Sashe 18
Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mu je ki ci abinci sai ki bani labarin missing dina da kika yi." Zaunar da ita ya yi a dining din sannan ya ɗauki plet ya cika da abinci
"Ina zuwa Cutie zan kaima Aneesa abinci, karki fara ci fa don tare za mu ci." Yana maganar yana tafiya.
"To! Kawai Ameesha ta amsa.
Kamar ko da yaushe yanzu ma kofar ta abude take shiga cikin falon kawai Dr ya yi bakinsa dauke da sallama, ko ɗago kai ta kalleshi bata yi ba sai ma ɗaukar remote control ta yi tana kara maganar t.v
Murmushi kawai ya yi lamarin Aneesa sai dai addu'a, kullum abin gaba yake ba ya sauki kusa da ita ya isa tare da aje plet ɗin ya ce "Ga abinci nan ki ci my Anee don nasan kina tare da yunwa." Yana gama faɗa ya sa kai zai fice.
Cak! Dr ya tsaya jin maganar da Aneesa ke yi.
"Zo ka ɗauki abincin ka bana ci, ko an ce ma ni mayunwaciya ce?" Ta kai karshen maganar tana watsa masa harara.
Takowa ya yi a hankali har inda take zaune ya sassauta murya ya ce
"Look Aneesa ya kamata kisan da wa kike magana, domin na fi kowa sanin ke ba mayunwaciya ba ce, amma hakkin ciyar da ke yana kaina don haka ga abinci nan na kawo maki, ko kici ko ki zubar ruwanki." Gama maganar sa ya yi dai dai da soma tafiyarsa.
Mtsww! Aneesa ta ja tsaki bayan fitar Dr daga falon, gaba daya haushinsa take ji, ko birgeta ba ya yi yanzu.
Yana takaicin halin Aneesa sam bata da halin kwarai ita kenan kullum cikin masifa, kai Allah ya kyauta, sai da ya daidaita nutsuwarsa kafin ya shiga falon, inda ya bar Ameesha zaune a nan ya sameta tana aikin Game a wayarsa.
"Sorry Cutie na barki ke kaɗai ko?"
A je wayar ta yi tana sakar masa murmushi bata iya cewa komai ba, saboda wani irin kallo da Dr ke aika mata, take wani irin kasala ta saukar mata, zama Dr ya yi bayan ya zuba masu abinci kan cinyarsa ya yi mata mazauni da kan sa ya rika bata har sai da ta koshi, sannan ita ma ta shiga ba shi, suna yi suna zuba soyayyar su har suka kammala, kwashe kayan Meesha ta yi ta kai kicin, sannan ta gyara inda ya ɓaci Dr kallonta kawai yake cikin wani irin shaukin soyayya, ya yadda yana son Ameesha so irin wanda bai taɓa yiwa wata ba, bai san time da ta iso wajensa ba sai jinta ya yi ta shige jikinsa.
"I love you Meesha." Dr ya faɗa yana kara shigar ta jikinsa
"I love you too." Ameesha ta ba shi amsa, wani irin tashi zaune ya yi wannan shi ne karon farko da ya ji Ameesha ta furta tana sonsa ita ma.
"Kina so na yaushe kika fara so na?" Dr ya yi tambayarsa da mamaki.
Babu kunya ta ce
"Tun ranar farko da muka soma haɗuwa a sahad store na fara sonka Dr."
"Kina nufin a lokacin ɗaya muka yi *MUSAYAR ZUCIYA*? (Littafin Hajja).
"Kwarai kuwa sai zuciyoyinmu ta soma mana *BAHAGGON TUNANI* (littafin Badeeyar beauty queen).
"Ba shakka *SANGARTAR* ki ta taka muhimmiyar rawa wajen hanamu mallakar juna tun tuni." Ya yi maganar yana lakace mata hanci.
Turo baki ta yi ta ce
"To amma duk *LAIFIN WA?* (Littafin Khadija S Muhammad).
"Dukkan mu muna da laifi tunda mun kasa bayyana soyayyar mu a fili, sai faɗa da muke da juna sam bama jituwa, lallai Allah shi kadai yasan abinda ya ɓoye cikin tarayyar mu." Ya dire maganar yana manna mata kiss a kumatu.
"Allah ya bamu hak'urin zama da juna lafiya. Ameesha ta faɗa tana kara shigewa jikinsa idonta lumshe kamar mai jin bacci.
"Amin." Ya amsa yana ci gaba da wasa da jikinta a haka bacci ya kwashe su, ba su farka ba sai bayan la'asar, Dr ya fara farkawa ya sauke idonsa kan agogon da ke manne a bangon falo, da sauri ya tashi zaune ganin lokacin sallah ya gota. Tashin Ameesha ya soma yi tana farkawa suka shige bedroom Dr niyyar wanka ya yi, don har ya ɗaura towel a kugunsa ya zubawa Ameesha ido ganin tana niyyar kwanciya
"Tashi mu yi wanka mana Cutie time na tafiya fa."
"No! A fito lafiya zan yi nawa."
"Ba ki yin wankan kenan?"
Kai ta gyaɗa tana gyara kwanciya, Dr bai ce komai ba ganin ta rufe ido, ai da sauri ya sureta bai zame da ita ko ina ba sai cikin toilet cikin kwamin wanka ya sakata, yana sanya ta ta mik'e zaune jinta cikin ruwa tsundum kallonsa ta yi a shagwaɓe ta ce
"Please Dr me haka?"
"Soyayya ce haka." Ya bata amsa yana shiga cikin kwamin shi ma. Shiru Ameesha ta yi masa tana jinsa ya gama cire mata kayan jikinta wanka ya mata tas yana yi yana love wanda Meesha ko kallonsa taki balle ta taimaka masa, a haka ma ya ji dadi yana gama mata ta daura alwala cikin towel ya nadeta da kaita bedroom, cikin sauri ya kammala wankan ya yo alwala ko da ya fito ya sameta har ta gama shafe jikinta da mai ɗaya daga cikin jallabiyar Dr Ameesha ta san ya suka gabatar da sallah.
Bayan sun idar Dr ya je ɗakinta kaya ya kwaso mata wanda zata saka, three kwatan wando da karamar top mai hannun bes, tana kwance Dr ya gama mata komai har shiya ta, ya feshe mata jiki da turaruka masu sanyin kamshi, woww gaskiya Ameesha ta yi kyau, Dr ma cikin kananan kaya ya shirya three kwata da singileti, sosai kayan suka amshi jikinsu, falo suka koma inda suka kunna tv suna kallon tashar Bollywood.
Karfe shida saura direban gidan Nenne ya kawo masu abinci, Dr da kan sa ya fita ya kwaso, a dining suka shirya komai
[10/8, 8:18 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*
©
_*ZULAYHEART RANO*_
*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*
*43*
Haka Ameesha ta sha kukanta daga karshe ta lallashi kanta, a three sitter ta kwanta tana mai ambaton sunan Allah a hankali wata nutsuwa ke saukar mata. Dr kuwa ko da ya shiga bangaren Aneesa kwance ya sameta kamar ko da yaushe tana aikin latsa waya, ko kallo Dr bai isheta ba balle ya samu arzikin sannu da zuwa. Zama ya yi tare da bismillah yana faɗin "my Anee barka da hutawa."
Bata amsa ba sai dan dagowar da ta yi ta kallaceshi, kamar wacce aka tsikara kuma sai ta mik'e tare da shigewarta bedroom. Girgiza kai kawai Dr ya yi shima ya shiga bedroom ɗinsa, kayan jikinsa ya rage sannan ya nufi toilet alwalarsa ya dauro ya zira jallabiya sannan ya nufi masallaci, bai shigo gidan ba sai bayan ishsha da tek away ya shigo da su, a dining ya aje ledojin babu kowa a falon hakan ya nuna Aneesa bata fito ba, bai bi ta kanta ba don yasan masifa take nema da shi shi kam ba zai biye mata ba.
Leda ɗaya ya ɗauka ya nufi bangaren Ameesha, kamar yadda ya zata kuwa a falo ya sameta tana zaune ta buga uban tagumi jin an bude kofa yasa ta yi saurin ɗagowa ido hudu suka yi da Dr wani irin lallausan murmushi ta sakar masa, sai da gabansa ya fadi da yadda yaga idanunta sun kumbura a lamar ta sha kuka, "Cutie lafiya kuwa kalli idonki fa?" "Babu komai fa baby." Ameesha ta ba shi amsa tana amsan ledar da ya shigo da ita.
"An ya kuwa Cutie?" "Allah nifa baby babu wani abu." A shagwaɓe ta yi maganar. "Ok tun da babu komai ai shi kenan, amma Please abar kukan haka nan ya isa." "Na daina." "Promise?"Dr ya fada yana kallonta. Murmushi ta saki ta ce "Yes promise." "Ga abinci nan ki ci sai ki kwanta, karki manta da addu'a fatan kin yi sallah?" "Eh na yi." Ameesha ta bashi amsa. Fita Dr ya yi yana mata sai da safe, bayan fitar Dr abincin ta jawo hankali ta soma ci, duk da dai turawa kawai take sam bata wani jin dadin sa, bata ci da yawa ba ta ture shi gefe tare da hamdala ga Allah.
Dr kam ko da ya koma falon Aneesa bata fito ba, don haka sai ya ɗauki leda daya ya nufi bedroom ɗinta akwance bisa gado ya sameta, cikin nutsuwa ya zauna a bakin gadon yana kallonta a hankali ya furta "My Anee." Sarai tasan da shigowar sa sai ta ɗauke kai, jin yadda ya ambaci sunanta sai da wani abu ya tsirga mata tun daga tsakar kai har yan yatsun kafarta, amsawa ta yi ba tare da ta tashi ba. "Tashi mu yi magana." Fuska babu walwala ya yi maganar.
Tashi ta yi tare da kauda kai gefe taki ko da kallonsa, murmushi ya yi ya ce "Aneesa faɗa min laifin da na yi maki kike fushi dani?" Ya ida maganar yana kafeta da ido. Shiru ta yi kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce "Ni baka min komai ba." "Ban yi maki komai ba kike fushi da ni Aneesa?" Cike da mamaki yake tambayarta. "Eh gaskiya na faɗa maka babu abin da ka yi min." Ta faɗa tana mik'ewa. Sam Dr baya son jan magana don haka sai ya ce "Shi kenan tunda kika ce haka, amma nasan mutum haka kawai bazai fara fushi ba tare da an yi masa komai ba." "Ni dai Hamman na faɗa maka baka min komai ba." "Ok dawo ki zauna, kila babu abin da kika ci ga abinci nan idan kin gama ina jiranki a bedroom."