← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 54

Sashe 23

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"No! Hafiz wallahi na cire raina daga Ameesha, duk da ina mugun sonta, kuma na tabbatar ko mutuwa na yi to sonta ne dalili amma kar wannan ya dameka."

"Yawwa abokina, kasa aranka in har matarka ce tofa babu makawa sai ka aureta."

"Insha Allahu na dauki shawarar ka, Allah dai ya kara rufa mana asiri."

Daga haka suka yi sallama.

A haka Dr Asmad ya gama aikinsa ya wuce gida, duk da zuciyarsa tana mararin ganin Ameesha amma haka ya daure don yasan kwanaki biyu ya rage ta matar wani.

Addu'a ya je mata da fatan alheri, a duk inda ta samu kanta, ko da ya fita ba gidansa ya nufa ba, gidan iyayensa ya nufa, don ya kwashi gaisuwa.

*Gidan Alhaji Taheer*

Ummi ce tsaye a farfajiyar gidan, tana kallon yadda baki 'yan biki ke ta hada - hada, yayin da wasu suke isowq ma a lokacin. Kasancewar kwana biyu ne ya rage kacal daurin auran Ameesha.

Duk wanda yasan Ummi da kuma yadda ya karancin halayyar dan Adam, to cikin kankanen lokaci zai gane Ummi na tattare da damuwa.

Ta ja wani siririn tsaki hade da daga kafafunta da suka yi mata nauyi, ta shige kuryar dakinta, inda ta yada zango a kan gadonta.

Namma tsakin ta rika ja, duk lokacin da ta dakko tunanin ta hade direwa. Da za a dure tsakin da Ummi ta yi yau a buhu, ba abun mamaki ba ne don ya cika buhu da rabi.

Tana daga kwancen ta amsa sallamar da aka yi, ba tare da ta dago kai ta kalli me sallamar ba.

" Tun da na shigo gidan nan na fahimci kina cikin damuwa. Wai duk tunanin rabuwa da Ameeshan ne tun yanzu?
Aunty Saude k'anwar Ummi ta yi tambayar tana zama kusa da ita.

"Bari kawai, har da hakan ma wallahi, ina tunanin ya zaman yarinyar nan zai kasance, ita ba wata me koshin lafiya, wallahi naso ace magani aka fara neman mata fiye da maganar aure. Har yanzu mune muke kidanmu da kuma rawarmu, don gidan su Angon nan har yanzu tsinkensu bai shigo gidan nan da sunan maganar aure ba."

Ta karasa maganar tata hade mikewa zaune, cikin jimami tana kallon Aunty Saude.

A jiyar zuciya Aunty Saude ta sauke ta ce

"Ki bar tunanin nan kar ya haifar maki da wata matsala, tunda Alhaji ya yi niyyar auren nan na tabbata ko da ba zasu kawo komai ba tofa sai anyi shi, ita dai Ameesha addu'o kawai zaki rika yi mata."

"Insha Allahu zan yi.

"Amma anya kuwa Aunty gidan mazan nan suna son auren kuwa...?

_Ku yi hakuri da wannan Please._

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*23*

"To ni ina zan sani masu, abu daya dai na sani shi ne sun bata min rai." Cikin takaici Ummi ta k'arasa maganar.

"A dai kara hakuri Aunty."

"Yo ai hak'uri ya zama dole, tashi ki je wajen autar kila tana bukatar wani abun."

"To Aunty" shi ne abin da Aunty Saude ta faɗa tana mik'ewa.

***********

Asmad ne kwance a daki sai juye juye ya ke yi, tunda garin Allah ya waye sallah kawai ya yi, sam baya jin dadin jikinsa tunanin rabuwa da abar sonsa Ameesha shi ya haddasa masa wannan zazzafar zazzaɓin, duk da ya sha magani amma babu wani sauki.

"Sannu Hamma ya jikin?" Aneesa ce ta yi maganar tana zama a bakin gadon.

"Da sauki." Asmad ya yi maganar cikin karamar murya.

"Allah ya kara sauki, ko za'a sanarwa su Nenne ne?"

"No! Ba sai kin sanar masu ba, kar hankalinsu ya tashi, ai na samu sauki zuwa anjima zan fita."

"Allah ya kara lafiya."

"Amin! Haɗa min ruwan wanka kila ko na kara samun kwarin jikin." Ya dire maganar yana tashi zaune.

Cikin kankanin lokaci har ta gama haɗa masa ruwan, sannan ta fito tana faɗin

"Hamma na gama!"

"Na gode, ɗan taimaka min."

Da taimakon Aneesa ya yi wankan, har ya shirya babu laifi ya ɗan samu kwarin jikin, tunda har falo ya fito ya kunna t.v .

*Yau saura kwana daya biki*

Zaune a falo Ameesha ce da Meena, Meena ke gyara mata gashinta wanda suka je aka wanke, shi ne kaɗai abin da Ummi ta yadda akawa Meesha don ta ce yarta bata da lafiya abarta har zuwa lokacin da zata sami sauki sai a yi shagalin auren.

Meena ta kalli Meesha ta ce

"Meesha gobe iwar haka kin zama amaryar Najeeb."

"Amaryar Najeeb?" Meesha ta tambaya.

"Eh! Gobe zaki tafi ki barmu, zan yi kewa."

Wannan karon Meesha shiru ta yi kamar mai tunanin wani abu, haka Meena ta ci gaba da mata hira amma taki amsawa.

"Alhaji wai kuwa kana ga yaron nan na son Auta?"

"Wannan wacce irin tambaya ce?"

"Allah ya baka hak'uri, amma ni sam tsarin auren nan bai min ba."

"To ni kuma ya min." Abba ya kai karshen maganar yana barin wajen.

"Allah ya kyauta, amma wannan abin ban taɓa ganin ko jin irinsa ba."

**

Yau kam jikin Dr ya yi sauki don har fita ya yi asbitin su, sai da ya kammala da duba marasa lafiya tunkun ya koma office, duk da yau din ta kasance Lahadi ne, babu aiki amma shi Asmad ya saba ya je don duba marasa lafiya.

Office ya koma, ya zauna tare da janyo laptop dinsa, wani bincike yake yi akan wata ciwon, wayarsa dake gefe ta soma kara, ɗan tsaki ya ja don bai so a katse masa aikin da yake, sunan Hafiz ya gani .

Hannu yakai tare da ɗaukar wayar ya kara a kunne

"Hello Dr kana jina?"

"Eh! Dr ya amsa a takaice.

"Dama zan ce maka ne zaka samu zuwa wajen daurin auran kuwa?"

"Daurin auran wa?" Ya yi tambayar.

"Auren Ameesha mana."

"Oh! Wai yau ne auren?"

"Eh! Mana hala baka duba katin da Jaheed ya kawo mana ba?"

"Gaskiya dai ban duba ba, kuma yanzu ina wani aiki ne, bani ma a gida ina office don haka ba zan samu zuwa ba, amma ko zuwa gobe zan je na yi masa Allah sanya Alhairi."

"To ai shi kenan, nima ɗin da kashe aikin zan yi muje tunda haka ne to mu bari sai goben."

"Allah ya kaimu." Dr ya faɗa yana kashe wayarsa.

Ko da ya gama wayar, tagumi ya zuba idonsa taf da kwallah, zuciyarsa wani mugun zafi take, musamman da ya ji yau auren farin cikinsa, a fili ya furta

*"Shi kenan ni kuma na rasa farin cikina daga yau har zuwa ranar da zan koma ga mahaliccina."*

A dole barin aikin ya yi don wani sabon zazzaɓin ne ya kuma saukar masa. Da taimakon addu'a ya isa gidansu. Ko kyakkyawan fakin ba yi ba, ya fita daga motar.

Ko sallama kasawa ya yi sai zubewa da ya yi akan kujera, dage da kansa Nenne dake zaune a falon ganin shigowar Asmad ɗin a wannan yanayin yasata saurin mik'ewa tana ambaton sunan Allah.

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Asmad lafiya?"

Da kyar ya iya furta "Nenne bani da lafiya ne."

"Subhanallah me ya same ka? Daga ina kake?" A hargitse Nenne kewa Asmad ɗin tambaya.

Cije leɓe ya yi ya ce

"Daga office nake, wayyo Nenne kaina ciwo ya ke."

Hankalin Nenne ya mugun tashi da ciwon Asmad ɗin, wayarta ta dauka ta kira Bobbo tana sanar masa da halin da ake ciki. Ai cikin sauri Bobbo ya iso gidan yana, shi ma ya tsorata da yadda Asmad ɗin ya ke.

Wayarsa yasa ya kira wani Dr abokin Asmad ɗin, cikin kankanin lokaci ya iso, duba shi ya yi sosai sannan ya masa allura ya bashi magani, babu jimawa bacci ya kwashe shi.

Kallon su Bobbo ya yi ya ce

"Ku kwantar da hankalinku damuwa ce ta haifar masa da zazzaɓin, amma insha Allah sanda zai farka zai ji sauki ."

Godiya sosai suka masa sannan ya tafi. (To Asmad Allah ya baka lafiya da sauran musulmai baki daya.)

*Wajen daurin auran*

Jama'a ne dankam a kofar gidan Alhaji Taheer, duk inda ka duba motocine ga sunan birjik manya na Alfarma, kallo ɗaya zakawa Abba kasan yana cikin farin ciki da wannan rana.

Su ya Jaheed ma sun hallara, fuskokinsu cike da farin ciki, dangin Ango kawai ake jira a daura auren. Tun 12 aka sa lokacin auren gashi har 12:30 da yawan mutane har sun fara kosawa, shi kansa Abba mamakin rashin zuwan su Alhajin yake.

Wani mutum dake gefe ya buɗe baki sosai tare da fadin

"Kai wallahi mukam mun gaji da wannan jiran, zamu wuce don muna da aikin yi..."

Tun kafin ya gama rufe baki sai ga wani mutum, da gani kasan dan jagaliya ne don yadda ya burgago mashing ɗinsa cikin mutane mai cikakken hankali ba zai iya yin haka ba.

Kai tsaye wajen da su ya Jaheed suke ya nufa tare da mika masu zungureriyar takadda mai cike da rubutu, da rashin sani ya Jaheed ya kalli mutumin ya ce

"Kai wannan fa daga ina?"

"Kai ma ba kazo daurin auran ba ne?" Ya yi maganar cikin muryar su irin ta yan dabar.

"Eh! Ya Jaheed ya bashi amsa.

"To ka bawa uban amaryan, don ni ba sanin sa na yi ba." Yana gama faɗin haka ya ja mashin dinsa ya bar wajen. Da kallo suka raka shi, juya takaddan ya Jaheed yake sannan ya nufi inda su Abba suke, zuwa wannan lokacin jikin Abba ya jike sharkaf da zufa.

Zuwa lokaci Alhaji Taheer da abokinsa Alhaji Usman sun yanke shawarar a daura auren, har an soma gabatar da yadda ake auren.

Maganar Jaheed ce ta dawo da shi

"Abba gashi wani ya kawo wai abaka." Jaheed ya yi maganar yana mik'a masa takaddan.

Hannu Abba ya mika cikin faduwar gaba, ya ce

"Daga ina kuma ina mutumin?" Ya yi maganar yana juya takaddan.

"Yana bani ya wu ce."

"To aje wajenka har a gama daurin auran."

"A'a Alhaji ya kamata abude wannan takarda don sanin me ta kunsa, mu je daga waje." Alhaji Usman ya yi maganar.
Chapter 23 · 0% Book details