Sashe 48
Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Inna lillahi! Wannan wacce irin masifa ce? Kuma kana sane baka dau mataki ba" "Ban ɗauka ba sai yanzu nake son ɗauka akansu duka, domin Ameesha ma sau biyu ina ganin maganin a bangaren ta." "Au har Ameesha din ma?" Hafiz ya yi saurin katse shi. "Tabbas, na farko ranar da ta dawo daga gidansu, na biyu shekaran jiya da dare, wallahi bazan ɓoye maka ba na Ameesha ya fi bani haushi domin yadda na dauketa ba haka ta ɗauke Ni ba, abin haushi kuma tana gaya min bata taɓa sha ba ka ji wani rainin wayau bayan na gani da idona..." "Amma Dr ka binciki na Ameesha kuwa? Ban ji ajikina Meesha zata ma haka ba... Idan har Aneesa ka sameta da laifin dumu dumu Ameesha fa? Bana jin zata iya aikata maka makamancin haka..."
Mtsww Dr ya ja tsaki "ya Ina sanar maka abu kana neman karyatani...? "Ka taɓa ganin ta da maganin a hannu tana sha?" Hafiz ya yo saurin jeho masa tambaya. "Look Hafiz bana son irin wannan tambayar please." "Am sorry to say Dr Asmad amma wallahi na yi rantsuwa Ameesha ba zata iya abin da kake tunani ba, shin ina hankalinka ya ke da baka bincika ba? Shin menene na saurin sanya zargi cikin rayuwar aurenku? Ina mai baka shawara ka je ka yi bincike domin tabbatar da abin dake wakana a gidanka." Wannan karan a zafafe Hafiz ya gama maganar.
"Bincike! Hmmmm ai ba sai na yi bincike ba, domin amsar a fili take na gani da idona, kuma ba sharri na yi mata ba, don haka Hafiz sai anjima." Yana direba maganar ya mike da niyyar barin falon. "Ka je Dr amma ka yi gaggawar daina wannan fushin tun kafin ta kai ka ga dana sani." Bai fasa tafiyar ba sai da ya kai kofa kafin ya juyo ya kalli Hafiz ya ci gaba da tafiyarsa.
Tafiya yake a mota maganganun Hafiz na yi masa yawo a k'wak'walwa, ya rasa ta ina zai fara matsalar sam Nenne bata sakar masa fuska balle ya je can ya samu mafita, to kuma idan ya je sangartacciya tana can haka zata sanya shi gaba da kuka mtsww ya ja tsaki a karo na barkatai.
****
Haka kwanaki ke tafiya yau watan Ameesha uku a gidan Nenne, tattali Nenne ke bama Ameesha sam bata barin ta da damuwa, ita dinma tana jin dadin zama da Nenne domin tana samun kula a wajenta har wata kiba Ameesha ta yi, ba lallai ne mutum ya kula tana da ciki ba, bata neman abu ta rasa duk kankantar sa Ummi da Abba sau uku suna zuwa duba ta, sun yi farin ciki da jin Autar su na dauke da ciki Ummi har tana tsokanarta "Oh! Autar Ummi yanzu kuma dole a rage sangarta domin kin kusa zama uwa." "A'a Hajiya Halima Ameesha ai sangarta ba zai barta ba yar gatan Abba da Nenne da Bobbo ne fa, ta ya zata daina sangarta." Gaba daya suka saki dariya Abba ya ce "Faɗa mata dai ai ba a canzawa tuwo suna sangarta kuwa uwata yanzu ta fara ko a gaban kanwata ko kanina (yaron Meesha ko yarta Abba ke nufi.) Kar ki fasa komai uwata. Murmushi ta yi bayan ta gama tunawa.
Dr ya yi na cin duniya Nenne ta bari Ameesha ta koma amma ta ki yarda, da taga zai dameta sai ta soma haɗe girar sama da ta kasa idan ta kasa gaisuwa ma da kyar yake samun ta amsa balle ya samu damar ganin Ameesha, har ya ɗan zama abin tausayi. Duk wannan abin da ake yi Aneesa bata taɓa sanin Ameesha tana gidan Nenne ba, domin ita bata wani damu da zuwa gidan ba kuma ko taje bata dadewa take tafiya, Ameesha kuma kullum cikin bedroom take sai kuma garden in tana son shan iska take zuwa.
A gaggauce ya yi parking motarsa ko tsayawa rufe motar da kyau bai yi ba, domin har ya je asbiti ya yi mantuwa shi ne dalilin dawowarsa, kai tsaye bangaren Aneesa ya yi, yana tura kofar ta buɗe kutsa kai cikin falon ya yi duk sallamar sa bai samu an amsa ba, yasan har matar gidan shi yasa bai damu ba ya yi wucewar sa bedroom ɗinsa, ya ɗauko file har zai fita sai ya fasa don yana son ya sanar mata da ta shirya idan ya dawo su je gidan Nenne, abin da kunnuwan sa suka soma jiyo masa ne yasa shi daskarewa...
*YAR MUTAN RANO*
*SANGARTA*
©
_*ZULAYHEART RANO*_
*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*
*48*
Da kyar ya janyo numfashin sa kafin ya gyara tsayuwa yana ci gaba da sauraren maganar Aneesa "Rukky wallahi bazan ɓoye maki ba ina cikin damuwa wacce ta amsa suna damuwa, ɗazun bayan Dr ya fita na sai nima na fita domin dama ina son komawa wajen Dr ya dubani, a halin da ake ciki so nake na samu ciki amma kin san ne Dr Ashrab yake faɗa min?" Daga can bangaren Rukky ta amsa da "A'a." Aneesa ta ci gaba cikin raunin murya "cewa ya yi mahaifata ta yi rauni dalilin magungunan da na rika sha ba za ta iya rike ciki ba." Wannan karon da kuka mai sauti ta gama maganar.
"Ki yi hakuri Anee kuma ai wannan ba wani abin damuwa ba ne da har za ki rika tada hankalin ki..." "Dole na tada hankali Rukky duk ke ce silar shigata duk wata matsala, yanzu ga abin da ya faru na yi nadamar bi yewa shawarar ki..." Tana gama faɗin haka bata jira jin me Rukky za ta faɗa ba ta kashe wayar. Tana ci gaba da kuka. Dr dake tsaye ya share zufar da ya tsatsatsafo masa "Lallai ina cikin masifa da jalala, Aneesa kin cuci kanki yanzu ga abin da ya faru dole ya dau mataki kan Ameesha, domin ba zai taba bari ta yi wa kanta illa irin ta Aneesa ba." Ransa a matukar ɓace ya bar kofar, sai da ya shiga mota kafin ya kirata bayan ya danne duk wani abu dake ransa.
Ringing biyu ta dauka cikin muryar kuka "Hello Hamman." Shi ne abin da ta iya faɗa. "Aneesa lafiya kuwa na ji muryar ki kamar wacce ta yi kuka?" "Lafiya lau sai dai ciwon kai ne ya dameni, amma nasha magani." "Ok dama na kira ne in sanar maki ki sameni a asbiti yanzu." "To." Ta amsa jiki a sanyaye.
Cikin mintinan da ba zasu gaza talatin ba Aneesa ta gama shiryawa, doguwar riga ta sanya ta yafa babban gyale, wayarta kawai ta rike a hannu sannan ta nufi asibitin Dr Asmad, bata dauki mota ba sai fita ta yi ta hau a dai dai ta. Mitina goma ta isa asibitin daret ofishin Dr ta nufa nocking ta yi daga ciki Dr ya bata umarnin ta shiga, shiga ta yi tare da yi masa sannu sannan ta zauna suna fuskantar juna.
Sun yi kusan minti biyar a haka idon Dr a kan fuskar Aneesa yana kallonta da nazarin yadda zai fara mata magana. A jiyar zuciya ya yi tare da ambaton sunanta "Aneesa." A ɗan razane ta amsa da "na'am." Muryarta na rawa. "Lafiya kuwa?" Ya jefa mata tambaya." "Lafiya lau Hamman." "Ok dama ina son in duba ki ne..." "Duba Ni Dr? Ai lafiya ta lau." Ta yi saurin katse shi. "Eh na san lafiyar ki lau amma ya zama dole na duba ki Aneesa saboda har yanzu tun bayan aurenmu ban ji alamar ko da ɓatan wata kin yi ba, kin ga ya kamata na duba ki domin gane ko akwai wata matsala." "No! Dr ka barni kawai lafiya lau nake ciki kuma Allah ne bai kawo ba, mu ci gaba da addu'a har Allah ya kawo." Ta dire maganar tana kokarin mai da hawayen ta.
"Na san lafiyar ki lau Aneesa amma ki bari na duba ki." Da kyar ya shawo kanta har aka yi mata komai, jikin Aneesa ban da tsuma babu abin da yake don tsabar farga, ta sa a ranta matukar Dr ya gane gaskiya zamanta ya kare a gidansa nan da nan sai zazzafan zazzaɓi ya saukar mata. Taimakon gaggawa Dr ya bata sannan bacci ya dauketa.
Dr Asmad na zaune ya zuba mata ido cike da takaicin halinta Nurse ta yi nocking, jiki babu kwari ya bata umurnin shigowa, mika masa result ɗin da aka yi wa Aneesa test ta yi. Zuciyarsa ta tsinke lokacin da ya yi karo da irin bayanin da Aneesa kewa kawarta a waya ce ya tabbata, sosai ya yi takaici da ganin sakamakon haka. A dana takaddun ya yi don baya son ta san ya san sanadin rashin lafiyar mahaifarta. Bayan ta farka tea ya Bata da magunguna lokacin biyar har da rabi don haka suka nufi gida, duk yadda ta so ta karanci wani abu game da shi abin bai yiyu ba, ganin har sun shiga gida da kansa ya haɗa mata ruwan wanka da abinci, suna zaune a falon Aneesa ta yi kasa da kai ta ce "Hamman wai me ke damuna ne, har yanzu baka ce min komai ba?" Murmushi ya tattaro don baya son ta ji komai, ya ce "Haba Anee me kike son sa ni bayan wanda kika sa ni kuma?" "Wanda na sa ni Hamman?" A razane ta yi tambayar. "No! Ke kina da saurin daukar zafi, bana son ki tayar da hankali domin baki da matsalar komai kuma rashin samun ciki lokaci ne, da zarar lokacin ya yi za ki samu ki kwantar da hankalin ki kin ji Anee." Da sigar lallashi ya yi maganar. Ganin yadda ya yi maganar yana lallashinta sai ta ɗan saki jiki. Haka dai rayuwa take tafiya musamman ta bangaren Aneesa da yanzu damuwarta ta ɗan ragu.