeeb haka, amma ya ce shi fa a haka yake sonta, zan aura masa ita in Allah yasa zata samu lafiya sai ta samu a ɗakinta."
"Allah yasa haka shi ne mafi alheri." Dr ya yi maganar cikin karfin hali.
Daga haka suka mik'e tare da faɗin
"Abba mu kam zamu ta fi gida, dama mun biyo duba Ameesha ne."
"Mun gode sosai Allah ya shi albarka, ka gaida iyayen ka."
"Za su ji." Ya yi maganar yana fara tafiya.
Ameesha da ke cin abinci tana ganin Dr ya mike da nu fi tafiya, ai da sauri ta mik'e tare da nufar su.
"Auta! Don Allah ki dawo ki gama cin abincin ki, ina kuma kika nufa?"
Ina ai sam bata masan me Ummi ke faɗa ba, har saida ta ɗan gana da inda Dr yake, kansa ta faɗa tare da sakin kuka. Sosai hankalinsa ya tashi da jin kukanta, saurin birkitota gabansa ya yi yana tambayar ta lafiya?
Shiru ta yi masa sai hawayen da ke zuba daga idonta, jan hannunta ya yi suka fita waje a can bayan gidan ya nufa da ita inda aka shirya wasu fararen kujeru domin shan iska, zaunar da ita ya yi shima ya zauna akan wacce ke fuskantar ta.
Zuba mata ido ya yi har na sakonni sannan ya sauka daga kujerarsa ya tsuguna a gaban ta, hannunsa ya zira cikin aljihu ya zaro kyakkyawan hankerchief ɗin sa ya soma share mata hawaye yana faɗin
"Me ya sanya ki kuka Princess?"
Shiru ta masa, ya kuma faɗin
"Ko baki son in tafi ne?"
Da sauri ta daga kai alamar "eh!
Murmushi ya yi irin wanda ake yiwa masoyin gaskiya
"Oh! Princess rigima."
"Zaki bini gidanmu?"
Nan ma da sauri ta amsa.
"Gud sai kin ce Sweety Asmad!"
Cikin daddaɗan murya ta ce
*"SWEETY ASMAD?"* Ta yi maganar cikin sigar tambaya.
Wani irin yar Dr ya ji a jikinsa musamman yadda ta ambaci sunan, sai ya ji ina ma zai dauwama yana mai jin muryar Ameesha, nan da nan sai ya ji damuwa ta ziyarci zuciyarsa da ya tuna da maganar Abba na ɗazun.
Kara kallonta ya yi ya ce
"Ki daina kuka insha Allah zan zo in tafi da ke, amma fa ba yau ba sai na Kuma zuwa kin ji, kuma in dai baki cin abinci ba zan je da ke ba, ki rika cin abinci kinji ko?"
Da sauri ta daga kai alamar dai "to!
"Yawwa tashi mu je karki kara kuka ki zauna a falo."
Ai ko babu musu ta mike suka nu fi cikin gidan, a kofar falo suka yi karo da Hafiz
"Sorry abokina mun bata lokacin ka ko?"
Murmushi ya yi kawai ya ce
"No! Babu komai tunda dai ka lallasheta."
Kallon kofar Dr ya yi sai ko ya ga Ameesha tsaye tana kallonsu, murmushi ya sakar mata tare da daga mata hannu alamar bye.
Ita ɗimma daga masa hannu ta yi har sai da taga fitar motarsu tukun ta shiga cikin falon.
**************************
Cikin wani irin yanayi Asmad ya isa gidansu Nenne, ko sallama ya kasa da dai yana cikin muguwar damuwa, babu kowa a falon don haka sai ya zube akan kujera tare da lumshe ido.
Nenne ce ta fito daga bedroom ɗinta, hannunta rike da waya tana dannawa da alama wata Number take nima. Kara bude ido ta yi ganin Asmad ɗin zaune a falon, da sauri ta k'arasa tana faɗin.
"Asmad lafiya kuwa, yau she ka shigo?"
Kasa magana ya yi kuma bai buɗe ido ba, har sai da Nenne ta kuma tambayarsa.
Da kyar cikin damuwa ya ce"Nenne na rasa Ameesha don Allah ki taimaka min!"
Da rashin fahimta Nenne ke kallonsa ta ce
"Ameesha ko Aneesa?"
"Ameesha dai Nenne." Asmad ya bata amsa.
"Wacece kuma Ameesha, a ina take?"
Sai a lokacin ya ɗan dawo nutsuwarsa jin tambayar da Nenne ke masa. Buɗe idonsa da yake yi jajir ya yi ya ce
"Nenne Ameesha budurwa ta ce aurenta zan yi.
Kallon mamaki Nenne ke bin Asmad da shi ta ce
"Ita kuma Aneesa fa?
"Ai ita matarsa ne, kuma yana da damar yin mata hudu."