Sashe 46
Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kafin ya yi yunkurin bata amsa ne suka ji maganar a bayansu. Da sauri Ummi ta juya tana kallon Alhaji Abubakar ɗin.
"Alhaji ka ji abin da ya ce kuwa?"
"Sosai na ji, koba ce wa ya yi zai kara aure ba?"
"Eh! Haka ya ce."
"To na bashi goyan baya Allah ya tabbatar da Alhairi, yar wacece?"
"Alhaji ka ce kana goyon bayan shi fa, duka duka yaushe ya yi auren?"
"Look! Hajiya ya kamata ki fahimci halin da yaron nan ya ke ciki."
Shiru Nenne ta yi, don ta san duk wani bayanin da zatawa Bobbo ba fahimta zai yi ba, amma sam bata son Asmad ya kuma aure a yanzu. Muryar Bobbo ta ji yana kuma tambayarsa yar wacece?
"Bobbo ina sonta sosai amma kuma yanzu da na je gurin mahaifinta ya ce ya mata miji, Bobbo wallahi idan na rasata zan shiga wani hali." Cikin karaya ya ida maganar.
"Kar ka sa damuwa a zuciyarka, ka yadda samu da rashi duk na Allah ne, kuma in har matar ka ce sai ka aureta, ina son farin cikin ka kamar yadda kake son na mu."
Wani daɗi ne ya rufe shi, duk da dai yasan Ameesha ta yi masa nisa, sai dai zai ci gaba da addu'a kamar yadda Bobbo ya bukata.
A haka Bobbo ya yi ta kwantar masa da hankali, sannan ya yi sallama da su ya ta fi zuciyarsa wasai.
*GIDAN ALHAJI MANSUR*
Mommy da Najeeb suna ta shirye shiryen aure, kuɗi sosai Mummy take kashewa Wajen haɗawa Ameesha kaya, kamar kullum yau ma zaune suke suna lissafin abin da basu saya ba.
"Kasan menene Najeeb?" Mummy ta tambaya.
"A'a" Mummy ya bata amsa.
"Yawwa so nake a kammala duka kayan kafin satin sama, don satin da zamu shiga lokaci ya kure."
"Eh! Mummy hakan yana da kyau, dama gidan an gama komai sai saukar Alkur'ani da nake so a yi."
"Madallah! Allah ya tabbatar da Alhairi."
Alhaji Mansur ne ya shigo falon, fuska sake kamar wanda aka wa bushara da aljanna, zama ya yi akan kujera tare da kallon Mummy ya ce
"Kuna nan sai shawara ku ke yi da ɗanki, kun wareni a gefe!"
"Abba ina wuni?" Najeeb ya yi maganar yana tsugunawa.
Sosai ya saki fuska yayin amsawa.
A jiyar zuciya Mummy ta sauke don jin yau Alhajin da yan mutunci aka shigo ta ce
"Haba Alhaji kana ranmu fa!
"Haka dai kika ce, maganar mai kuke tattaunawa?"
"Maganar yadda auren Najeeb zai kasance mu ke yi."
Ta ba shi amsa cike da jimamin yadda zai dauki maganar.
Wani irin zabura Alhaji Mansur ya yi ya ce...
*A dai kara hakuri da ni Please, Zulayheart Rano tana tsananin kaunar ku gaba ɗaya.*
_*YAR MUTAN RANO*_
*SANGARTA*
©
_*ZULAYHEART RANO*_
*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*
```Wannan shafin na ku ne ku kadai yan jahata babban birnin Nijeriya wato RANO a duk inda kuke ina alfahari da ku ina jin duk wani dan Rano jinina ne, Allah ya barmu da kaunar juna```
_*Happy birthday Ramlat Ar Manga wish you many many year's in your life*_😍😍😘
*46*
Tunanin inda zata nufa take, sam bata jin zata iya komawa gidansu tasan sarai halin Abba tunda Asmad ya shiga rayuwar ta ya rage sake mata sai Asmad ɗin, yanzu idan ta tunkare shi tabbas tasan ba zata taɓa samun mafaka ba, kila ma a daren nan ya dawo da ita hukuncin Ya Jaheed ma yafi daga mata hankali babu makawa Ummi fushi zata yi da ita, hannu tasa a ka ta fashe da wani kuka a fili ta furta "oh! Ni Maryerm ina zan nufa?" Take wata zuciyar ta bata amsa gidan Nenne. Bata tsaya komai ba ta yi na'am da shawarar zuciyarta domin shi ne mafita, da kyar ta kai kanta bakin titi domin cikin layin babu wani masu abin hawa, ta dade sosai kafin ta iya taran dan keke napep, duk da ko kwabo babu a hannunta haka ta shiga ko ciniki ba su yi ba, domin yadda kanta ke mugun sarawa bata jin zata iya magana. Tafiyar mintina ta kaisu gidan "ka yi hakuri bari a kawo maka kuɗi." Ta yi maganar da kyar tana nufa get din.
Kwankwasawa ta yi cikin rashin kuzari, maigadin ya fito cikin sauri ganin Ameesha ya yi saurin tsugunawa yana gaidata, bata iya amsawa ba sai ce masa ta yi "ya amso dari biyar a cikin gida ya bama mai napep ɗin." Cikin kankanin lokaci ya isa cikin gidan sallama ya yi a kofar falon Nenne da Bobbo ne zaune suna hira, kafin Nenne ta amsa har Bobbo ya amsa bayan sun gaisa ya ce "Hajiya dama matar Alhaji karami ne ta ce a amshi dari biyar a kai wa dan adaidaita." Bobbo ya ɗauki dari biyar din ya mika masa ya yin da Nenne ta cika da mamakin wai matar Asmad ce ta zo kuma ta sanya a amshi kuɗin napep, ko kafin ta gama mamakin sai jin sallamar Ameesha ta yi cikin wahalalliyar murya, da sauri ta isa gareta ganin tana niyyar faduwa kasa.
"Subhanallah! Ameesha ke ce da daren nan ina Asmad ɗin?" A kidime Nenne ta jero mata tambayar. "Nenne zan sha ruwa." Ta furta da kyar." Bobbo ne ya mikawa Nenne goran ruwan Faro da ya siyaya ɗazun, ɓalle murfin ta yi ta shiga bata ruwan har sai da ta shanye kafin ta saki goran tare da ajiyar zuciya. "Maryam sannu dama baki da lafiya ne?" "Eh!" Ta bata amsa. "Kuma dan rashin hankali irin na Asmad sai ya barki kika fito a wannan yanayin?" A fadace Bobbo ya yi maganar. Ganin jikin nata ya fara zafi sai Nenne ta ce "Alhaji ko zaka kira Asmad ba ne? Don jikinta kara zafi yake." Zazzafan zazzaɓi ne ya rufeta, cikin muryar da bata fita ta ce "a'a Bobbo karka kira shi ba sai ya duba ni ba, idan akwai pracitamol a bani." "Ki dai bari a kira shi don kina da buk'atar taimako." Nenne ta yi saurin katse ta.
Kuka ta sanya tana faɗin kar a kira shi, take Bobbo ya fasa tare da tsare Ameesha da ido "Anya kuwa lafiya Maryerm?" Kanta a kasa ta ce "lafiya lau Bobbo, bana jin dadi ne na fito kuma bai san ina rashin lafiyar ba." "Kan ji shashanci kuma shi ne kika fito baki tunanin zai iya shiga wani halin idan?" "A yi hakuri Bobbo da safe a kira shi." Ganin kamar ba cikin nutsuwa take ba yasa Bobbo amincewa. da taimakon Nenne suka shiga ciki, ruwan wanka Nenne ta haɗa mata sai da ta taimaka mata wajen shiga toilet din kafin ta bata waje.
Bata jima ba ta fito ko tsayawa sanya kaya bata yi ba ta kwanta, gaba daya jikinta ya kuma gashewa da dumi, bargo ta ja ta rufe jikinta hakoranta sai haduwa suke da juna, a haka Nenne ta shigo ta sameta "Tashi ki sha tea sai ki sha magani." Kaɗan ta kurba ta watsa maganin kafin ta koma ta kwanta.
A haka suka kwana Ameesha bata jin dadi, zazzaɓin ya sauka sai ciwon da gaɓoɓinta ke yi, sam Nenne bata rintsa ba domin tausayin halin da Ameesha ke ciki, tabbas tasan ba lafiya ya kawo ta gidan cikin daren ba, amma duk tambayar da ta yi mata amsa daya take bata shi ne "Babu komai." Ta ta gaji da tambayar sai ta yi shiru, ta kudiri a zuciyarta in har Dr wani abu ya yiwa Ameesha tazo gidan zai ga ɓacin rai ganin idonsa.
****
Tun bayan tafiyar Ameesha Dr ya kasa samun nutsuwa sai zarya yake a dakin shi kaɗai, tsaki ya yi shi har bai san yawan su ba, daga karshe komawa toilet ya yi ya sakarwa kansa ruwa ko zai samu sauki a zuciyarsa. Bayan ya fita kayan bacci ya sanya ya kwanta sai juyi yake zuciyarsa tana tuno masa yadda Ameesha ke kuka tana rokonsa, mtsww ya ja tsaki tare da juyawa da kyar bacci ɓarawo ya samu nasarar ɗaukan shi, kallo ɗaya zaka masa kasan baya cikin nutsuwarsa.
"Hmmmm! Rukky wallahi bazan ɓoye maki ba ina cikin damuwa." Aneesa ce ke maganar cikin waya bayan ta kule a bedroom ɗinta. Daga ɗaya bangaren Rukky ta ce "kina da matsala Aneesa, yanzu baki ga canji ba ne da kika kai maganin? Ko dai baki sanya inda zai gansa ba?" Mtsww Aneesa ta saki tsaki ta ce "Ni Ko na sanya inda zai gani domin na farko sai da suka yi kwana huɗu basa magana, da kyar ta samu suka daidaita yau kuma abin ya kara gaba ina jin koranta ya yi don naga ta fita." Hehehe! Rukky ta saki dariyar keta, ta ce "Kina wuta Anee, kinga yanzu saura kiris Dr ya zama naki ke kaɗai, idan kin dage gaba kadan komai zai daidaita." Cike da murna ta kammala maganar. Hmmmm! Kawai ta iya faɗa suka yi sallama, tana aje wayar ta buga uban tagumi, a yanzu sam hankalin ya kasa kwanciya.
Washegari da safe sai da ya yi wanka, ruwan zafi kawai ya ɗaura tea ya haɗa bayan ya gama sha ya yi shirin zuwa office, sama sama suka gaisa da Aneesa ya tambayi ko da matsala, ta tabbatar masa babu sannan ya wuce domin akwai masu jiran sa a office din.
*Bangaren Ameesha*
Kamar ciwon na jiran Bobbo ya fita ya dawo sabo, dalilin break ɗin da Nenne ta kawo mata, tunda ta ci hankalinta ya kasa kwanciya sai yunkuri take amma aman yaki fitowa, haka ta wuni aikin abu daya da Nenne ta yi mata maganar Asmad sai ta kuma fashewa da kuka, shi yasa ta zuba mata ido.