← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 54

Sashe 35

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(" To Nenne jotta saito miyahi Adamawa? Minna mi anda tomi andino da miyahino miwarti.") Yo Nanne wai a haka har Adamawa zanje, ni ai ban yi wannan tunanin ba, da tuni naje ai."

(Nenne d'oiliti moo) Harara ta yi masa cikin wasa,ta ce

( "Nananam 6ingel, jotta ad'on numa na saito a yahi ha Aneesa maan? To dei on narrata be mako?" )" Kuji min yaro , yanzu kai kana tunanin ba sai kaje wajen Aneesa ba? To kenan ta ya zaku fahimci juna?"

(" Allah Nenne sina gam awolwi mii tammai saito miyahi, amma jotta de a hirliti aam der satii do miyahan.") " Allah Nanne ban da yanzu da kika yi maganar ban san sai naje ba, amma tunda haka ne insha Allah cikin satin nan zan yi k'ok'arin shiga."

(" Yawwa barkantejo yahu Allah wanne barka.") Yawwa ɗan kirki ka k'ok'arta ka shiga ɗin Allah ya yi albarka."

("Amin") "Amin Nanne."

(Asmad noti d'on lara agogo jungo mako.) ya amsa yana kallon agogon hannunsa.

("Nanne hami yaha Asibiti gammi d'on momi wanni *CS* o badeke fintugo.") "Nanne bari na tafi asibiti don akwai wacce nayi wa *CS* to ta kusa farkawa."

("Allah wallu Nenne wii.") "Allah ya taimaka."

Nanne ta faɗa.

Mintina goma suka kai shi asibitin, a parking space ya paka motar sa, wasu takaddu ya kai hannu zai ɗauko kamar ance ya ɗago kai, sai kuwa idon sa ya sauka akan su.

Kara buɗe ido ya yi sosai, tabbas itan ce suke hira da saurayi da alama tana jin daɗin hiran musamman yadda take ta sakin murmushi, kana kallon su zaka gane su ɗin masoya ne, shi duk gani ganin da yake mata bai taɓa koda ganin tayi murmushi ba, amma gashi yau har dariya take, ji ya yi ransa ya sosu da ganin da ya mata haka.

_*( A'a ikon Allah, kuji shiga uku takabar suruki, inji Kamala Minna, in ba shiga uku ba ina ruwan Asmad da Ameesha? To ko dai ko dai..... bari nayi shiru don ban tabbatar ba.)*_

A fusace ya fita daga motar cikin zuciyarsa yana dana sanin zuwan sa asibiti a dai dai wannan lokacin, tabbas da yasan irin wannan gamon zai yi gaskiya babu abin da zai kawo shi.

Office ɗin sa ya shiga, sam bai samu sukuni ba a wannan rana, don hoton su kawai yake gani kota ina, tsaki kam har ya yi babu adadi.

Haka dai ya yi ta duba majinyatan nashi, duk don ya manta dasu amma ina kamar ma yanzu suke zaunen haka yake gani.

Su kam bama su san ya na yi ba, don hiran su suke sha irin ta masoya, Najeeb ne ya kawowa Ameesha ziyara har asibitin, karkashin wata bishiya suka zauna sai hira suke zubawa, sosai Ameesha ta kamu da yawa, bata k'aunar abin da zai raba ta da Najeeb don tana masa wani irin so ne.

Sun daɗe suna hiran kafin su ka yi sallama, shi ma badon sun so rabuwa da juna ba, Najeeb ya soma wucewa ita kuma ta kuma shiga ciki inda Meena ke jiranta

"Kai Meesha hala da ba zaku rabu da juna ba ne ? Kin shanyani Bros Abdul sai kirana yake."

"Ki bari kawai Meena wallahi in Ina tare da Najeeb bana k'aunar abin da zai gifta da sunan katse mana jin daɗin mu."

" Yana da kyau haka, yanzu dai tashi muje lokaci kan ya tafi sosai."

Meena ta k'arasa maganar tana ɗaukar jakarta, Meesha ma jakarta ta ɗauka sannan suka nufi inda motar Ameesha ya ke, suna zuwa shima Asmad na zuwa don shi ɗin ma gida zashi ya gaji da takaicin da yake tunawa

" Dr sai gobe."

Meena ce mai maganar,ita Madam ko kallon sa bata yi ba tayi shigewarta mota.

Murmushi ya yi ya ce

" Allah ya kaimu."

Tsaki taja tare da bama motar wuta ta juyo ta kalli Meena ta ce

"Ke kam kin fiye cusa kai ba k'warjini, wannan miskilin kikewa magana?"

" Babu wani cusa kai, yanzu ke fisbilillah ya da ce mu wuce ba tare da munyi sallama da shi ba?"

" Yo Ina ruwan biri da gada?"

Tayi maganar tana watsa hannu irin ko a jikina

Gyada kai Meena tayi cikin zuciyarta ta ce

"Allah ya shirya min ke."

Meesha kam bata kuma magana ba,don wayarta ta ɗauko ta kunna wak'a ,ita ma shiru ta yi har suka iso kofar gidan su Meena , buɗe kofa Meena ta yi ta ce

" To ta Najeeb! jikam sai gobe in Allah ya kaimu."

" Allah ya kaimu, don Allah ki zomin da han out ɗin nan na Chemistry, don gobe school zamu shiga kuma test jibi."

" Ok zan fito maki da shi ɗin."

Meena ta kai karshen maganar tana nufa get ɗin gidan su.

Meena tana wu ce wa, sai ta soma duba wasu takaddun ta ,duk ta duba motar babu ,da sauri ta kira Meena ta ce bata gansu ba, fitowa Meena ta yi ta ce "ki koma asibiti, muje ina raka ki."

"No Meena koma gida kawai bari na koma asibitin."

Ta ida maganar tana juya kan motar ,gudu take yi kai tsaye asibitin ta shiga don babu tantama a cen ta zubar, addu'a takeyi Allah yasa ta gani.

Tana shiga ta faka motar cikin sauri sauri ta fita , cikin ta shiga ta dudduba amma bata gani ba, bayan ta gama duba duk inda take saran ganin takaddun amma bata gani ba. Sai kawai ta dawo gurin motar jiki a mace, ji take kamar ta kwanta ta yi ta birgima da ƙafafuwanta kamar dai yadda yara suke yi idan abu ya ɓata masu rai sosai. Ta kai hannu jiki a mace da niyyar buɗe motar sai ta ji magana kamar daga sama.

" Lafiya ki ka dawo?"

Ta juyo kamar ta k'wala ihu, rasa abin da zata ce ta yi,sai ta zuba ma sa ido game da langaɓar da kai gefe hawayen da ta ke ɓoyewa , suka ziraro.

Mamaki ya kama Asmad,duk irin tsiwarta,yau kuma ita ce ta koma haka. Sai kawai ya yi murmushin da yake k'arawa fuskarsa kyau , buɗe wani file ya yi ya zaro takardun tare da mik'a mata.

_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:05 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

``` ina matukar taya ki murna my sweet sister BILKISU BILYAMIN Ubangiji Allah yasa kifi haka Allah ya kara baiwar fasaha da kaifin brain```

*Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*

*11*

A hankali cikin mutuwar jiki ta kai hannu ta amsa.

" Na gode"

Ameesha ta yi maganar cikin wani irin voice.

Murmushin nan ne dai kwance a fuskar sa

" no need "

Ya bata amsa, yana juya kai, bai wani bata lokaci ba ya tada motarsa don dama jiranta ya tsaya yi, kuma tunda ta dawo har ta amshi abin ta mai zai tsaya yi.

Fuskar nan tata yake gani kota ina, yanayin da ta shiga dazun yake mamaki, da wannan tunanin ya kama hanyar gidan su.

Ameesha kuwa bayan wucewar sa, da kallo ta raka motar har sai da ya kulewa ganin ta sannan ta saki wani sansanyan ajiyar zuciya a fili ta furta

" Allah na gode maka."

Motarta ta koma, zuciyar ta cike da tunanin Dr dan fullo, da irin taimakon da ya mata a wannan rana, da wannan tunanin ta isa gida.

Parking ta yi tare da zaro hand back din ta, cikin rashin kwarin jiki ta nufi hanyar shiga falo, dan juyowar da zata yi sai ko idonta ya sauka kan motar Najeeb dake aje a parking space, siririn tsaki taja ranta ya dan sosu da ganin motar.

Falo ta shiga ko sallama bata samu ikon yi ba sai ma zubewa da ta yi a kujeran falon ta furta

" Wash! "

Ummi dake fitowa daga kicin ta zubawa Ameesha ido, da mamaki ta ke kallonta don duk wanda ya ga Ameesha yasan ba a cikin nutsuwa take ba.

" Lafiya kuwa Auta? "

Ummi ta karasa tambayar tana nufa inda Ameesha ta ke.

Wani murmushi ta k'ak'alo wanda iya karsa lebe, don tun kallon da Asmad ya mata Jikinta ke mace.

" Ummi lafiya lau fa, kawai gajiya ce."

Ta bata amsa tare da maida hankali kan Ummi.

Zama Hajiya Halima tayi tare da riko hannun Ameesha, don ko kadan bata kaunar damuwar Ameesha.

" Anya kuwa Ameesha? Jifa yadda kika koma kodai baki da lafiya ne? "

Girgiza kai tayi alamar a'a.
" Are your sure?"

"Sure Ummi."

" OK tashi kije kiyi wanka, sai ki ci abinci, ga Najeeb can yana jiran ki."

"To " kawai ta amsa tana mikewa.

A toilet ma dai da Ameesha ta shiga, duk tunanin Asmad din ne a zuciyar ta, ruwa ta watsa tana fitowa ta shirya, Yau simple dress tayi, don riga da siket ta sanya na atamfa, powder ta mursa sai lipstick da ta shafa, ya zuwa wannan lokacin miss call a wayarta sun haurawa ashirin, a fusace ta dauki wayar

" Hello." ta fada bayan ta Kara wayar a kunne.

Banji mai aka ce mata ba Sai ce wa ta yi, ai nasan da zuwan ka amma yau sai dai ka daga min Kafa don ina da bukatar in samu nutsuwa."

Fadin haka keda wuya ta yanke kiran, tare da jifa da wayar rai a bace, tafiya ta soma yi don sauka falo, domin tasan matukar bata sauka falon ba to Ummi sai ta daga hankalin ta.

Najeeb kuwa tunda ya ga Ameesha ta datse kiran, yasan da matsala, shi kuma baya son tambaya don haka sai ya fito daga falon bakin da yake, jikin sa a sanyaye yana Addu'a Allah yasa ba shi ya bata mata rai ba.

Koda ta kammala da cin abinci sama ta koma, tana shiga taji karar wayarta, da sauri ta karasa tare da d'auka, suna nan Meena ta gani akan screen din.

" Ya Meesha wai kuwa kinga takardun? "

Ajiyar zuciya ta ja ta ce

" Eh Meena na gani a asbiti."

" Masha Allah, wallahi tun dazun tunani kawai nake yi fa."

" Ki bari kawai Meena zamu hadu a school akwai labari."

" Allah k'awata? "

" Allah kuwa."
Chapter 35 · 0% Book details