Sashe 53
Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*GODIYA MAI TARIN YAWA GA*
*My Besty Khadija S Muhammad, hakika ina alfaharin samun ki a matsayin amintacciya, domin kuwa duk wani abu da aka gani cikin wannan labari ke ce silar shigarsa banza gaji da gode maki ba, Allah ta'ala ya saka maki da mafificin Alhairi ya bar mana zumunci har ya'ya da jikoki Allahumma amin.*
```JINJINA GA
Ummyn Yusrah fan's group
Bilkisu Bilyamin Novel's
3 Star Hausa Novel's
Surbajo Hausa Novel's group
Láifin wa? And sangarta fan's
Khalisat Haydar Hausa Novel's
Zama na amana 2
Hassan ATK
Hussain ATK
Umar Dalhat
Kamala Minna
Khadijah S Muhammad
Fa'eeza S Muhammad
Ummu Sayyid
Ummyn Yusrah
Amrah Auwal mashi (Princess Amrah)
Ramlat Ar Manga (My me Dambu)
Nafeesa Musa Ankerh```
Da sauran wanda ban lissafo ba.
```I hearttttt you my daughter Badeeyar Adam (beauty queen)```
*51*
Daukarta ya yi ba tare da ya ce komai ba ya nufi motarsa, ciki ya sanya su suna ci gaba da wasa da Littel Ameesha kai tsaye gidan su ya kaita, Rufaida kanta ta yi mamakin ganin Miemie har ta kasa hak'uri ta ce "Honey wannan kamar yarinyar da ake cigiya ko?" "Eh! Ya amsa mata a takaice. "Please ki yi mata wanka ki canza mata kaya sai mu kaita gidan su." "Gidan su honey baka tsoro ace kai ka saceta?" "Ai Gara ace ni ne na saceta akan akama wanda ya saceta ɗin, amma duk da haka ya zama dole iyayenta su san wanda ya saceta." Ya gama magana tana dage kai wanda ke tsananin yi masa ciwo, tir yake da halin mahaifinsa na son abin duniya, wato ashe Abba zai iya hada kai a yi kidnapped din jikar amininsa? Lallai duniya tazo karshe Allah ya rabamu da son zuciya.
Cikin kananun lokaci har Rufaida ta tsaftace Miemie ta shiryata cikin wata kyakkyawan doguwar riga mai kyau da tsada sosai yarinyar ta yi kyau da yake har kitson kanta ta canza mata sai ta fito fes, suna rike da hannun juna ita da Littel suka shiga mota, sai da suka biya suka ɗauki mommy sannan suka dauki hanya a tsanaki yake tuki har suka isa unguwar. Horn ya yi a kofar gidan mai gadi ya buɗe masa parking ya yi yana hamdala da ganin motar Abban Ameesha a gidan, hakan ya nuna cewa yana cikin gidan kenan, bayan ya faka motar bai fita ba sai ya ce "Littel da Miemie su fita, sai da yaga sun yi nisa har sun kai kofar falon Aneesa sannan suka fito daga cikin motar, kowa ya ga fuskar Najeeb yasan akwai damuwa "Ka ga Najeeb ka cire wannan damuwar kar wani cutar ta shigeka." Mommy ta yi maganar cikin sigar lallashi. "To mommy ya amsa yana kalkalo murmushi iri wanda iyakar sa laɓɓa. Suna kallon yaran suka fito daga ɗaya bangaren suka nufi ɗayan.
Duk suna zaune sai ganin Miemie ta shigo rike da hannun Littel, da mamaki suke kallonta sun kasa motsi, kallo ɗaya zaka masu ka tabbatar sun cikin farin cikin ganinta, babu ma kamar Aneesa har rige rigen zuwa daukarta ake wani irin mik'ewa Aneesa ta yi da gudu ta nufi Miemie wacce ta saki hannun Littel ta nufi Aneesa tana faɗin "oyo-yo Momma." "Oyo-yo 2 My baby I miss you, daga ina kike? Wa Ye suka dauke ki Miemie?" Aneesa ta jero mata tambayoyin cikin sauri. "Watu mutane tuka ta ni a motarsu wai za su kaini wajen Daddy shi kenan na tena ka nin ku." Cikin maganarta ta yi maganar. Kafin ta yi wata magana sai jin sallamar su Najeeb suka yi. Gaba daya suka ɗago da mamaki suna amsawa.
Ciki suka shiga aka gaisa Ameesha cike da ɓacin rai tana shirin yi wa Najeeb rashin mutunci, wato shi ya ɗauki mata yarinya ya barsu cikin matsala da tashin hankali, shima a bangaren Dr haka abin yake hanya yake nema da zai nuna wa Najeeb kurensa, sai yanzu ya tuna shi wannan saurayin Ameesha ne na da wanda suka yi zaman asbiti lokacin, maganar Najeeb ce ta dawo da su hsnkalinsu"Abba a yi hakuri ga Miemie nan ɗazun Allah ya sanya muka ganta, bana son kowa ya ce komai sai kun je gidan da muka samu Miemie daga nan sai ku san matakin da za ku dauka, amma ina rokon alfarma Abba kar ka ji kunyar wanda ya aikata hakan.
Duk sun yi na'am da maganarsa don haka gaba daya suka ɗauki mota don zuwa gidan motoci uku suka nufi gidan Aneesa rungume da Miemie kamar wani ya ce zai raba su.
Can bangaren kuwa ba su tashi farga babu Miemie ba sai da suka ga ta yi kusan awa bata shigo, nan fa hankalin su ya tashi duk gidan an duba babu Miemie sun tambayi mai gadi ya ce babu wanda ya shigo, domin Najeeb ya bashi kuɗi masu yawa ya ce kar ya faɗawa Alhaji Mansur ya shigo, ai ko ya ce babu wanda ya shigo, ya sanya su mugu su daure shi kenan aka fara horn, da sauri ya je ya bude don a tunaninsa Najeeb ne ya dawo, su mugu sun yi tunanin Yan sanda ne don haka da gudu suka biya. Mamaki matuka ya kama su gaba daya, Alhaji Taheer cikin fara'a ya fito yana faɗin "a'a Alhaji har kun riga mu isowa kenan? Lallai na yadda da soyayyar ka a gareni." Dabur cewa Alhaji Mansur ya yi zai fara kame kame Najeeb ya yi saurin cewa
"Ina mai bakin cikin sanar maku da mahaifina Alhaji Mansur ya sanya a dauke Miemie domin kwadayin abin duniya." Doguwar salati jama'ar wajen suka dauka "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." "Kai Najeeb bana son shashanci Yanzu ka rasa wanda za ka yi wa sharri sai mahaifinka?? Wannan wacce irin rayuwa ce Allah ya kawo mu da 'ya'ya basa kaunar iyayensu??"" "ABBA ya yi maganar cikin tashin hankali. "Sam Alhaji a zamanin yanzu kafin ka samu yaro mai biyayya wa iyayen sa kamar Najeeb da wahala wallahi duk abin da ya faɗa maka gaskiya ne, wannan kadan kenan daga cikin halin Mansur inda har baka ji tsoro ba wallahi shi ya sanya wasu marasa imani suka bige Ameesha har ta samu wannan lalurar." Wannan karon har kusan faduwa Abba ya yi don firgici, mutumin da ka yadda da shi shi ke ha'intar ka? Lallai mutum ba abin yadda ba ne, kallon Alhaji Mansur ya yi wanda ya yi tsiru-tsiru kunyar duniya ta rufe shi bai taba tunanin yana da kunya irin ta yau ba ji ya yi uwa kasa ta nitse ya faɗa ciki ko ya huta da kunya da nadama, yau kaɗai na ya ji ya tsani irin halinsa.
"Babu komai Alhaji duk abin da ka yi ka yi wa kanka, Allah ya sani da zuciya daya na daukeka amma tun da haka ne babu komai, har cikin zuciyata na yafe ma duk abin da ka yi min, kuma ina rokonku da ku yafe masa kunshi? Kai Jaheed ɗauko jakar kuɗin nan ka bashi miliyan biyar a ciki yi tun da domin kuɗi ya yi." Cikin sauri Jaheed ya cika umurnin Abba nusiha sosai Abba ya yi wa Najeeb wanda ya sanyaya masa jiki sannan suka juya, su ma su Najeeb motarsu suka shiga sai dai ya kasa jan motar sai Rufaida ta ja.
Su Abba na fita su mugu suka fito, Alhaji Mansur har zai fara kaso suka kwace kudin babu tausayi babu tsoro yana kallo suka wuce da shi, kuka sosai ya yi ya rasa aboki mai taimakonsa sannan kudin da aka bashi sun kwace wayyo tarin nadama da dana sani suka masa yawa take kansa ya fara wani irin sarawa. Da kyar ya iya jan motarsa zuwa gida, kwana biyu ciwo ya kwantar da shi, da kyar da lallashi Mummy ta samu Najeeb ya kai shi asbiti. Gwajin farko aka ce ciwon zuciya da hawan jini wanda suka masa mummunan kama, domin zuciyarsa kumbura ta yi haka jikinsa ya fara kumburi.
Allah ka bamu ikon aikat kyakkyawa, ba irin halin Alhaji Mansur ba na zallar cin amana da bakin ciki tare da hassada, ga dai yadda ya kare nan
Bangaren su Ameesha ma Alhamdulillah komai ya wuce, ta ci gaba da shayar da su Hibban da Hibba yara masu kyau da wayau sun yi tula-tula gwanin sha'awa
*BAYAN SHEKARA GOMA*
Alhamdulillah! Gidan Dr arziki ya ci uban na da don yanzu ya zama katafaren mai kuɗi k'aton gida ya gina masu, haka ya mallaki asbitoci har uku wanda ya sanya masu suna *A'A specal hospital* (Asmad Abubakar) duk a cikin garin Kano, duk inda ka zaga maganar sa ake Dr Asmad, ya yi suna fiye da tunani, yanzu yaransa biyar duk da su twins
*Fatimah (Miemie), sai su Hibban da Hibba, sai mai sunan Meena wacce suke kira (Besty) sai yanzu da take goyon mai sunan Bobbo suna masa lakabi da (Aryan)* gaba da yara yan gata da ko wanne fanni ga tarbiyya da nutsuwa.