Sashe 19
Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To kawai ta amsa tana shigewa bedroom, ruwan sanyi ta sakarwa kanta zafin da zuciyarta take ta ɗan ragu ko yanzu tasan tana da matsayi a idon Dr tunda har ya yi mata magana cikin tausasa murya, duk da tarin rashin mutuncin da ta yi masa, bayan ta fito ta zauna ta ci ta koshi da yake ta yi sallah sai kawai ta koma toilet ta kuskure baki, rigar bacci ta zura ta nufi dakin Dr. Lokacin Dr na zaune cikin tunanin halin da Ameesha ke ciki, kalkalo murmushi ya yi ya ce "Barka da zuwa My Anee." "Hmm! Barkammu dai Hamman." Tana gama faɗin haka ta yi kwanciyar a kan gadon, wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyarta don ganin ta a kwance a gadon Hamman ɗinta.
Dan ɗago kai ya yi ya ce "Daga zuwa sai kwanciya? Ko dan hira baki taya mijinki." Kunya ce ta kamata don haka sai ta sauka daga gadon ta nufi inda yake zaune, kusa da kafafunsa ta zauna. Murmushi ya saki sannan suka soma hira irin ta mata da miji, idan ka ga yadda Aneesa ta saki jiki sai murmushi take yi ba ka taɓa cewa ita ce. Tsakanin miji da mata sai Allah nan take suka ɗinke, dama dai Aneesa kishin Dr ke damunta.
Gari na wayewa Aneesa da kanta ta shiga kicin ta haɗawa Dr break, bai fita ba sai da ya yi shirin zuwa office break din ya yi kafin ya yi mata sallama, yana fita bangaren Ameesha ya yi don ganin yadda ta kwana.
*****
Ameesha kam ganin bacci yaki zuwa mata sai ta mik'e alwala ta dauro mai kyau ta shiga nafilfili, ba ita ta bar sallayar ba sai bayan ta yi asbah sannan bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita.
Dr na shiga falon yaga bai ganta ba sai ya nufi bedroom ɗinta, amfani ya yi da fitilar wayarsa ya haska daki don gulob ɗin akashe yake, can ya hangota karshen gado a kwance kallo ɗaya zaka mata kasan sam bata jin dadin baccin, musamman yadda ta wani ta kure waje daya. A hankali Dr ke takawa har ya isa gadon, tsayawa ya yi yana kallon gadon, ko alama bai yamutse ba a gyare yake tsaf shi kansa dakin wani irin kamashi yake fitarwa, haka kan gadon lumshe ido ya yi ya buɗe sannan ya hau gadon bayan ya cire takalmarsa, kusa da kanta ya zauna a hankali yake shafa gefen fuskarta yana magana a kunnenta "Cutie tashi gari ya waye fa." Buɗe ido ta yi jin muryar Dr fes ta sauke idonta cikin nashi murmushi ta sakar masa tana kokarin tashi duk da idonta fal bacci.
"Baby yaushe ka shigo?" "Yanzu ban dade ba Cutie kina ta bacci, kamar ba ki yi kewata kamar yadda na yi taki ba?" Yana maganar ne yana jawota jikinsa. "Baby kenan kewarka da nayi ba zai fadu ba, nasan wanda ka yi ko kwatan nawa bai kai ba domin kana da Sister Aneesa kusa da kai." Cikin turo baki ta gama maganar. "Da gaske kin yi kewata?" Sauri ta daga kai, alamar "eh!" Tana tuna yadda bacci ya kwasheta a daren jiya. "Idan na dawo zaki gwada min irin kewata da kika yi, yanzu dai tashi ki yi break don gari ya gama wayewa, zan tafi office duk abin da kike buk'ata ki sanar min."
Mik'ewa ta yi tare da jawo hijjab ɗinta dake kusa ta sanya, tana faɗin "a dawo lafiya Allah ya tsare ya bada sa a." Maganar ta ta dire lokacin da suka isa kofar falo." Murmushi ya yi yana amsa addu'ar ta tare da manna mata kiss a goshi, sannan ya tafi.
Ciki ta koma sai da ta gama haɗa break ɗin ta, doya kawai ta soya da kwai sai ruwan shayi, bata zauna ba sai da ta gyara ko ina na bangaren, sannan ta shiga wanka shiryawa ta yi cikin wasu riga da siket wanda suka yi mata kyau jikinta ta feshe da turare sannan ta koma ta fara break. Karfe goma da rabi ta gama, duk ranta babu dadi kasantuwarta ita ɗaya a gidan, hijjab ta dauka bayan ta sanya ta fita daret bangaren Aneesa ta shiga, duk da Aneesa na zaune a falon amma ko ɗagowa ta kalli Ameesha ba ta yi ba. Sai cewa ta yi "Lafiya da safen nan?
Murmushin yake kawai Ameesha ta yi ta ce " lafiya lau gaisarki kawai na zo yi." "Na gode da gaisuwa, tunda kin ganni lafiya ai sai ki tashi." Ta dire maganar tana aika mata harara ta mike tare da barin mata falon ta yi shigewarta bedroom. Shiru Meesha ta yi tana kara mamakin halin Aneesa, girgiza kai ta yi tare da tashi ko alama bata nuna wani damuwa ba.
Tana komawa bangaren ta wayarta ta soma ringing, cikin sauri ta dauka da sallama, Dr ne ke tambayarta lafiyar ta, ita kuma ta tabbatar masa tana cikin koshin lafiya. Bayan sun gama wayar Meena ya shigo inda take shaida mata zata zo anjima, wani irin murna Ameesha ta yi, ai da sauri ta shiga kicin ta haɗa mata lafiyayyen abinci, hira suka sha sosai don yini Meena ta yi mata, da zata tafi kamar kar su rabu haka Ameesha ta ji.
Haka rayuwa ke tafiya kwanaki suna zama makonni haka makonni ke komawa watanni, su Ameesha zuwa yanzu watan ta biyu kenan a gidan Dr tana samun duk wani jin dadi a wajen Dr sam baya kaunar ganin ɓacin ranta, ta yadda da irin soyayyar da Dr ke mata, duk da Aneesa tana yi mata abubuwa marasa daɗi amma ita sam bata damu ba, don ita da zuciya daya ta dauketa.
Ranar safiyar wata Alhamis Dr ne kwance ya yin da Ameesha ta yi filo da faffadar kirjinsa sai wasa take da suman dake kwance luf a kirjinsa bayan sun gama shan love dinsu, wayar Ameesha ce ta soma ringing Dr wanda hannunsa yafi kusa da wayar ya mika mata, ganin Number din Meena yasa ta yi saurin ɗauka, wani irin kara ta saki irin na marna ta na faɗin "Yaushe? To gamu zuwa da Dr." Tana aje wayar ta ce "baby tashi ka yi wanka mu je gidan su Ummi Meena ta haihu."
"Kai Masha Allah! Abin farin ciki Allah ya raya, ya nuna min lokacin da Cutie zata haifa min yara." "Amin." Ta amsa tana saurin rufe fuska. "Kunya kike ji ne Cutie? Ki bar Jin kunya ina son yara ko nawa zaki haifa ba zan taɓa gajiya da ke ba please Maryam karki sha wani abu don hana daukar ciki." Da muryar tausayi ya gama maganar.
Tausayin Dr ne ya kama Meesha ta ce "in sha Allah babu abin da zan sha Allah ya bamu masu albarka." "Ameen matata yar albarka." Yana gama fadi ya shige toilet, itama ɗakinta ta wuce ta shiga wanka bata jima ba ta fito kai tsaye kicin ta nufa ta sama masu abin break kunun gyada ta dama sai ta soya doya da dankalin turawa, komai ta jera a dining bayan ta gyara kicin ɗin fes baka taɓa cewa an yi aiki a ciki.
Kai tsaye bedroom ɗinsa ta nufa, a kwance ta same shi yana game a wayarsa, kan gadon ta hau tare da amshe sayar ta ce "baby break is ready." A shagwaɓe ta yi maganar. Tashi ya yi yana murmushi ya ce "An gaida Cutie mu je mu gama har an soma kira na." Yana rike da hannunta suka isa, a natse suka kammala break ɗin kwashe kayan ta yi ta kai kicen sai da ta wanke ta gyara komai kafin ta dauki gyalen ta. Bangaren Aneesa suka shiga suka mata sallama.
Cikin farin ciki Ameesha ta shiga gidansu, har bangaren Meena Ameesha ta kai Dr da kanta ta shiga bedroom ta ɗauko masa jaririn tukeke da shi tubarkallah ta kaiwa Dr, sosai Dr ya rike dan a hannu kamar kar ya rabu da shi, domin Allah ya yi Dr Asmad da san yara, sai da ya yiwa su Ummi barka kafin ya tafi da cewa idan ya dawo aiki zai biya ya dauketa.
Rayuwar farin ciki Ameesha ta yi a gidan su, kaf yan'uwanta sai da ta gansu sun nuna irin kewarta da suka yi babu ma kamar Haydar da yamma Dr ya dauketa suka tafi gida, sai dai fa Ameesha da ciwon kai ta koma, tun tana daurewa har Dr ya fahimta hankali tashe yake tambayarta "Cutie lafiya kuwa?" Da kyar ta ce "kaina ke ciwo." "Ayya sannu." Ya yi maganar da muryar tausayi sannan ya nufi inda yake aje magani don ya bata ta sha yana cikin duba maganin sai ga wani ya fado da sauri ya kai hannu ya dauko yana gama karantawa ya furta " *Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!* Ni Ameesha zata ciwa amana?" Da sauri ya dafe kansa dake barazanar rabewa biyu.
Tofa Dr me ka gani ne haka, har kake furta irin wannan maganar ga Cutie din ka Ameesha? Ku biyo alkalamin Zulayheart Rano don jin yadda zata kaya don koni bana ce ga abin da ya gani ba .
*Don Allah ku yi min addu'a wallahi bani da lafiya sosai*👏🏻
_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:18 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*
©
_*ZULAYHEART RANO*_
*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*
_Ina dai bada hak'urin rashin ganin post kullum wallahi dai abubuwa ne sai a hankali amma zan fara k'ok'ari ina typing ɗin. Matsalar baku yi comment._
*44*
Zama ya yi kansa na wani irin sarawa, juya kwalin maganin yake yana karawa ya yi kusan minti biyar a wajen sannan ya ɗauki maganin ciwon kan ya fita falo inda Ameesha take, mika mata ya yi bayan ya yi kokarin danne zuciyarsa. Amsa Ameesha ta yi sam bata kula da yanayin da yake ciki ba tunda idanunta a rufe suke, sai dai ta yi mamakin ganin ya mika mata maganin ba tare da ya bare ba, bai saba yi mata haka ba sannan kuma babu ruwa.