← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 54

Sashe 20

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baby baka bare min maganin ba kuma baka kawo min ruwa ba." A shagwaɓe ta gama maganar, da muryar ciwo. Dan tsaki Dr ya ja zuciyarsa cike da haushinta ya ce "sai na kawo maki ruwa za ki sha maganin? Ashe kam yau ba za ki sha ba." Yana gama faɗin haka ya yi shigewarsa bedroom. Kan Ameesha ya daure da maganar da Dr "me haka ke nufi?" Tambayar da ta yiwa kanta kenan hankali tashe, sai ma ta ji ciwon kan ya ware, jiki a sanyaye ta nufi dakin sa tana faɗin "baby wai yau ba zaka min wanka bane tunda ka ki bani ruwan na maganin to na fasa sha." Tana maganar hawaye suna barazanar zubowa.

Mtsww Dr ya ja tsakin da ya yi sanadin daukewar numfashin Ameesha na sakonni, sai kuma ta tsinkayo muryarsa yana magana cikin muryar da bata taba sanin Dr na da irin ta ba "Ke bana son damuwa, ki barni na huta kina neman takurani fa Ameesha je ki waje bana buk'atar ki kusa dani." A zafafe ya ke maganar. "Ameesha." Ta maimaita yadda Dr ya kira sunan ta kai tsaye, saurin toshe kunne ta yi tana ambaton sunan Allah a fili. Wasu hawaye suna zubowa daga idonta jikinta ya yi sanyi kalau take ciwon kan ya dawo sabo, da kyar ta bude baki ta ce

"Baby me kake nufi da maganar da na ji, shin ba kunnena suka ji.." hannun da ya daga mata yasa ta yi shiru da sauri. "Za ki fita ko ni na bar maki daki?" Tambayar ya yi yana daukan wayarsa. Kallonsa ta yi sai ta ga kamar ba Dr Asmad da ta sani ba ne wannan don shi ko da yaushe fuskarsa ɗauke da murmushi yake, saɓanin wannan da ya wani murtuke kamar wanda baisa wani abu dariya ba, da sauri ta fita tana kara fashewa da kuka.

Dr na ganin ta fita ya furzar da wani iska mai zafi, zuciyarsa cike da takaicin matan nasa yanzu duk so da tattalin da yake wa Ameesha da wannan zata saka masa, shi ko me yake wa matansa da suka zaɓi su musguna masa ta hanya mafi muni, Aneesa ta zubar masa da ciki bata tsaya iya nan ba ta ci gaba da shan magungunan hana daukar ciki, sam bai damu ba shi ne itama Ameesha zata bullo da haka me ya yi masu da zafi da basu kaunar hada jini da shi? Wannan tambayar shi ya ci gaba da yiwa kan sa sai dai ya rasa amsansu.

Ameesha kuwa tana shiga bedroom din ta kuka ta ci gaba da yi, duk iya tunanin ta ta kasa tuna laifin da ta aikatawa Dr mafi muni da har ya jefa ta cikin wannan mawuyacin halin, kwana ta yi idonta na hawaye sam bata rintsa ba yadda taga dare haka ta ga rana, shi ma bangaren Dr da kyar wani wahalallen bacci ya kashe shi ko da asbah sallah kawai ya yi ya koma baccinsa.

Ameesha tana idar da sallah ta shiga kicin ta fara shiryawa Dr abin break tana yi tana hawaye a haka ta kammala, sannan ta gyara kicin ɗin da falo, kafin ta yi wanka sai da ta gyara bedroom ɗinta ta turareshi da turare, wanka ta shiga bayan ta cika ruwan wankan da turaruka masu sanyin kamshi, bata wani jima ba ta fito simple dressing ta yi top da wani three kwantan wado ta sanya ta raba gashinta gida biyu da reboom kalar rigar ta, jikinta sai kamshi yake fitarwa kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin damuwa musamman yadda idanuwanta suka kumbura sosai. Jiki a mace ta nufi dakin Dr.

Ta kai hannu da niyyar buɗewa sai ta ga an buɗe kofar, baya ta ja tana faɗin "Barka da safiya." Bai amsa ba sai ma hanyar wucewa da ya lalubo, ganin da gaske zai wuce sai ta yi saurin riko hannunsa tana faɗin "mai na yi maka baby kake fushi da ni tun jiya ga shi kuma yanzu gaisuwata ma kaki amsawa?" Zame hannunsa ya yi daga rikon ba tare da ya furta komai ba. Wasu sabbin hawaye suka zubo daga idonta murya na rawa ta ce

"Na kammala break please ka tsaya ka yi." Sai yanzu ya yi magana shi ma a takaice ya ce "bana buk'ata." Daga haka ya yi wucewar sa, inda ya bar Ameesha zaune cikin kuka ta kasa ko da tashi a inda take, duk iya tunanin ta bata gano laifin da tawa Dr ba, haka dai ta kasance cikin hawaye har bayan la'asar da kyar ta iya yin break shi ma sai da ta ji tana shirin hallaka kanta, tana zuba idon ganin Dr amma sai ta ji shiru, duk da tasan yau ba ita keda shi ba amma ya saba zuwa ya yi mata sallama yau kam shiru har bayan magriba.

Sabon kuka ta fashe da shi tana tir da halinta tunda ta kasance mai sabawa mijinta har ya dau fushi da ita mai tsanani, sam ta manta da wai ana cin abinci don rabonta da shi tun na safe ta nemi yunwar ta rasa, alwala ta dauro tazo ta zube gaban Ubangijinta ta ci gaba da kai kukanta bata gushe ba har sai da ta yi sallar asuba sannan nannauyan bacci ya kwashe akan sallayar.

Duk da ya ji zafin abinda da yake ganin Ameesha ta ha'ince shi da shi, wani gefen na zuciyarsa tana jin haushin yadda Ameesha ta kasance daga dare zuwa safe, kukanta ya tsaya masa a rai sosai, har ya ji kamar ya je ya lallasheta sai dai ya zama dole ya nuna mata kurenta. Aneesa ma tunda taga Dr da ya dawo office yau bai je sallama da Ameesha kamar yadda ya saba ba sai ta yi tunanin kila ba'a gidan ta kwana ba, ci gaba ta yi da kulawa da Dr tana son ta bashi dukkan wani farin ciki. Sosai ya yi kokarin biye mata ko dan ya sauke hakkinta da ke kanshi, duk da hankali da tunanin sa suna ga Ameesha ba.

****
Najeeb ne keta kai komo tsakanin repretion da kofar dakin haihuwa, gefe guda kuma Mumynsa ce da alama Rufaida ce a dakin don yadda Najeeb ke zarya hankali a tashe. "Haba Najeeb ka kwantar da hankalinka insha Allahu lafiya zata sauka." Da taushin murya take masa kalaman.

"Na kwantar Mumy Allah ya sauketa lafiya." Amin Mumy ta amsa tana ci gaba da kwantar masa da hankali, minti talatin tsakani wata Nurse ta fito dauke da jaririya cikin towel mai laushi da kyau, mikawa Mumy ta yi tana faɗin "Hajiya ga baby girl nan Madam ta sauka." "Alhamdulillah!" Suka hada baki wajen fada, Najeeb kuɗi ya zaro ya mikawa Nurse din ya ce ga goron albishir nan. Amsa ta yi tana godiya Mumy ta cika da murnar samun jika yarinya kyakkyawa da ita, ko kunya Najeeb bai ji ba ya amshi yarsa yana kiss da addu'oi. Babu jimawa aka fito da Rufaida zuwa dakin hutu tunda lafiya ta haihu sai gajiya.

Cikin dakin bayan Mumy ta haɗa mata shayi mai zafi ta sha, sai Najeeb ya kuma rungumar yarsa ya bata zamzam da zuma kafin ya soma yi mata huduba, Mumy ta kalleshi ta ce "huduba kake mata?" "Eh Mumy na yi mata huduba da *Maryam*. _Littel Ameesha_." Murmushi Mumy ta yi ta ce "Allah ya raya Maryam cikin musulunci." Domin dai tasa irin son da Najeeb ke yiwa Ameesha.

Ita kanta Rufaida bata ji haushin sunan da ya sanya wa jaririyar ba, sai ma addu'a da take yiwa yarta, babu dadewa jama'a suka cika asibitin don taya su murna.

****

Wasa wasa dai har Dr ya fita dakin Aneesa bai saurari Ameesha ba, yau take sa ran zata karbi Dr kuma ta yi alkawarin sai ta daidaita tsakanin ta da Dr kuma sai tasan laifin da ta yi masa domin a kwanaki biyun nan ita kadai tasan a hankali da ta yi su. Mikewarta kenan daga kujera zata nufi kicin domin uku da kwata ta yi sai ta ji ana buga kofarta, da mamaki ta isa kofar tana faɗin "waye?" Muryar da ta ji ya sanya ta buɗewa tana kallonta baki bude. Aneesa kam wani kallo ta watsawa Ameesha tare da jan siririyar tsaki ta ce "Hamman ne ya ce in kawo maki wannan lemon ki sanya masa a firij don ke kike da shi." Har ba za ta amsa ba, domin bata taɓa ganin haka ba sai kuma ta Murmushi wanda ya tsaya iya labba tasa hannu ta amsa tare da shigewa ciki.
[10/8, 8:18 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
_*ZULAYHEART RANO*_

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*45*

A firij din kicin ta sanya sannan ta fara aikinta hankali kwance, tafashen nama ta ɗaura baya ta wanke, yana fara taushi ta sauke sannan ta haɗa masa kayan hadi lokacin an shiga sallar la'asar don haka ita ɗin ma bedroom ta shiga ta gabatar da sallar, bayan ta idar ta koma ta ci gaba da aikinta, dambun shinkafa ta yi masa sai farfesun naman rago da sansanyan abin sha. Karfe biyar saura ta kammala aikin ta jera komai akan dining bayan ta gyara kicin ta wanke duk kayan da ta yi amfani da shi.

Falo ta koma ta kara gyara duk inda ya kamata ta turare shi da turaruka masu kamshi da daɗi gaba daya gidan ya cika da kamshin abincin tare da na turare, cikin sauri ta faɗa toilet don ganin lokacin shigowar Dr ya kusa, wanka ta yo ta mulke jikinta da mayuka masu kamshi cikin wata riga ta shirya wanda iyakar sa cinya, santala santalan cinyoyinta duk sun bayyana sosai ta yi kyau duk da ba wani make up ta yi a fuska ba. A falo ta zauna tare da daura kafa daya kan daya tana canza tashoshin t.v. kamar a mafarki ta soma jiyo fitinan nan kamshin turaren Dr wanda ya yi sanadin da ta lumshe ido wani irin feeling ya saukar mata, tana jiyo takunshi ta yi saurin tashi tare da nufa kofar.
Chapter 20 · 0% Book details