← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 54

Sashe 44

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idonta biyu amma in ba ka duba da kyau ba sai ka ce bacci ta ke yi, ko da ya yi maganar tana jinsa amma da yake yan maimaita maganar basu kusa ko ɗago kai ta kalleshi bata yi ba, domin dai wannan muryar bata saba jin taba, ita kuma so take ta ji irin wanda ta saba ji. Haka ya gaji da magana ya tafi.

Yana fita Meena ta shigo falon, ganin ta ita ɗaya a kwance sai ta matsa tana faɗin

"Meesha ke ce kawai a falon?"

Bata yi magana ba sai buɗe dara daran idonta da ta yi tana kallon Meena ɗin. Gyara zama Meena ta yi tare da sanya game a wayar Ameesha, kuma shi ne game din da Ameesha ta fi so akan ko wanne. Zuba wa wayar ido ta yi tana kallon yadda Meena ke buga game ɗin, har wani murmushi ta ke yi alamar abin ya mata daɗi, ganin haka sai itama Meena ta ji dadi.

"In baki kema ki buga?"

Bata fahimci me Meena ta ke nufi ba, don haka sai ta ci gaba da kallon wayar, mika mata wayar ta yi , amma sai ta bata rai, cikin sauri ta kamo hannun Meena ta daura akan wayar alamar dai ta ci gaba da bugawa .

Da ta fahimci nufin ta sai kawai ta ci gaba da bugawar, haka suka kasance cikin farin ciki, domin dai a duniya Meena tana son farin cikin Meesha.

*************************

Aneesa ce zaune a can kuryar gado, ta zabga uban tagumi kai da gani kasan cikin tunani take, can dai ta sauke tagumin tare da jawo wayarta dake dan nesa da ita. Number ta lalubo sannan ta danna kira ringing biyu aka daga wayar.

"Hello k'awata gaskiya fa ina cikin wani mawuyacin hali." Ta yi maganar ciki rashin nutsuwa.

Daga ɗaya bangaren ta amsa

"Anee mai ya sameki?"

"Ki bari kawai wallahi ina cikin matsala."

"Ke nifa bani son wannan abin na, ki yi min magana sak bana don kwana kwana."

Ajiyar zuciya Aneesa ta sauke ta ce

"Kinga wai fa ciki ne da ni, kuma ke kinsan bana son haihuwa a irin wannan lokacin."

Mtsss Rukky ta ja tsaki, ta ce

"Amma wallahi Aneesa har kin bani haushi, yanzu don Allah saboda cikin ne ki ka tada hankalin ki?"

"Dole in tada hankalina duka yaushe aka yi auren? Wata fa na uku kenan, shi ne har zan samu ciki?" Ta ci-gaba

"Gaskiya dai ban shirya haihuwa ba, kuma bana kaunar cikin nan wallahi, yanzu ya ki ke ganin za'a yi?"

"Gaskiya nima dai ban baki goyon bayan haihuwa yanzu ba, don mazan yanzu da kun haihu suke daina ya yin ki, musamman irin su Dr da yanzu suke ganiyar tashen su. Akwai hanya amma da fatar bai san da cikin ba?"

"Eh! Gaskiya dai bana tunanin yasan da shi, domin da ya sani da kansa zai sanarmin don dai yana da son yara sosai."

"Gud! Haka yana da kyau, kina ji kawai ki shirya ki je asibiti sai a zubar da shi, tunda bai wani girma ya...

"Ke! Aneesa ta yi saurin katseta, ta ce "nifa nan babu inda na sani."

"Dallah! Ke wallahi baki haɗu ba, ga asbitoci nan da yawa a gari, ki bari in ya fita kema ki fita abinki, kafin ya dawo kin gama komai, kuma ai nan layinku naga wani asbiti ki gwada zuwa, ke kam wani lokacin kamar wacce bata waye ba."

"Tom shi kenan, zan gwada ɗin. Zaki ji kirana a kowane lokaci."

"Yawwa ko ke fa! Amma ki yi kokari don matukar ya fahimci kina da ciki to fa sai kin haifa masa, musamman da shi fa a gidansu shi kadai ya taso, zai so ganin jinin sa."

"Karki damu an gama."

"Sosai Aneesa ta yi na'am da shawarar Rukky, don ita fa bata son ta rasa Dr Asmad ne, kar ta haihu ya je ya sake auro wata, ita kuma ya daina ya yinta, tana wa Dr wani irin so ne ba na wasa ba."

*( Hmmmm Aneesa kenan, wannan sam ba shawarar arziki ba ce, Allah ya baki kyauta mafi daraja amma saboda wani banzar hujjar ki ki ce baki so? Ina ji ye maki zuwan ranar nadama)*

Aiko cikin zuciyarta ta kudurci niyyar gobe yana fita, itama zata kama kanta.

*ASBITIN MALAM AMINU KANO*

Asmad ne zaune ya zuba wani uban tagumi, tunanin Ameesha kawai ya ke yi, shi bai taɓa tunanin sonta ya kama shi haka ba, sai da wannan ciwon ya kamata, ya ji daɗin kasancewar su a asbitin, yana son Ameesha so mai tsanani amma ya rasa hanyar da zai bi don ganin ya mallaketa. Masifar sonta yake don ko motsi ya yi sai ya tuna ta, musamman murmushinta, kallonta, dariyarta, uwa uba kuma *SANGARTA* da take yi, kai komai nata yana burgeshi.

Wayarsa ya jawo ya soma buɗe pic din da ya mata lokacin da take asbiti, wasu tana bacci wasu kuma idonta biyu, wani kuma tana murmushi, yana kallon pic din yana murmushi tare da girgiza kai a fili ya furta

*Princess kin haɗu iya haɗawa, Allah ya mallaka min ke matsayin matar aure*

_Don Allah ku yi hakuri da wannan, wallahi shi din ma da kyar na tafa shi_ ``` I hearttttt you all my fans```😍😍

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*I love you all SANGARTA FANS* 😍😍😍😍

Dedicated to *SHAMSHIYA SALIS*

_*Na yi mamaki sosai a lokacin da na samu labarin harda SHAMSHIYA SALIS, cikin masu bibiyar wannan Nobel din. Gaisuwa ta musamman tare da fatar alheri a gareki*

*20*
Sosai ya maida hankali wajen kallon pic din Ameesha, sai ko dayar wayarsa ta soma ruri, sunan wanda yaga yana kiranne yasa shi ɗauka tare da karawa a kunne

"Hello abokina ya garin?"

"Lafiya lau! Aka bashi amsa daga ɗaya bangaren.

"Kana ina ne?" Dr ya tambaya.

"Gani zan shigo asbiti, shi ne na ce bari na kira ko ka fita?"

Dan dariya Dr Asmad ya yi ya ce

"Ina office ka shigo kawai."

"To! Ya amsa ta re da kashe wayar.

Minti biyar tsakani sai ko yaji norking ɗin kofar office din. "Yes shigo mana!"

Babu bata lokaci ya shigo, a tare suka sakarwa juna murmushi, tare da gaisawa.

"Kai wallahi na yi farin ciki da ganin ka Hafiz, domin dai ina da bukatar shawarar ka."

Wanda aka kira da Hafiz zama ya yi tare da fuskantar Dr ɗan fullo, yana sauraron maganar da ya ke masa. A jiyar zuciya Dr ya sauke yana ci gaba da kallon pic din Ameesha.

"Dr ka fara magana kuma ka yi shiru, wai me ya faru ne?"

Murmushi ya yi ya ce

"Haba Hafiz, babu fa wani abu na damuwa, shawara kawai nake nema a wajen ka."

"Ok ina sauraron ka!"

Gyara zama ya yi tare da maida hankali kan Hafiz din ya ce

"Wato maganar dai ita ce, kasan wannan yarinyar dana taɓa baka labarin ta, wacce muka haɗu a shahad store har na mareta?"

"Yes! Na gane ta, amma ban san yarinyar ba." Hafiz ya bashi amsa.

"Ok mun kuma haɗuwa da ita, har ma na zama mata Malami ta fannin karatu, duk da dai a da ba wani shiri muke ba, amma a yan kwanakin can kafin ta samu ciwo mun fara dai dai tawa, tun ranar farko da na ganta nake jin sonta, har zuwa yau ina jin kishin in ganta da wani saurayin balle inga tana masa murmushi, kai a takaice dai ina mugun sonta so irin mai tsanani ɗin nan, wallahi sonta ya hanani sukuni, ko yaushe cikin tunanin ta nake, duk wannan abin bata masan ina yi ba, na yi dogon tunani ya kamata in sanar mata, sai dai an samu matsala, domin ranar da nake niyyar bayyana mata kudirina sai Allah ya gifto da wani iftila'i ."

Dr ya yi shiru da maganar sa yana mai tsantsan tausayin Ameesha.

"Ina jinka ." Hafiz ya faɗa.

"Eh iftila'i domin dai ta samu ciwon mantau, ma'ana ta manta komai na rayuwar ta na baya, ina sonta tare da tausaya mata, ina burin ta zama matata, amma na rasa ta yadda zan yi wa su Nenne bayani."

Jinjina kai Hafiz ya yi ya ce "duk ta su Nenne mai sauki ne, matsalar tana ga ita yarinyar domin a yanzu komai zaka faɗa mata ba zata gane ba, hasalima bata sanka..."

"No! Hafiz wallahi tun ranar da ta samu ciwon babu wanda ta yadda da shi kamar ni, domin da kyar nake guje mata har kunya ta rika bani a gaban iyayenta."

"Simple ai ma maganar ta zo cikin sauki, domin kuwa basai ka tsaya bata time dinka ba, kaje ka faɗawa iyayenta kana sonta fakat."

A jiyar zuciya ya sauke ya ce "toh! Zan gwada amma ina kunya."

"Ka tsaya kunya sai dai kaji labarin aurenta."

"Kuma fa haka ne, wannan saurayin nata kamar zai cinyeta ɗanya ko yaushe cikin rawan kai yake." Dr ya k'arasa maganar yana kwashe wayoyinsa.

Dariya Hafiz ya yi ya ce "to ita kuma Aneesa fa?"

"Ina sonta, amma son Ameesha ya fi nata a zuciyata." Dr ya bashi amsa.

"Allah ya tabbatar da Alhairi, ya baka ikon yin adalci in ka auri Ameeshar taka."

"Ameen" ya amsa " tashi ka rakani ma in dubo ta! Haka suka fita a office din tare don zuwa gidan.

**************************

Tun daga nesa ya soma kwallah mata kira, cikin sauri ta fito daga bedroom ɗinta tana faɗin "gani Alhaji Allah yasa lafiya?"

Wata muguwar harara ya cilla mata, zuciyarsa na tafarfasa ya ce
"Wallahi keda danki ku fita idona, ida ba haka ba wallahil Azeem sai na mugun bata ranku."

"Allah ya baka hakuri Alhaji, amma ban san laifin da muka yi ba?"

"Au tambayata ma kike to? To bari ki ji domin nasan ke ce kike zuga Najeeb har yake min rashin mutunci son ransa ko? Wallahi zan yi maku walak'anci sosai a gidan nan."

"Allah dai ya baka hakuri, amma ban san laifin da ake tuhumar mu da shi ba." Ta yi maganar cikin sanyin murya.
Chapter 44 · 0% Book details