← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 54

Sashe 54

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Miemie da Sahal yaron Meena suka shigo cikin falon bakin su ɗauke da sallama, Ameesha da ke zaune ita da Dr tana shayar da Aryan ta amsa "Mami Daddy sannunku da hutawa." Suka hada baki wajen fada. "Yawwa Abbana da Nennena an dawo daga school ɗin?" Da yake school daya suke da Sahal yau sai ya biyo direban Miemie wai zai gaida Ameesha "Eh Daddy Mommana bata da lafiya tana can sai juyi take yi." Miemie ta gama maganar tana hawaye. Kusan a tare suka tashi Ameesha saɓe da Aryan falon Aneesa suka shiga inda suka sameta kwance kamar yadda Miemie ta faɗa, da sauri Dr ya matsa kusa da Aneesa yana faɗin "sannu Aneesa me yake damunki?" "Cikina." Ta yi maganar da kyar. Cikin tausayi Ameesha ke mata sannu, shi kuma Dr ya dauko kayan aiki gwaje gwaje ya soma mata cikin kwarewa, Yana gamawa ya saki murmushi ya ce "Masha Allah! Miemie kin kusa yin kani Momma na da cikin wata biyu da kwanaki." Tsalle Miemie ta soma na jin dadi, ita ma Meesha farin ciki ne ya kamata har da hawaye ta rika godiya ga Allah, ya yin da Aneesa idonta ke fitar da hawaye duk na farin ciki." Sai ku bar kuka shi yasa tun tuni ban faɗa maku ba gashi yanzu ya nuna da kansa a bar kuka a yi murna Allah ya inganta. Aiko murna sosai suka yi daga lokacin Aneesa ta daina aikin komai sai da ta huta tattali da kula Dr na yi mata daidai gorgodo har Allah ya sauketa lafiya in da ta haifi santaleliyar budurwa mai kama da Dr kar kusa kuga farin cikin da family ɗin Dr suka shiga, ranar suna yarinya ta ci sunan Maryerm Aneesa da kanta ta zaɓi sunan da aka sanyawa 'yarta suna kiranta da *(IFTIHAL)*.

DUK WANDA YA GA ZURI'AR DR ASMAD SAI SUN BURGESHI, DOMIN MATAN BIYU SUN HADA KAN YA'YANSU BAKA TABA CEWA YA'YAN KISHIYOYI NE, DON TUNI IFTIHAL TA KOMA BANGAREN AMEESHA, FARIN CIKI KE WANZUWA A KO WANE RANA A GIDAN DR ASMAD. To muna sai mu ce Allah ya bamu farin ciki da kwanciyar hankali.

TAMMAT ALHAMDULILLAH

Anan na kawo karshen wannan littafi Mai suna sangarta, Alhairin dake ciki Allah ya sadamu da shi kuskuren da ke ciki Allah ya yafe mana.

Godiya gare ku masoya abin tunkaho abin alfahari, Allah ya barmu da ku har gaban abada Amin.🤩🤩

Tukuici ga my Besty Khadija S Muhammad, bana gajiya da yabon ki wallahi, domin karamcin ki a gareni ba ya faduwa sai dai na ce Allah ya biya bukatu na Alhairi.😘

SAI MUN HADU A WANI

*Ni ce ta ku har kullum*
*ZULAYHEART HARUNA RANO*
*ZULAYHEART RANO*
*UWAR FAWZAN*💞
Chapter 54 · 0% Book details