← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 54

Sashe 12

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi, kishinta da sonta suka rufe masa ido har bai san lokacin da ya isa inda take ba, bai jira komai ba ya finciki hannunta, a firgice take kallonsa ganin kamar ba a hayyacinsa ya ke ba yasa ta yi shiru, shi kam bai zame ko ina da ita ba sai cikin falo jefata kan kujera ya yi sai huci ya ke yi.

"Baki da hankali ne zaki je ki tsaya gaban wani kato har kina masa murmushi?" A kausashe yake maganar.

Harara ta jefa masa ta ce "ikon Allah kai a suwa kuma *kare da gudun layya*? Ina ruwan ka sani? Bana son shishshigi ban shiga rayuwar ka ba, don haka kaima karka shiga rayuwata, baka isa ka rabani da samarina ba." Cikin karaji ta dire maganar.

Murmushin takaici ya yi ya ce

"Ni kike tambaya matsayina a gareki? Tabbas kuwa nike da matsayi da iko dake."

Dariyar rainin hankali ta masa ta ce, "kenan kaine Abba? Don nasan babu mai iko dani kamar Abba, idan ko kai ba Abbana bane waye kai?"

"Mijinki ne ni." Ya bata amsa kai tsaye.

Wani irin ihu Meesha ta yi cike da tashin hankali ta ce"..."

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

```Wannan page din Sadaukarwa ne ga KHADIJA BEE BEEN MASOYA uwar Ilham mata a wajen Hafiz, uwargida kike kinfi amarya 😉 Hajiya ki daɗe ki karko ki yi shekaru irin na dabino, Allah ya ja zamanin ta Masoya mai Masoya da yawa, wannan kirarin duk domin ki ne ke ɗaya Հմʆαίհզ ɾզησ tαηα ψίηKi ιяσи ѕσѕαι ∂ιи иαи😍😍😍```

*37*

"Miji? Mijin wa kenan?"

"Mijin Maryerm Taheer Ameesha, don haka ina kara gargadin ki da ki shiga hankalinki wallahi idan ba haka sai kin gane kuranki." Yana gama faɗa mata haka ya juya fuuu ya bar gidan ma gaba ɗaya domin ransa ya ɓaci da kallon Ameesha da wani.

Ita kam Meesha duniyar mamaki ta shi da jin furucin Dr "Wai mijina! To ta ya har ya zama mijina da har yake ikirari?" A bayyane take wannan tambayar da sauri ganin bata da amsa, sai ta nufi bedroom din Ummi domin samun amsoshin tambayoyin ta.

Ko sallama bata yi ba ta shige cikin dakin, Ummi dake zaune tana linke kayan da aka gogo mata sai ganin Ameesha ta yi a yam a kanta kamar wacce aka jeho.

"Oh! Ni Halima ke kam Auta zanga ranar da zaki yi hankali, lafiya kika shigo min daki a wannan yanayin?"

Kukan shagwaɓa ta fashe da shi ta zube a wajen

"Ke nifa bana son rashin hankali, daga tambaya sai ki kama kuka, naga alamar ke kullum SANGARTAR ki gaba take, idan ba zaki bani amsa ba tashi ki fita."

Mik'ewa ta yi tare da ficewa, a cewar ta Ummi ta kara bata mata rai, girgiza kai Ummi ta yi tare da fadin

"Allah ya shirya min ke Ameesha." Ta gama maganar tana ci gaba da abin da take yi.

Ameesha kam bedroom ɗinta ta shige inda ta ci gaba da kukanta, wani tunani ta yi wanda yasa ta yi saurin mik'ewa sai alokacin maganganun Meena ke dawo mata

*"Meesha kenan Dr ai yana da matsayin da kike da shi a gidan nan, ke kusan ya fiki ma."*

*"Allah da gaske Dr yana da matsayin da na sanar maki, wallahi da zaki san irin taimakon da ya yi wa rayuwar ki to tabbas da babu raini har abada tsakanin ku, kuma sai soyayyar da kike masa ta karu, Asmad wani jigo ne a rayuwar ki*

"JIGO? ta yi tambayar a bayyane, "kenan jigo na nufin mijina ne? Ta ya ya zama mijina? Me yasa daga ranar da na tuna komai zuwa yau ban fahimta ba?" Wa zan tara da wandinnan tarin tambayoyin?

"Abba." Shi ne amsa da wata zuciyar ta bata amsa.

Wani sabon kuka ta fashe da shi, wata zuciyar tana farin cikin samun Dr matsayin miji, wata zuciyar kuma tana alhini, a haka bacci ya yi awon gaba da ita.

Dr kan ransa a matukar ɓace ya bar gidan, zuciyarsa wani irin zafi take masa, bai san son da yake wa Ameesha ya zarta har haka ba, ji yake kamar zuciyarsa zata faso, kasa zuwa gidansa ya yi sai ya dauki hanyar gidan Nenne, idonsa jawur kamar garwashin.

Ko parking Mai kyau bai tsaya ya yi ba, ya fita daga motar cikin kai tsaye falo ya shi da wani irin sauri, sallama ma kasawa ya yi sai zubewa da ya yi akan kujera.

Bobbo da Nenne a tare suka ɗago da kai suna kallon Asmad wanda yake dafe kansa da hannu bibbiyu

"Lafiya?" Nenne ta yi masa tambaya.

"Babu komai." Ya basu amsa yana a yadda yake.

"Kai karka faɗa min zancen banza, ya ana tambayarka kana faɗa mana babu komai bayan ga a yanayin da ka shigo? A fusace Bobbo ya dire maganar.

"So nake Maryerm ta tare cikin satin nan." Jikinsa ko alamar motsi baiyi ba ya yi maganar.

"Maryerm ta tare anya kana cikin nutsuwarka kuwa Asmad?"

"Eh! Nenne ina cikin hankalina."

"To bazata tare a satin nan ba ka ji na faɗa maka, tashi ka bamu waje shashasha kawai." Cikin faɗa Bobbo yake maganar.

Sai a lokacin ya dago kansa tare da bude ido sa, wanda suke masa nauyi, hankalinsu ya tashi da ganin yadda Asmad ya koma.

Dafa kansa Nenne ta yi tana faɗin

"Asmad ka riƙa hakuri da duniya saurin fushi yana kawo dana sani, riƙa maimaita inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, zaka samu sassauci."

Gyada kai ya yi cikin zuciyarsa yana maimaita inna lillahi, a hankali ya ji zafin zuciyarsa yana ragu wa, su kam kallonsa kawai su ke yi, ganin an kira magriba sai Bobbo ya fita Masallaci, Nenne dai bata matsa ko ina ba har sai da ta ji abin da yasa ɗanta ɗaya tillo damuwa.

"Ina jinka Asmad ɗina mai ya sameka haka?"

"Nenne wai na je gidan su Ameesha shi ne na ganta da wani a tsaye, wallahil azeem Nenne raina ya mugun ɓaci har dai na kasa danne kishina na yi mata magana Allah Nenne baki ji amsar da ta bani ba." Cikin takaici ya gama maganar.

"To ka yi hakuri, Ameesha dai matarka ce, komai dadewa zata tare gidan ka, da kanka zaka koya mata yadda zata soka kuma bana tunanin tasan kai miji ne a gare ta, na tabbatar da saurayi ne yazo wajen ta Hajiya Halima ba zata barta ba, babu mamaki cikin masu zuwa dubata ne. saurin fushi yanzu ba naka bane kaji ko?"

"To amma Nenne sai ta saka shi gaba har tana masa murmushi?"

"Ka dai yi hakuri na ce, tashi ka je ka yi sallah lokaci na tafiya."

Kai ya gyada alamar ya gamsu da bayanin Nenne

******
A gajiye Alhaji Taheer ya shiga gida, yau ko bedroom ɗinsa bai nufa ba, a babban falo ya yada zango, yana furta

"Wash!

"Sannu da dawowa Alhaji ya aikin?" Ummi ta yi maganar tana mika masa sassanyan ruwa.

"Aikin Alhamdulillah! Wallahi na gaji sosai, duk na kosa in dawo." Abba ya yi maganar bayan ya gama shan ruwan.

"Ai gaka ka dawo hankali ya kwanta." Cikin murmushi ta fada.

"Lallai kuwa Halima tunda na yi tozali da ke hankalina ya kwanta."

"Hmmm! Alhaji kenan." Ummi ta, ka yi wanka lokacin sallah ya gabato go."

"Mu je uwargida kuma amarya." Cike da farin ciki Abba ya fita Masallaci, ko da ya dawo a falo ya yada zango, Ummi ce ta fito cikin kwalliyar ta, kusa da Alhaji Taheer ta zauna tana faɗin

"Alhaji an dawo?".

"Eh! Na dawo." Ya bata amsa.

"Abinci na jiranka."

"Ok wai ina yaran gidan ne? Uwata fa tunda na dawo ban ji motsinta ba?"

"Rigimammiya Ameesha ɗazun ta shigo wai zata tambayeni, na ce akan me shi ne ta fara kukan sangarta bata ce min komai ba ta fita, to nidai daga haka ban kuma ganin ta ba."

"Kuka?" Abba ya tambaya cikin mamaki.

"Eh! Alhaji Ummi ta tabbatar masa.

Wayarsa ya jawo Number Ameesha ya kira ringing biyu ta dauka muryar irin ta mai bacci.

"Subhanallah! Uwata lafiya kuwa?"

Shagwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce

"Abba Dr ne."

"Dr kuma me ya faru da Dr?" A rude yake mata tambayar.

Wannan karan bata yi magana ba sai kuka da ta fashe da shi mai tsuma zuciya, hankalin Abba ba karamin tashi ya yi ba da jin kukan Ameesha don haka cikin sauri ya ce

"Sauko ina falo kin jiko ki daina kuka haka nan."

Ummi dai zubawa sarautar Allah ido ta yi har zuwa lokacin da Meesha ta sauko, kusa da Abba ta zauna tare da ɗaura kanta a kafadar Abban, har a time ɗin idonta na hawaye, saurin sa hannu ya yi yana share mata.

"Sorry uwata ki bar kuka me ya samu Dr?"

"Abba da gaske wai Dr Asmad mijina ne?"

"Wa ya faɗa maki?" Abba ya yi tambayar yana dan bubbuga kafadar ta.

"Shi da kansa ya faɗa min."

"To kuma shi ne abin tada hankali uwata?" Cin kwanta da hankali Abba ke Magana.

Wasu hawaye ne suka kuma zubowa ta ce

"Abba ta ya har ya zama mijina bayan Bama son junanmu?"

Murmushi Abba ya yi cikin nutsuwar da lallama ya warware mata komai, babu abin da Abba ya boye mata, kuka sosai Meesha ta yi domin jin yadda Alhaji Mansur ya kirata mahaukaciya sannan ya yiwa Abban ta walak'anci, sosai ta yaba da mutuncin Dr da na Bobbo domin sune silar samun nutsuwar mahaifinta, sai dai bata so yadda auren ya zama kamar na hadi ba, taso taji labarin Dr da kansa ya ce yana sonta ba wai mahaifinsa ya nemi a ɗaura ba kamar yadda ta ji Abba ya fada

Wani irin zabura ta yi ta ce

"Abba Dr Asmad shi ne mijina? Abba shi ne fa wanda ya mareni a sahad."

Wani irin zabura Alhaji Taheer ya yi cikin tashin hankali ya ce what..?"
Chapter 12 · 0% Book details