← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 54

Sashe 28

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaro ido ya yi yace "Me Hajiya take nufi da wannan kalmar? Tana nufin ke ba shiryayya bace?" a zafafe yake maganar.

"To Nima fa Abba abin da ya ban haushi kenan, ita Ummi kullum bata son taga ina farin ciki, sai tayi dalilin sani cikin damuwa"

Ameesha tayi maganar tana cigaba da matsar kwalla. "Yi hakuri yar Abba tashi kije zan sami Hajiyar yanzu, sai ta fada min dalilin ce maki hakan, oya je ki wanke fuskarki"

Ummi ce ta fito daga bedroom dinta, ganin Ameesha na kuka yasa ta mamaki tace "ke lafiyar ki kuwa?"

"Wani irin tambaya ce haka Hajiya, kefa kika sa Yarinyar nan kuka, amma yanzu kina tambayar ta" cikin fad'a ya kara sa maganar.

Dan murmushi Ummi tayi tace "Haba Alhaji ka daina saurin daukar fushi a kan lamarin Ameesha, in banda kaima kana biye mata, har yaushe zata ce na sata kuka ka yadda? Ko da yake tunda *Sangarta* na damunta, dole tayi kuka don nace Allah ya shirya min ita"

"Yawwa kinji ba, me kalmar Allah ya shirya ta yake nufi?Gaskiya ni ban son haka, duk mai son zaman lafiya to karya tab'a min uwata."ya yi maganar cikin fushi.

Jinjina kai Ummi tayi tace"Allah ya baka hakuri Alhaji, amma maganar neman shirin Ameesha wajen Allah yanzu na fara fada" tana gama fadi haka ta yi kicin.

"'Yar Abba tashi kije ki wanke fuskarki, sai kizo ki tafi ko?"

"Nifa Abba kamar na fasa zuwa"

Ameesha tayi maganar tana cigaba da latsa wayar ta. Don dama duk maganar da Abbanta da Umminta suke tana jin su, ko kallon su bata yi ba har suka gama.

"Haba yar'lele mai zaisa ki fasa, tashi maza kije ko kina son na kaiki da kaina ne?"

"A'a Abba da kaina zanje."

"Ok wane motar zaki fita da shi?"

"Abba sabuwar motar ka zan hau yau, wannan wanda aka kawo last week, *Bugatti vogron* dinka" ta bashi amsa tana hawa down step.

Fada da fara'ar sa ya yi yace "To maza ki fito kizo ki dauko key, sai ki tafi yar Abbanta." ya karasa maganar yana girgiza kai.

Da sallama ya shigo falon tare da tsugunawa, ya soma gaida mahaifin nashi. Fuska sake ya amsa da "Lafiya Lau Jaheed ya ka tashi"

dukar da kai kasa ya yi yana amsawa. Hajiya Halima ce ta fito daga kicin fuska dauke da fara'a tace"Lallai Jaheed yau Kayi nannauyan bacci, har sha daya kafin ka fito?"

Dan murmushi ya yi yace "Wallahi Ummi jiya da zazzabi na Kwana yanzu ma da kyar na tashi"

"ayya Sannu Allah ya kawo sauki, tashi kayi break sai kasha magani, shi yasa banga ka fito da wuri ba, gashi yau kuna da aiki." cikin tausayawa dan nata take maganar.

"Abba na dauko key din Sai na dawo." muryan Ameesha ya cika falon.

"OK yar Abba a dawo lafiya"

"Ke ina zaki yanzu a wannan lokacin har da daukan mota?"

Jaheed ya tambaya ransa a b'ace"Yaya saloon zanje fa daga nan zan biya nayi shopping"

cikin shagwaba ta yi maganar. Harara Alhaji Tahir ya zabga masa yace"Kai nikam ban son fi'ili ina ruwan ka da inda zata je, kawai ka sawa Yarinya ido sai faman tambayar ta kakeyi"

"Yi hakuri Abba bada wani manufa nayi Mata tambayar ba."

"Kudai kuka sani kuma, amma uwata da shen Allah ne."

Ummi ta jinjina kai cikin ranta tace"Lallai lamarin Alhaji kara gaba yake"

Ameesha ta matsa inda Abban ta yake ta manna masa kiss a kumatu tace"Abbana ina sonka sosai, sai na dawo."

murmushi ya saki yace "A dawo lafiya uwata Allah ya tsare, ki rika kula don kin San akwai Wanda suka sa maki ido."

"Insha Allah Abba." ta yi maganar tana fita daga falon.

Mamaki sosai ya rufe Ummi, da irin maganar Alhaji Tahir din, jaheed ya bude baki zayyi magana suka hada ido da Ummi, yana ganin kallon da Ummin tayi masa ya gane nufinta, don haka sai ya yi shiru. Ameesha kam tayi tafiyar ta.

*ASALIN LABARIN*

AMEESHA diya ce wajen Alhaji Tahir da Hajiya Halima,Yarinya ce yar gata wajen mahaifinta, Alhaji Tahir haifaffan garin kano ne, cikin karamar hukumar bicci, yana da matar aure d'aya da ya'yan sa biyar,Hajiya Halima itace matar sa, Kuma ita ce ta haifa masa duk ya'yan sa, suna zaune cikin garin kano a unguwar Tudun Yola dan kasuwa ne babba Allah ya bashi tarin dukiya. Don yana da manya manya shaguna a kantin Kwari da singa duk dake garin kano,Babban dansa shine Muh'd Mujahideen, wanda suke kira Jaheed, sai AbdulMalik, Umar Faruk, sai Aliyu Haidar, sai Auta Maryam Wacce suke kira Ameesha, Allah ya daurawa Alhaji Tahir son Ameesha, yana kaunar ta sosai don tace Sunan mahaifiyar sa, Kuma ta kasance ita daya ce ya mace da Allah ya azurta shi da ita, Baya kaunar bacin ranta, lokacin da take karama duk rashin kunyar da tayi maka, baka isa ko kallon banza Kayi mata ba, balle akai ga maganar duka ko zagi, to a ranar ba zaman lafiya don an tab'a masa 'yar lelensa, haka yasha zuwa makarantar akan an daketa ya zabgawa malaman rashin Mutunci, Ameesha tun tana karama abin da tayi niyya shi takeyi, babu daman wani ya yi magana sai Alhaji Tahir ya soma, yana cewa an sawa yarsa ido, Koda kuwa Ummi ce da yayyin ta sukai magana Kan abin da take haka yake rufe ido ya yi ta ruwan masifa, *Sangarta* kala kala Ameesha keyi, babu mai magana. wannan Abu yana bawa Hajiya Halima haushi, sai dai bata da yadda zatayi da ya wuce Addu'a. Har zuwa lokacin da ta girman ta bata rage ko Abu daya daga Halayyar ta ba, sai ma rashin Mutuncin ta dake karuwa a kullu yaumin.

***

Fitowar ta kenan daga cikin Shahad store, inda tayo shopping din duk wani Abu da take so, idonta sanye da wani kwamemen glass, Kallo daya zaka yi mata kasan babu mutunci a tattare da ita. Musamman yadda take wani irin taku cikin isa da tak'ama. Hannu tasa tare da zame glass din idonta, tana kallon motar da aka faka kusa da ta ta motar. Jinjina kai ta yi tana mamakin wanda ya faka motar don ya tare mata hanyar fita, tsayawa ta yi jikin motar tana jiran ganin fitowar ko ma waye mai motar, don ta nuna masa ba'a mata haka, Yau zata nuna ma duk Wanda ya yi mata wannan aikin rashin Mutunci. Tafiya yake cikin nutsuwa, wayar sa makale a kunnen sa, da gani kasan waya yake yi, isa ya yi wajen motar sa tare da budewa, zai shiga ciki kenan maganarta ta hana shi shiga.

"Kai Malam me kake ji dashi da har zakayi min crossing din hanya, sannan kazo ka wuce ba tare da ka ban hakuri ba?"

Dago da kyakykyawan fuskar sa ya yi, ya sauke idon sa Kan fuskar ta, take ya ji wani yanayi ya shige sa wanda bai tab'a jin sa ba. Kallon beauty face din ta yake babu kakkautawa. Ran Ameesha ya baci matukar da irin kallon da yake mata, sannan ta yi magana bai amsa mata ba, don haka sai ta daga hannunta tare da kaiwa fuskarsa mari. Saurin gocewa ya yi bata same shiba, ransa ne ya baci har Shima bai San Sanda ya daga hannu tare da gwaura mata wani lafiyayyen mari. cikin sanyanyar murya yace" Ke dabba, mahaukaciyar ina ce da har zaki daga hannu da sunan marina?"

Bude ido ta yi cike da mamakin marin da ya mata, a iya saninta rabon da wani ya mareta tun tana primary 3, Shima malamin Sanadin dukan da ya mata ya bar koyarwa a school din, cikin sauri ta zaro wayar ta tare da dailing number din Abbanta cikin kuka ta soma zayyane masa abin da ya faru...... "

*_Yar mutan rano_*
[10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*3*

"Wa ye shi a Nigeria da har zai daga hannu ya mareki?"

Alhaji Taheer ya yi tambayar a zafafe.
Hawaye suka kuma zubo wa a idon Ameesha, don ba karamin shigar ta marin ya yi ba. Murya a sanyaye tace

"Abba badan ko wa bane hasalima wani kaskantaccen mutum ne, wanda ba shi da ko sisi, motar da yake hawa ko kyauta aka bani bazan iya hawanta ba."

"Maza dauko min number din motarsa, zanyi maganin kowaye."

Dago kan da Ameesha ta yi sai taga wayam babu motar mutumin, wani karin takaici ya rufeta, a zafafe tace

"Abba ya wuce ban san ma lokacin da ya wuce ba."

"Maza ki dawo gida, ko nazo na dauke ki ne? "

" No Abba ba sai kazo ba yanzu zan taho."
Ameesha ta yi maganar tana shiga motar, a ranta ta kudurta bata kuma zuwa *Sahad store* ba domin wajen ya zama mata wajen jin kunya.

Cikin gida kuwa Abba sai kai komo yake, yana ta jan tsaki, don hankalin sa ya tashi da jin maganar marin Ameesha, Hajiya Halima ta fito daga kicin tare da kallon mai gidan nata, cikin kulawa tace

"Alhaji lafiya kuwa?"

Tsaki yaja tare da hararan Hajiyar yace

"Yo ina fa lafiya, an samu wani dan iskan ya maran min yarinya a banza."

Mamaki ya kama Hajiyar tace

"Alhaji mari Ameesha aka mara kowa? "

" Inada wata 'yar ce bayan Uwata? Ya cigaba kinga Hajiya karki kuma 'bata min rai, dama fa na kula tun farko baki so fitan yarinyar nan ba, don haka burin ki ya cika tunda an wulakanta min ita a waje."

Girgiza kai Ummi ta yi tace

"Amma Alhaji kana bani mamaki, in ka fad'i wata maganar, ta ya zakace wai ina son a wulakanta Ameesha?kar fa ka mata ni na haifeta, kuma banki ace Ameesha tafi ko wace ya mace nutsuwa ba, na tabbata Ameesha rashin kunya ta yi wa duk wanda ya mareta, amma kai ba ka yi bincike ba, sai ka yanke hukunci ka daura laifi akan mutum, gaskiya haka ba kyau.

Daga mata hannu ya yi alamar ta yi masa shiru, dai dai da shigowar Ameesha, jikin Abba ta fad'a tare da sakin wani sabon kukan.
Chapter 28 · 0% Book details