Sashe 4
Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*
``` Wannan page din kyauta na baki RUFAIDA OMAR fatan Alhairi a gareki da zuri'arki baki daya, Zulayheart Rano tana yinki sosai Allah ya kara maki basira da kaifin k'wak'walwa na fasihiyar marubuciya mai baiwar fikira da Nagarta```
*30*
Tsam ya rungume ta cikin jikinsa, yana kallon yadda take fusgar numfashi da kyar! Duk tausayinta ya cika shi. ɗago da kai ya yi ya ce
"Nenne bani ruwa da towel a goge mata jiki zafin zai ragu." Yana maganar ne yana kuma tallabar ta.
"To." Nenne ta amsa tare da fita. Cikin sakan ashirin har ta kawo masa ruwan, koda ta ba shi fita ta yi don ta ba shi waje. Yana ganin Nenne ta fita sai ya yi saurin kwantar da ita, ya zame rigar ta cikin nutsuwa yake bin jikinta da jikakken towel din yana manna mata, jikin dai har lokacin da zafi amma numfashi ya daidai ta.
Rasa yadda zai yi da ita ya yi, domin shi a wannan lokaci ya manta shi fa Dr ne, sai zuwa can wata basira ta fado masa cikin sauri ya kuma rungumota ya cusata a jikinsa ya soma murza mata baya ahankali, ya yi kusan minti sha biyar kafin ya ji zafin jikin ya koma daidai.
A lokacin kuwa har bacci ya yi gaba da Ameesha, a hankali ya zame jikinsa ya gyara mata kwanciya. Fita ya yi ya dauko first aid kit ɗinsa, allura ya haɗa ya yi mata. Ya zauna a gefenta yana kallonta fuskarsa ɗauke da damuwa, sosai yake jin Ameesha a zuciyarsa baya k'aunar koda 'kuda ne ya sauka jikinta balle aje ga batun ciwo.
"Sannu Asmad har ta samu bacci kenan?" Muryar Nenne ya ji.
"Eh! Ta samu yanzu." Dr ya bata amsa.
"To ya kamata dai ka tafi gida, domin dare yana kara yi fa, yanzu tara harda rabi." Ta dire maganar tana kallonsa.
Jikinsa sam babu kwari ya mike yana faɗin,
"To Nenne sai da safe duk yadda ake ciki da safe sai ki sanar min, duk da nayi mata allurar saukar da zazzabi." Cikin sanyin murya ya yi maganar.
"Allah ya kaimu, insha Allahu za ta samu sauki zuwa safen ma." Cikin karfafa masa gwiwa ta yi maganar.
Fita Dr. ya yi badan ya so tafiyar ba. Da tunanin Ameesha ya isa gida, ko da ya shiga cikin falon babu kowa don haka bai tsaya ba sai ya nufi bedroom ɗinta. Kwance ya same ta kallo ɗaya zaka mata kasan ba bacci take ba, zama ya yi kusa da ita yana faɗin
"Madam har kin kwanta?"
Wani mugun kallo ta aika masa da shi tare da juya masa baya, mamaki ya kama Dr. ganin dai lafiya lau suka rabu ɗazun amma yanzu har ta ɗauki fushi
"Wai lafiyar ki kuwa?" Ya kuma mata magana.
Tsaki ta ja mai karfi ta ce,
"Ina ruwan ka da lafiyata? Ba wajen amaryarka ka je ba? Ita wato ka damu da damuwarta? Amma ni da yake baka kaunata baka damu da halin da zan shiga ba, ai shi yasa ka yi tafiyar ka sai yanzu kake dawowa anya ma kuwa Hamman kana tsoron Allah?"
Murmushi mai ciwo ya yi ya ce, "Ki yi hakuri duk yadda kike tunani ba haka bane, amma ki yi hakuri." Daga haka yasa kai ya fita.
Domin dai zafin karshen maganar Aneesa basu da maraba da saukar tafasasshen ruwa a jikinsa, ya barta mata dakin ne don karda zuciya ta sashi aikata mummunan aiki. Amma tabbas maganar ta ta bata ransa, duk iya kokarin da yake akanta bata gani, yana lallaɓata ne ba dan komai ba sai su Nenne amma yau har ta iya bude baki tana fada mishi *Yana tsoron Allah kuwa*. Ajiyar zuciya ya sauke a fili ya furta, "Aneesa kenan kinci daraja ɗaya amma karki bari laifin ki ya kara girma, domin dai akwai babban laifin da kika aikata min mafi muni amma na barki ne har zuwa lokacin da zan baki mamaki.
Dafe kai ya yi da ya tuna lokacin da ya yi arba da Aneesa ta zubar masa da cikinsa, tsab! Yasan tana da ciki amma sai bai nuna mata ba, shi ne da ta tashi ta zubar da shi zai nuna mata bata da wayyo rakata kawai ya ke.
Tashi ya yi zuciyarsa sam babu daɗi ya nufi toilet, ruwan sanyi ya sakarwa kansa, ya yi kusan minti sha biyar kafin ya fito, sallaya ya shimfiɗa domin dai ya dauro alwalarsa.
Tada sallah ya yi, sai da ya gabatar da ishsha a ya yi shafa'i da wuturi, addu'oi sosai ya yi na nemarwa Ameesha lafiya kafin daga bisani ya tashi tare da cire jallabiyar jikinsa ya jawo laptop ɗinsa don ya ci gaba da binciken da ya soma.
Bar mu waiwayi NAJEEB da amaryar sa.
Kasancewar yau week end, Najeeb ne zaune a k'aton falon gidansa, daga shi sai singileti da gajeren wando, hannunsa cup din fresh milk ne yake kurba. Rufaida ce ta fito cikin kyakkyawar shirinta na atamfa riga da siket sosai kayan suka mata kyau, fuskarta ta sha kwalliya, jikinta sai fitar da sansanyar kamshi yake.
Fuskarta ɗauke da murmushi mai birgewa ta nufi Najeeb ɗin rankwafawa ta yi dai dai fuskarsa ta ce"Ranka ya dade barka da hutawa." Cikin sanyin murya ta yi maganar.
Ɗago kansa ya yi cikin nashi murmushi ya ce
"Barkammu dai gimbiya, kin yi kyau"
"Na gode! Ta faɗa tana zama a kasan carfet tare da lankwashe ƙafafunta.
"Kamar kina son yin magana ko?" Ya dire maganar idonsa a kanta
Murmushi dai ta kuma yi tana wasa da yatsun hannunta ba tare da ta ce komai ba.
"Rufaida! Ya ambaci sunanta cikin wata irin murya. Saurin ɗago da kai ta yi jin yadda ya kira sunan.
"Na'am." Shi ne abin da ta iya faɗa.
"Me yasa kike min haka bayan kinsan mun zama daya Ni mijinki ne, ke matata ce, ki daina ɓoye min komai duk abin da kike bukata ki sanar min insha Allahu zan yi kokarin yi maki."
Gyada kai ta yi ta ce
"Babu komai fa Ranka ya daɗe."
"No! Rufaida tell me your problem."
"Sadda kai ta yi ta ce dama cewa zan yi ka kaini gidanmu ina son ganin Mamana." Cikin kunya ta k'arasa maganar, don sosai take son ganin family ɗinta tunda aka kawota babu wanda ya zo.
"Oh! Baby dama don wannan ne kika kasa faɗa min? To bari na yi wanka sai mu je har gidan Mummy." Cikin sakin fuska ya ke maganar.
Wani farin ciki ne ya rufe Rufaida har bata san time ɗin da ta rungume Najeeb ba, tana zuba masa godiya cikin tsantsan jin dadi.
"Na gode *hubby*." Ta faɗa tana kara hugging ɗinsa.
"You are welcome my baby, Amma fa sunan can da kina ambata ya min daɗi ki rika kirana da shi ina son sunan."
Kunya ce ta kama Rufaida, da sauri ta sake shi ta na nemar hanyar guduwa, har ta kusa shiga koriɗo wanda zai sadaka da ɗakunan baccinsu ya ce
"Baby ki haɗa min ruwan wanka gani nan zuwa."
"To." Ta amsa tare da shigewa.
Murmushi ya yi tare da girgiza kai, cikin farin ciki da samun Rufaida matsayin mata sam ita bata fushi, yana alfahari samun ta matsayin mata, shi yasa tun da Mummy ta yi masa bayanin aurensa da Rufaida, komai bai ji ba na takaici ko da nasani, domin dai Rufaida ma masoyiyar sa ce, yasan ya so Ameesha so na gaskiya amma tunda Allah baiyi nufin ita matarsa ba ce ya yadda da kaddara, ya kuma rungumi matarsa yana addu'ar dorewar zaman lafiya a aurensa.
Da taimakon Rufaida ya kammala shiryawa, cikin wasu riga da wando wanda suka amshi jikinsa, sansanyar kamshi turare ke fita daga ko wane lungu na jikinsa, keys ɗin mota ya ɗauka yana faɗin
"Madam mu je ko?"
Murmushi ta saki tare da daga kai alamar "to."
"Ka yi kyau hubby." Cikin muryarta mai sanyi ta yi maganar.
"Na gode." Shi ne abin da Najeeb ya faɗa yana ci gaba da tafiya.
Sai da suka biya wani babban kanti ya sayawa iyayen Rufaida tsaraba wacce zata kai masu, domin ko ya basu kuɗi ba amsa zasu yi ba, shi yasa ya sai masu kawai, tare suka shiga bayan ya gaida da Mamanta sai ya koma mota inda zai jirata, sai Maman ta yi farin ciki da ganin yartata don da gani hankalinta a kwance yake duba da irin kyaun da ta yi.
Bata wani jima sosai ba ta yi masu sallama, zata ta fi
"Hajiya ki yiwa mijinki godiya, mun gode Allah ya saka da Alhairi, don Allah Hajiya ki kula da auranki duk abin da zaki gani ki rika hakuri kin ji ko?"Maman Rufaida ke mata nusiha, da yake bata faɗan sunan Rufaida sai dai ta ce mata Hajiya, don sunan k'anwar mahaifiyar ta aka sanya mata.
"Insha Allahu Mama zan yi yadda kika ce, mu dai a ci gaba da yi mana addu'a."
"Addu'a kam ana yi sai dai a kara kaimi, Allah ya kai ku gida lafiya."
Da haka suka yi sallama, ji ta yi kamar kar ta tafi, a mota ta same shi yana zaune yana latsa wayarsa kamshin turare ta ya sanar shi isowarta.
Ɗago da kai ya yi tare da aje wayar ya ce
"Har kin fito?" Ya yi tambayar idonsa a kan ta.
"Eh! Ta bashi amsa tana bude kofar motar.
"Mama ta ce ayi maka godiya." A hankali ta yi furucin.
"No ba sai sun gode min ba domin suma iyayena ne." Cikin kulawa ya bata amsa.
Murmushi ta yi don ta ji dadin furucin sa, da haka suka isa gidan Mummy, sosai Mummy ta ji dadin zuwan Rufaida sai nan nan take da ita, tana son Rufaida har cikin ranta domin Allah ya yota da nutsuwa ga hankali uwa uba kuma kunya.
Nan Najeeb ya barta akan bayan magriba zai zo ya dauketa su koma gida.
***