← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 54

Sashe 50

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwa mai daɗi ake a gidan Dr Asmad, zuwa yanzu dai Aneesa ta rage zafin da ta dauka da Meesha domin yanzu har zuwa take bangaren Ameesha su gaisa. Hankalin Dr akwance ba ya da wata mata, babban burinsa shi ne yaga Ameesha ta sauka lafiya don cikinta ya shiga watan haihuwa kuma ko da yaushe tana iya zuwa. Kamar kullum suna zaune suna hira duk da yau Dr ba a bangaren ta yake ba ya zo mata sallama ne, duk hiran da suke dauriya kawai ta ke domin tun safe take jin alamar ciwo sai dai ba ya wani matsa mata shi yasa ba ta damu ba amma yanzu abin yana neman ya yi yawa, Dr ya kula da halin da take ciki tun shigowar sa zama ya yi tare da riko hannunta ya ce "Cutie an ya yau kam lafiya?" "Me ka gani baby?" "Komai ma na gani haihuwa ce gata nan." "Hmmmm! Baby kenan wai haihuwa ce to ina kaga haihuwar?" "Wajen autar Ummi." "A'a ni kam babu wata haihuwa haba haihuwar kamar wani shan ruwa Allah babu komai."

Gyada kai Dr ya yi badan ya yadda da maganar ta ba, mik'ewa ya yi don ya sanar da Aneesa halin da ake ciki kar ta ji shiru, yana fita jikin Ameesha ya hau tsuma ciwo wanda tun da take bata taɓa ko da jin irinsa ba ya taso mata gadan gadan, ji take mutuwa zata yi zufa kawai ke karyo mata ko ta ina sunan Allah kadai take iya ambato, a haka Dr da Aneesa suka sameta da sauri Aneesa ta matsa tana yi mata sannu wannan shi ne karon farko da Aneesa ta ji tausayin Ameesha. Da sauri Dr ya kwaso kayan aiki nan ya shiga bata taimako yana yi yana addu'a, aiko cikin nasara sai ga kan jaririya ya fita. "Alhamdulillah! Suka faɗa kusan a tare.

Murna wajen Dr ba a magana da kansa ya gyara yarinyar da uwarta, Aneesa kuma ta gyara wajen tsaf babu mai cewa a wajen aka haihu, sai tashin kamshi wajen ke yi. Shayi mai kauri Dr ya haɗa mata sannan ya yi mata allurai, Aneesa kam na rungume da babyn wani irin soyayyar babyn na shigarta har sai ta ji bata kaunar a raba su.

Sai da Ameesha ta huta sannan ta yi wanka, bayan ta fito ta shirya kai ka ce ba ita ce ta haihu ba don yadda ta yi kyau abinta, Aneesa matsawa ta yi kusa da ita tana faɗin"Ameesha amshi yarki ta ji duminki ki ji nata ta haka ne zata taso da soyayyar ki tare da tausayinki.

Murmushi Ameesha ta yi ta ce "Dama babban burina in haifi mace, ya kasance ke ce mace ta farko da zata fara rungumarta kuma Allah ya amshi addu'ata domin ke ce uwarta Aneesa har gaban abada bana son yarinyar nan tasan ni ce na haifeta." Ta gama maganar daidai da shigowar Dr daga shi har Aneesa mutuwar tsaye suka yi da jin kalaman Ameesha, Aneesa kasa motsi ta yi sai Dr ne ya yi karfin halin cewa "ke kina da hankali kuwa yarinyar tawa za ki yi min kyauta da ita dawa kuka yi shawara to wallahi ba ki is..."

To fa! Yau fa ake yinta. Ga Ameesha daga haihuwa ta yi kyauta da yarinya shi kuma Dr Asmad ya ce bai san wannan ba, ya kuke ganin zata kaya? Ku bi Yar Mutan Rano a hankali don ta warware maku, a yi hakuri kaɗan ya rage in sha Allah. I hearttttt You fisibilillahi😘

*YAR MUTAN RANO*
*SANGARTA*

©
_*ZULAYHEART RANO*_

*SADAUKARWA*
*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

_*Wow Masha Allah hakika na ji dadin comment ɗin ku, hakika ya sanya Ni nishaɗi ku ci gaba da ina son comment dinku hakan ya nuna min kuna bibiyar labarin sosai, masu korafin cewa Ameesha ta yi wauta da ta yi wa Aneesa kyautar 'yarta ku sa ni cewa ba wauta Ameesha ta yi ba, domin rama Alhairi ga mai sharri ba illah ne ba, ko ni zan iya fiye da abin da ta aikata.*_
*49*
"Yau kuma sangartar ne da wauta ya fado kanmu ni da ɗiyata?" Turo baki Ameesha ta yi ta ce "Babu wani wauta ni dai wannan maganar har cikin zuciyata na yi ta ko bayan babu raina Aneesa zata riki 'yar na..." Saurin rufe mata baki Dr ya yi cikin sauri ya ce " ki bar yi min wannan mummunar fatan in sha Allah babu maganar mutuwa yanzu sai kin haifa min 'ya'ya goma sha biyar." Zaro ido ta yi ta ce "Sha biyar? Tab sannu baby ai mutuwa ta Allah ce idan lokaci ya yi babu makawa." Kasa furta komai ya yi sai kallonta yana matukar mamakin maganar ta.

Wani kallo ta aika masa da shi wanda ya sanya jikinsa mutuwa murus, shi sai yaga kamar ba Ameeshar sa ba, duk lokacin da suka hada ido sai yaga murmushi ne kwance a fuskar ta wanda ya kara fito da zallar kyaunta, "Cutie kin yi kyau da shayarwa fa." Ya yi sauri kawar da wan can maganar."Babu wani kyau ni kuma zafi nake ji baby." "Kwantar da hankalinki ki saba tukun, idan na fita zan shigo maki da magunguna wanda za su rage maki zafin." "Tom kafin na saba da aiki, ka fadawa Nenne kuwa?"

"Eh! Har da su Ummi sai dai na manta ban fadawa Meena ba." "Ok bari na kira ta har da k'awata Ni'eema Allah yasa tana gari." Ta ida maganar tana lalubo wayar. Amsan babyn ya yi a hannunta, tare da zuba mata ido "Cutie Wai yarinyar nan da wa take kama?" "Yo Ina zan iya bambance wa kasan jarirai rikida ne da su, amma kamar tana kama da Autar Ummi." Ta karasa maganar cikin sigar tsokana. "A'a da Autan Nenne ta ke kama Malama." Dariya suka sake gaba daya kafin su yi wata maganar Aneesa ta yi sallama, hannunta rike da plet na farfesun kayan ciki. "Ki fara cin wannan kafin na yi maki girki." Amsa Ameesha ta yi tana faɗin"Na gode." Idonta akan Aneesa don gani ta yi kamar ta yi kuka. Sai dai bata yi magana ba ta soma shan farfesun suna dan taɓa hira. Kwantar da jaririyar Dr ya yi ya fita.

"Wai Yar'uwa kuka ki ka yi ko?" Ameesha ta yi tambayar tana ci gaba da shan farfesun ta. "A'a ban yi kuka ba mai kika gani?" "No! Ban ga komai ba, amma yana da kyau komai a rika fawwalawa Allah shi zai kawo karshen damuwa." "In sha Allah ina godiya." Tabbas Ameesha ta yi gaskiya domin ba karamin kuka Aneesa ta yi ba, nadama sosai ya shige t da yanzu ita Dr ya fara yi wa hidima, tana ji Dr har kyautar sabuwar mota ya yi wa Ameesha dalilin haihuwa, lallai ta cutar da kanta. Cikin hiransu sosai Aneesa ta fahimci wasu daga cikin halayyar Ameesha kuma ta tabbata mutum ce ita mai sanyin hali da cikakken imani, tana yi wa 'yarta fatan ta dauki halinta na karamci. Mik'ewa ta yi tana faɗin kin ga "bari na je na dafa maki abu mai dan nauyi yadda baby zata samu ta koshi. Tana mik'ewa Meena tana yin sallama, sai da suka gaisa kafin ta fita.

Fitar ta babu jimawa Dr ne ya shigo hannunsa dauke da ledoji irin ta pamarcy Ameesha ya mik'awa yana faɗa mata yadda zata yi amfani da shi, sannan ya amshi yariyar a hannun Meena har tana tsokanarsa "Oh! Yau ga ɗiyar sangartacciya Ameesha a hannun Dr! Dariya ya yi ya ce "Meena kar ki ta do min baya yanzu dai ita kanta ta shaida ta girma sangarta sai a barwa yara. Harara kawai Ameesha ke aika masu, Meena fita ta yi ta bar Dr dauke da 'yarsa yana mata addu'a bayan ya gama ya dubeta tare da ya ce "Cutie kin ga kyautar da Allah ya yi mana wanda babu mai iya bamu sai Ubangiji sai mu godewa Allah." "Alhamdulillah! Ta furta cikin sanyin murya. "Yanzu wani suna kike son a sanya mata?" "Bani da zaɓi bari Aneesa ta shigo." "Ok." Ya amsa yana ci gaba da kallon yarsa. Cikin kananun lokaci har ta kammala girkin da taimakon Meena cikin babban tire suka shiryo.

Da sallama ta shiga dakin ta aje tana faɗin "Hamman Baban baby Sannu da hutawa, Yar'uwa sannu." Yawwa suka amsa a tare, zuba mata abincin ta yi ta mikawa Ameesha. Dr ya dubi Aneesa cikin kulawa ya ce "Uwar 'ya wane suna za a sanyawa ɗiyar taki?" "A'a tambayi Yar'uwa duk wanda ta zaba ya yi min." "A'a zaɓa dai Yar'uwa na baki dama." "Tom ina godiya da wannan dama a sanya mata sunan Nennena." Dariya Dr ya yi ya ce "Babban BURINA kenan to Allah ya raya mana FATIMA BINTA." Take ya yi mata huduba ya kalli Aneesa yana faɗin.

"To kuma ya lakabin ta?" "*(Miemie)*." Zamu rika ce mata. Ameesha dai tana gefe sai murmushi take dokawa, yau abin masha Allah daɗi yake mata tana fatan Allah ya dauwamar da su cikin farin ciki mai dorewa. Babu jimawa Nenne suka iso kamar haɗin baki su Ummi ma suka zo, gida ya cika da murna babu kamar Nenne da ta samu takwara.

Haka suka ci gaba da zama kullum gidan cike da masu zuwa barka, har ranar suna ya zagayo inda aka yi gagarumin taro wanda ya amsa sunan sa, an ci an sha an yi komai cikin kwanciyar hankali, su Nenne sun taka muhimmiyar rawa haka ma Hafiz da yan gidan su sun yi hidima sosai wa Ameesha da yarta.

Bangaren gidan su Ameesha ma sosai aka yi hidima. Ba a bar Aneesa a baya ba ta yi bajinta sosai wanda ya ba wa kowa mamaki ciki har da Dr, domin akwati guda ta yi ma Ameesha da diyarta. Haka dai taro ya tashi lafiya Ameesha ta ci gaba da kula da Miemie yarinya mai kama da ubanta sak, idan kaga Miemie a wajen Ameesha to abinci aka kawota ta ci amma wajen Aneesa take wuni komai ita ke mata, zaman su abin burgewa da sha'awa. Yanzu watan Miemie biyu ta yi wayau sosai abinta gwanin sha'awa gata tubarkallah.
Chapter 50 · 0% Book details