← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 54

Sashe 27

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Dr ya ina faɗa maka maganar gaskiya kana karyata ni, ka je ka tambayi Bobbo ko Nenne zasu sanar ma shekaran jiya da kai aka daura auren Ameesha." Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa.

Da kallo Dr ya bi wayarsa, cikin zuciyarsa yana mamaki da tunanin maganar Aneesa da ta Hafiz, Aneesa ta ce Nenne ta sanar mata, shi kuma Hafiz ya ce ya tambayi Nenne, abin da ya daure masa kai shi ne "ɗazun da zai dawo gida sai da ya biya ta gidan don ya ɗauko Aneesa a tunanin sa tana can gidan, kuma bai ji Nenne ta sanar masa da makamanciyar wannan maganar ba, kai shi kam bai yadda da wannan maganar ba."

"Yanzu me abin yi?" Ya yi wa kansa tambaya.

"Ka fara zuwa ka lallashi Aneesa tukun." Wata zuciyar ta bashi amsa.

"A'a kar ka je domin kuwa a yadda ta ɗauki fushin nan ko ka je bata sauraron ka." Wata zuciyar ta yi saurin tunasar da shi.

"To mai zan yi, menene mafita?" A fili ya yi maganar.

"Wajen Nenne da Bobbo." Wani bangare na zuciyarsa ta bashi amsa.

"Yes! Sosai ya ji ya yi na'am da shawarar da zuciyarsa ta bashi. Cikin kwarin gwiwa ya mik'e yana fita motarsa ya ɗauka tare da bata wuta sai gidansu Nenne.

Ko tsayawa kyakkyawan fakin bai yi ba, ya fita daga motar, cikin gida ya nufa da sassarfa a wannan gaɓar sallama ma ta gagareshi da Nenne ya yi karo ta fito daga hanyar kicin.

Kallonsa ta yi tare da girgiza kai ta ce

"Lafiya kuwa?"

"Lafiya lau Nenne." Ya bata amsa.

"An ya kuwa lafiya, kalli fa ta yadda ka shigo?"

Sosa kai ya fara da keys din hannunsa ya ce

"Allah Nenne babu komai, dama dai tambayar ki zan yi?"

"Tambaya?" Wacce irin tambaya kuma? Ko da yake zauna in ji me ke tafe da kai?"

Zama ya yi tare da lankwashe ƙafafunsa ya sun kuyar da kai, sai dai me tambayar da ya ke niyyar yi ta ki fitowa. Ita dai Nenne zuba masa ido ta yi tana sauraron abin da zai ce, ganin ya yi shiru sai ta gyara zama ta ce

"Asmad wai kuwa ka je gidansu Ameesha kuwa?"

Ɗago da kai ya yi yana kallonta ya ce

"Gidansu Ameesha? Me zan je yi mata bayan yanzu tana inuwar wani, ko kin manta na ce an daura auren ta da wani?"

"A'a ban manta ba, sai dai yana da kyau ka lek'a domin duba a wani hali ta ke, saboda wannan ɗin ya rataya a wuyar ka ne."

Da amaki ƙarara a fuskarsa yake kallon Nenne bakinsa har yana rawa ya ce

"Ya rataya a wuyana? Nenne ban gane nufin ki ba?"

"Eh! Haka nake nufi, yau kwana biyu da Ameesha ta zama a karkashin inuwar ka, ma'ana dai Maryerm Taheer wato Ameesha ta zama mata a gare ka."

Kallon Mahaifiyarsa ya yi a karo na barkatai, ganin yadda ta dire maganar sam babu alamar wasa ya sa shi ya yadda, ai da sauri ya tashi tare da yin sujada ga Allah don nuna farin ciki, yana ɗagowa ya zubawa Nenne ido kallo ɗaya zaka masa kasance wa yana cikin zallar farin ciki, musamman yadda fuskarsa ta nuna.

Kasa furta komai ya yi sai wani fara'a da murmushin da ke k'arasawa fuskarsa kyau ya yi, cikin zuciyarsa kam godiya ya ke ga Allah. Muryar Nenne ya ji tana faɗin

"Kaga yanzu dai ka tashi ka je gidan nasu domin duba wani hali take ciki."

"To." Tare da mik'ewa yana faɗin Nenne sai na dawo.

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:00 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAIHEART RANO*

*_Bismillahir Rahmanir Rahim._*

*_Allah ina rokon ka don karfin ikon ka, kabani iko kamar Yadda na fara rubuta littafin nan lafiya Allah kasa in kammala rubutawashi lafiya_*

*1*

Zaune yake cikin kasaitaccen falonsa wanda aka tsara su da manya-manyan kujeru ne na alfarma. Kallo daya zaka yiwa falon ka san ba karamin dukiya aka narka ba. shi kansa kafet din falon ba duka gidaje ake samun irinsa ba sai gidan wane da wane.

Hannunsa ya mika tare da dauko jaridar Leadership daga kan wani kyakykyawan teburin dake kusa dashi, ya bude tare da soma karantawa. Cikin wata irin tafiya take taka steps din tana saukowa fuskarta dauke da murmushi, jikinta sanye da wata rigar bacci wandda bata gama rufe mata cinyoyi ba, kanta ko dankwali babu. Kai tsaye wajensa ta nufa. Shi ma tunda ya hangota fara'ar fuskarsa ta karu. Bata zame ko'ina ba sai inda yake zaune, ta zauna tare da dora kanta saman kafadarsa, cikin shagwab'a tace
"Abbana barka da safiya"
Murmushi ya yi yace "Barka dai uwata, fatan kin tashi lafiya?"
Dariya ta yi tace " Lafiya lau Abbana."
"Madallah, fatan babu wata matsala?" Ya yi tambayar yana kallonta.

"Innalillahi.... Ni Halimatu! ke kuma Amesha kina daukan maganata kuwa? sau nawa ina maki maganar ki daina fitowa a haka?" Maganarta da suka ji kamar daga sama ne ya hana ta ba Abban nata amsar tambayarsa, duk suka juyo ga mai maganar.

Turo baki tayi tare da kunkunai "To ni Ummi wai shikenan mutum ba zai sake ba shi da gidannsu?"
Dakuwa Ummin ta watsa mata tare da daure fuska tace "za ki tashi kije ki suturta jikin ki kosai na bata maki rai?"

Ganin fuskar Ummin ba wasa yasa ta mikewa cikin takaici. Abbanta yace "Haba Hajiya! me yasa kullum sai kin rika takurawa Yarinyar nan ne? Ko baki san har yanzu karamar Yarinya take ba?"

Wani takaici ya rufe Ummi ta ji kamar ta gaurawa mijin nata mari "Haba Alhaji, ta yaya zaka ce kar na yiwa Ameesha fada in ta yi ba dai dai ba? Yarinyar nan fa kullum kara girma take yi amma babu hankali a tare da ita. Ji fa irin kayan da take fitowa falo dasu, by mistake ayi bako ta fito haka ai kunya zamu ji....."

Ya dakatar da ita da hannu "Look! Hajiya ban son dogon turanci, gida dai nawa ne kuma Ameesha gidan ubanta take, don haka babu mai takura mata. Ke kullum baki da abokiyar fada sai yar cikinnki? wallahi wani in ya shigo sai ya yi tunanin bake kika haife taba, musamman da kullum fada kike mata. Kuma kina maganar bako, ai ba mai shigowa falon nan sai da izini. Gidan nan duk muharramanta ne, basai ta rika sa kaya masu nauyi ba."

Takaici ya rufe Hajiya, Wanda har ta kasa furta komai, sai aje masa cup din coffee din tayi ta nufi bedroom dinta. Tabbas ta san duk wani abu da Ameesha takeyi da izinin mahaifinta, don shine baya kaunar a fadi laifin Yarinyar. Allah ya sani ina iya bakin kokari na wajen bama Yarinyar tarbiyya, amma taki daukan duk wani nasiha ta, ta fada a ranta.

Ameesha tana shiga bedroom dinta toilet ta zarce ta sallo wanka. Tana fitowa ta zauna gaban dressing mirror ta soma tsantsara kwalliya. Tana gamawa ta shirya cikin wata bakar doguwar riga, mai masifar kyau, tayi rolling dankwali a kanta. Iya kyau dai kam Ameesha tayi, kamar a sace a gudu. Kyakykyawa ce sosai yar shekara goma sha takwas. fara ce amma ba sosai ba. Ta samo asali da kyau ne wajen mahaifiyarta, komai nata irin na mahaifiyar ne. *MARYAM TAHIR* kenan inkiya kuma Amesha Yarinya yar gatan Abbanta.

Wayoyinta ta kwasa daga kan gado ta sanya takalminta mai kyau, sannan ta fita falon don yunwa take ji sosai. wani murmushi ta saki ganin har a lokacin Abbanta na zaune a falon
"Wow! Babyna kinyi kyau."
Abban ya fada yana nuna farin ciki.
Dan turo baki tayi ta ce "Na gode Abban Ameesha. Abba so fa nakeyi naje saloon a wanke min kai" Cike da shagwab'a ta karasa maganar.
"Ok babu damuwa my baby. Yanzu dai je ki fara yin break don nasan kina jin yunwa. In kin gama sai ki tafi."

"Abba nifa ba kudi a hannuna, ka ban kudin da zanyi amfani da shi"

"Sai dai kije da ATM Card don banda wasu kudi masu yawa a gida" Ya bata amsa a lokacin da yake kokarin mayar da hankalinsa ga jaridar da ke hannunsa.
"No Abba, Gaskiya ba zan iya bin layin ATM ba, mutum yaje ya yi ta tsayuwa" Ta yi maganar kamar zata yi kuka a daidai lokacin da Hajiya Halima mahaifiyar Ameesha ta iso inda suke.

"Yawwa Hajiya muna da bukatar kudi in kina da su a hannu" Alhaji Tahir ya fada, yana rufe jaridar.

"Wani irin kudi kuma Alhaji?" Hajiya ta tambaya cikin nuna rashin fahimta "Baby ce zata saloon kuma wajena babu kudi a gida, ki bata 30 thousand naira kila su ishe ta"

Zaro ido Ummi tayi tace "Alhaji dubu talatin fa kace! Da su zata wajen saloon din?"

"Eh, saboda zata biya ta yiwo shopping. ko kuma dai bata fifty zaifi"

Jinjina kai tayi tare da cewa'
"Ai bani da su"

"Zan maida maki kudinki Hajiya"

Juyawa tayi ta nufi bedroom dinta, tana Kara mamakin halin mijin nata.

Ameesha kam sai da ta kammala break din tsaf, kana ta baro dining tabke din. Wajen Abban ta taje tace "Abbana na gama"

"Ok je ki amshi kudin wajen Umminki, 50k ne ai zasu ishe ki ko? Sai ki siyo yan abubuwan bukata da abinda ya rage."

Daga kai tayi kafin ta nufi bedroom din Ummin. Ta yi Sallama ta shiga. Hajiya Halima dake zaune ta amsa. "Ummi ki ban kudi inji Abba" Ameesha ta fada.

Girgiza kai Ummi ta yi tace "Allah ya shirya min ke Ameesha, wai yaushe zaki hankali ne?" Ta karasa maganar tana mika mata kudin.

Amsa tayi tare da yin waje. tana zuwa ta aje masa kudin a kusa da shi. Cikin muryar kuka ta ce " Abba ba na son kudin nan"

Hankalin sa ya tashi da ganin hawayen tilon diyarsa mace, yace "Uwata me ya faru?"

Jikinsa har wani rawa yake. "Ba Ummi bace bayan ta ban kudin tace Wai Allah ya shirya ni.........."

*_Yawan Comment dinku zai sa ni cigaba..._*

*_Yar Mutan Rano._*
[10/8, 8:00 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAIHEART RANO*

*2*
Chapter 27 · 0% Book details