Sashe 51
Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai fa Allah ya yi Miemie da shegen rigima, kullum kuka har asbiti suka je aka tabbatar lafiyar ta lau, sosai kukanta haushi yake ba Ameesha, Aneesa kaɗai ke iya lallashinta.
****
Kaiwa kawai yake yana komowa a cikin katafaren falonsa , hannunsa rike da waya yana kiran amininsa Alhaji Mamman "Hello ina jiran ka cikin gidana dake bayan gari." Daga haka ya katse wayar yana jero tsaki marasa adadi, ban abin da yake so a yanzu sai dai ya samu mafita domin kullum tsanar Alhaji Taheer gaba yake a zuciyarsa. Ba a jima ba Alhaji Mamman ya iso, gaisawa suka yi ya bashi ruwa don tsabar tashin hankali kasa ce masa komai ya yi sai girgiza kai da yake irin dai yana cikin muguwar damuwa Alhaji Mamman ya muskuta tare da cewa
"Wai Alhaji Mansur ya maganar ka da Alhaji Taheer ne?" A jiyar zuciya ya sauke mai karfi kafin ya yi karfin halin cewa"Yo wane amsa zan baka ai Ni kam Taheer ya zame min ciwon ido na rasa ya zan yi da shi, wannan shashashan da matarsa ta haihu ko shawara dani baiyi ba ta sanyawa 'yarsa sunan mahaukaciyar yar Taheer wannan abu ya min ciwo amma akwai shirin da nake masu." " Gaskiya dai ka dage don kullum abin gaba yake kayan da ake shigo masa da shi har sun haura na da, ga yar tashi ma ta haihu ba kaga irin dukiyar da suka kashe ba."
"Kai dai zuba ido ka yi kallo kidnapped ɗinsa zan sa ayi, kila ko tanan ma samu rabonmu." "Wannan gaskiya ne, yin haka shi ya fi maka." Haka dai suka ci gaba da hira Alhaji Mansur yana ci gaba da bayyana munanan manufofin sa akan Alhaji Taheer.
Kwanci tashi babu wuya wajen Allah har Miemie ta yi shekara a duniya, yarinya mai shegen wayau tasan kowa na gidan, bata saba da Meesha da Dr ba kamar Aneesa komai Momma haka take faɗawa Aneesa, Ameesha kuma Mami Dr Kuma Daddy, tun tana da wata bakwai a duniya ta soma tafiya magana kuwa kamar wacce ta hadiyi rediyo, wani lokacin har mamakin wayanta suke yi. Meesha ce kwance idonta lumshe kamar mai bacci, Miemie ta kwaso da gudu ta faɗa kanta tana faɗin "Mami tashi." "Oh! Allah Miemie ke kam ba ki son na huta idan na tashi mai zan yi maki?" Aneesa dake zaune a falon ta saki dariya tana faɗin " ke kuwa Yar'uwa tashi mana ki ji me zata faɗa maki." Ta shi ta yi zaune hannunta dafe da goshinta, ta ce "wallahi kaina ciwo yake." "Ayya sannu." "Yawwa ina za ku je ne haka?" Da sauri Miemie ta ce cikin Hausar ta mara fita "gitan Nenne ta mu je." "Shi ne ko ku faɗa min na shirya?" "A'a yi zamanki wannan baccin da ya sarface ki a kwanakin nan bana jin zai barki zuwa unguwa." "Hmmmm! Ki dai bari Yar'uwa wallahi kamar mai cutar bacci haka nake jina, sam na rasa gane kaina ɗazun indomie zan dafa daga daura ruwan zafi kafin ya yi zafi na dawo falo wallahi bacci ya dauke ni, in da Allah ya rufa min asiri ruwan bai kai ga kone wa ba na farka." Murmushi Aneesa ta yi ta ce "Bari Hamman ya zo ya kamata ya duba ki wannan sleeping ɗin ba na lafiya ba ne."
Zaro ido ta yi ta ce "A'a nikam lau nake bacci ne kawai Allah ya kawo bari ma ki ga na tashi." "Za ki ga lafiya Yar'uwa mu dai Ni da babyna mun ce Allah ya inganta." Tana dire maganar ta suri Miemie suka fice, ya yin da suka bar Ameesha cikin mamaki. Bata bar mamaki ba har zuwan Dr bayan ya gama cin abinci ya fara tambayarta ko me ke damunta, a sanyaye ta ce "ɗazun Aneesa ta yi wata magana kamar nufin ta ciki ne dani." "To kuma shi ne abin damuwa?" "Haba beby ciki tun yanzu wallahi haihuwa da wahala duka yaushe na haifi Miemie?" "Kwantar da hankalin ki Cutie Yi addu'a Allah ya baki nagari, domin ciki ya tabbata a gareki har na wata biyu." Kara zare ido ta yi da jin maganar Dr ta ciki? Ai ni sam ban ji wani alamomi ba sai bacci kamar wata mai cuta." "Baccin shi ne alamar da ya kamata ki gane, nikam tun bai kai wata ba na fahimci ajiya ta don wannan karon ban yi sake ba." Fuska dauke da murmushi mai nuna zallar farin ciki da jin dadi Dr ya dire maganar.
Ameesha kam kasa cewa komai ta yi sai kallon Dr da take yi.
Mu je zuwa dai an zo final in sha Allah.
*YAR MUTAN RANO*
[10/27, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*
®
_*ZULAYHEART RANO*_
*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*
*50*
Haka ta wuni sukuku har su Aneesa suka dawo, a falo suka sameta kwance Miemie da sauri ta faɗa kanta tana faɗin "Mami min dawo." "Sannu da dawowa 'yar Momma ya Nenne?" "Lafiya lau tana gaidaki." Aneesa ta bata amsa. "Ina amsawa." Ta amsa a takaice "Wai har yanzu ciwon kan ne?" "A'a me kika gani?" "Babu komai kawai na ga kamar ba ki cikin nutsuwa?" "Ki bar kawai wallahi ɗazun bayan fitar ku Dr ya tabbatar min ina da ciki har tsawon wata biyu." "Shi ne abin tashin hankalin?" "Eh mana duka shekarar Miemie daya fa gaskiya ba haka na so ba." "Hmmm! Yar'uwa kenan wallahi wannan ba abin damuwa ba ne ki bar tada hankali ki yi addu'a Allah ya sauke ki lafiya, idan ta Miemie ne ba abin damuwa ba ne saboda Miemie tana cin komai tana tafiya kuma bata damu da nono ba."
"To ya zan yi dole ai na hakura Allah ya bamu masu albarka, Miemie kuma yanzu zan hado mata sauran kayanta dake dakina ku karata can, dama kun saba Allah ya raya maki ita." "Yar'uwa kina nufin kin yaye Miemie kenan?" "Eh, ta koma dakin Momman ta dama tun da ta zo duniya take ɗiyar Momma to yau Allah to yau Allah ya tabbatar." Ameesha ta gama maganar tana mik'ewa tsaye. Rasa abin da zata faɗa Aneesa ta yi don sosai abin ya bata mamaki, wato kyautar da Ameesha ta yi mata na Miemie tun ranar da ta fado duniya gaske ne? Lallai ta jinjina da karamci irin nata da zallar farin ciki da murna ta ce "Na gode sosai Ameesha Ubangiji Allah ya baki abin da kike nema duniya da lahira, wallahi da ana samun kishiya irin ki da ko wacce mace zata so a yi mata kishiya hakika ke kin bambanta da sauran mata, na cutar da ke Ameesha na mugunawa rayuwar ki amma duk da haka ke kullum da Alhairi kike nufina, a zatona tun da kin kasance shagwaɓaɓɓa idan kika auri Hamman za ki iya raba ni da shi ko dan salon SANGARTAR ki ashe abin ba haka ba ne, ki yafe min don Allah." "Na yafe maki Allah ya yafe mana baki daya." Ameesha ta faɗa fuska sake.
"Na gode Allah ya saka da mafificin Alhairi, Ubangiji ya biya maki buk'atar ki ya sauke ki lafiya." Murmushi kawai Ameesha ta yi ta amsa amin "Allah ya ci gaba da bamu hak'urin zama da juna da zuciya daya." "Amin" suka amsa tare. Sannan ta nufi bedroom kaf kayan Miemie ta kwashe ta kai bangaren Aneesa, farin cikin da Aneesa ta shiga a ranar baya misaltuwa. Ko da Dr ya dawo ya samu labari dariya kawai ya yi ya ce "Allah ya taya ta riko, Ameesha na lura dama kamar baki damu da Miemie ba?" "Haba beby wannan wacce irin magana ce? Miemie fa 'yata ce bana jin duk duniya akwai wanda ya kaini sonta, amma ka duba hidimar da Aneesa ke yi wa Miemie wallahi ta cancanci kyautar Miemie, na bata da zuciya daya Allah ya kara haɗe kanmu."
Rungumota jikinsa ya yi yana jin wani sabon soyayyar ta a zuciyarsa, bai taɓa ganin mai sanyin hali irin ta Ameesha ba, wallahi a time ɗin da suka fara haɗuwa da Ameesha a sahad bai taɓa tunanin tana da sanyin hali da tunani ba sai da ya mallaketa, kara matseta ya yi jikinsa ya ce "ina sonki matata so irin wanda bazai misaltu ba Allah ya yi maki albarka." "Nima ina sonka Dr Asmad Abubakar My fullo, Ina jinka har cikin zuciyata uban 'yayana, kullum fatana shi ne in faranta maka." Daɗi sosai ya rufe Dr jin kalaman da take faɗa masa, shi sai ya ji a duniya ya fi kowa sa'a. Sun daɗe a haka rungume da juna kafin Ameesha ta lankwashe murya tana faɗin "Beby wankan fa kalli time ga yi baka lek'a Aneesa da Miemie ba." "Oh! Wallahi har na manta, idan ina tare da ke manta kowa nake yi mu je ki yi min My wife." "An gama mijin mace biyu." Ta gama maganar da dariya. "Baki karya na autar Ummi ni ne mijin mace biyu Aneesa da Ameesha Baban Fatimah (Miemie)." Dariya sosai maganar Dr ya ba Ameesha don haka har suka shiga toilet din tana dariya.
Sun ci gaba da gudanar da rayuwar su cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har Allah ya sanya Ameesha ta shiga watan haihuwar ta, ranar wata Alhamis ta tashi da nakuda ga shi Dr baya gida, Aneesa ce ke ta taimaka mata amma fa sosai ta sha wahala fiye ma da haihuwar Miemie sannan ta haifi lafiyayyun yaranta biyu mace da namiji, tsaf Aneesa ta wanke yaran tare da shirya su cikin kayan sanyi masu taushi da kyau.