← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 54

Sashe 38

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitar Najeeb ɗin sai Dr ɗan fullo ya watsawa wa Ameesha harara ,wanda akayi sa'a tagani

" Ashe daman rashin lafiyar karya ki ke yi?"

" Bangane ba?" Tayi tambayar tana murguɗa baki.

"Ai dama ba zaki gane ba, tunda fa kinsa wannan k'aton a gaba kina masa dariya taya za ki gane?"

Mamakin maganar nasa take yi, don bata fahimci me yake nufi ba... Bata gama tunanin ba sai ta kuma tsinkayar maganar sa

" Bari na sallame ki don nan asibiti ne ba gidan love ba, don naga alamar ke baki da ta ido, a gaban iyayen ki sai ki zauna kina wa wani k'ato murmushi, ku ala dole ga masoya ko? To kuje gida can kuyi soyayyar."

Yana maganar tana aika masa harara, cikin zallar rashin kunya.

Yana gama faɗin haka ya mik'a mata takaddan da ya rubuta mata sallamar, sannan ya yi sallama da su Ummi ya yi gaba, ita kam banda juya maganar da ya faɗa mata babu abin da ta ke yi, gaba daya ta kasa gane inda maganar ta dosa .

" Auta ya ce ya sallame ki ko?"

" Eh Ummi ga takardan da ya bani."

" Ok to bari mu tafi kenan, dama ɗazun na rage wasu kayan."

Dan danan suka tattara kayan su suka koma gida.

Yau dai rana bata karya a yau asabar aka ɗaura auren Asmad da Aneesa wanda dubban jama'ar Adamawa suka shaida, shi dai ango a nashi fannin babu kuka babu dariya, baya farin ciki kuma baya bak'in ciki.

Yana cikin abokan sa sai harkan bikin suke.

Aneesa kuwa yau babban burinta ya cika, tunda yau ta kasance matsayin matar *Asmad Abubakar ɗan fullo* ta zama matar Dr ɗan fullo kyakkyawan matashi mai ji da kyau da kuɗi,kai ita kam babu wacce ta kaita sa'a.

Ana gama ɗaura aure suka kamo hanyar kano, inda abokan sa suka shirya masa dinner a cikin wani haɗaɗen hall mai suna *Zamani* .

Basu isa gida ba sai bayan magriba, don haka wanka kawai su ka yi ta yi tare da salloli, sannan suka soma shiri don karfe goma za'a fara tafiya.

Sosai amarya ta yi kyau na ban mamaki, take aka fara haska bikin cikin gidajen Talabijin, a dai dai lokacin Ameesha ne zaune da Abbanta yana lallaɓata akan ta sha yogurt ɗin da ya shigo mata da shi, don kwata kwata bata son cin abinci TV Abbanta ya kunna ya kamo tashar liberty , dai dai sanda ake nuno shagalin bikin.

Sam Ameesha hankalin ta bashi kan tv ɗin sai da Abbanta ya ce

"A'a uwata wannan ba shi ne likitan da ya duba ki ba ?"

Gabanta ya yi wani irin faduwa da jin maganar Abba, saurin ɗago kai ta yi tare da watsa idonta akan TV ɗin Dr ɗan fullo ne da wata sun yi mugun kyau, gashi sun da ce da junansu.

"wai dama da gaske aure zai yi?"

Gyada kai ta yi da kyar ta buɗe baki ta ce " eh shi ne" tana gama faɗin haka ta yi saurin mik'ewa tare da nufa bedroom ɗin ta hankalinta a mugun tashe.

Ko da ta shiga bed room ɗinta,kuka ta fashe da shi irin mai ban tausayi, wani irin zafi ta ke ji a zuciyarta, ta rasa me ke mata daɗi ta ji takaicin auren Dr tana nan tana fama da ciwon sonsa, ashe yana da wacce yake gashi har an ɗaura aure suna can cikin farin ciki, ita kuma tana fama da ɓaci rai

Ta sha kukan ta inda daga karshe ta rarrashi kanta, Amma ko da safe da ciwon kai ta tashi, don kar ta ɗaga hankalin su Ummi sai kawai ta cije.

Ganin bata iya direvin mota ya sa ta amsa kudi wajen Ummi, sannan ta fita ko tsayawa jiran Meena bata yi ba
*** *** ***

Kai na gaji Yaseen

Please kuyi min addu'a am not feeling fine 👏

_*Yar Mutun Rano*_
[10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*
*14*

Tsaye ya ke a kofar gidan hannayen sa rungume a kirjin sa, ya zubawa get ɗin gidan idanu, burinsa bai wu ce yaga ta fito ba , gefe ɗaya kuma yana tunanin yadda zata kaya, rabon sa da zuwa wajen ta yau kusan wata biyu kenan.

Yanzu ma nazari ya yi ya ga dai tabbas bata cancanci irin wannan hukuncin daga gare shi ba, sosai ya lula duniyar tunani,sai jin Muryar ta ya yi ta na faɗin

" Barka da zuwa, yau a gari, ashe talaka na ganin ku?"

Ju yowa ya yi tare da sauke idonsa a fuskarta, wanda ke ɗaure kamar bata taɓa sanin wani abu wai shi murmushi ba balle dariya ba, take ya ji gaban sa ya faɗi da yanayin ta, da kyar ya dage tare da tattaro nutsuwar sa ya buɗe bakin sa da ya masa nauyi ya ce

" Ki yi *Rufaida* wallahi abubuwa ne su ka yi min yawa."

(Fatan masu karatu basu manta da Rufaida ba, asalin budurwar Najeeb?")

" Har suka hana ka ɗaukan wayata?"

Ta yi saurin jefa masa tambaya, har yanzu bata ko kalli inda ya ke ba.

"No Ruffy ba shi ne yasa ba ."

" Ok ganin dama ne kenan? Ashe haka k'auna take komawa? Wallahi Najeeb ka bani mamaki ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba"

"Kiyi hakuri Ruffy na yi kuskure, amma insha Allah haka ba zai kuma faruwa ba."

" Hmmmm Najeeb kenan ai bana jin akwai abin da zaka gaya min in yadda."

"Haba Please Ruffy ki fahimce ni, kin fi kowa sani halina fa, Please ki yafe ni."

Da kyar ya lallaɓata ta yadda, da abin da ya ke faɗa mata.

"Fatar kin yafe min?"

" Ba komai Najeeb amma tabbas kasani a damuwa, har nake tunanin na aikata maka ka dai dai ba."

" Baki min komai ba, kuma gani yanzu nazo fitar da ke." Ya karasa maganar cikin murmushi.

Itama murmushi ta saki ta ce

" Tom nayi farin ciki, amma fa Najeeb ina ga lokaci ya yi da zaka gabatar da kan ka a wajen Abbana."

" Karki damu na kusa shiga,so nake na kammala wasu abubuwa."

"Allah ya tabbatar da Alhairi."

Haka Najeeb da Rufaida suka kasance cikin hira irin ta masoya.

Sam Rufaida Allah ya yi ta bata da fushi, ko da yaushe fuskantar a sake take bama idan tana tare da Najeeb manta duk wani damuwa ta ke yi.

Shi kuma Najeeb gefe ɗaya tunanin Ameesha ne ya addabi zuciyarsa, tabbas yana don Ameesha sai dai kuma yana alhinin rabuwa da Rufaida.

Ameesha kuwa ko da ta fita a gida, ta yi tafiya mai dan nisa bata samu adai dai ta ba, ga jikinta na ci gaba da ciwo, kan wani ɗan dakali ta zauna tare da zubawa hanyar ido, duk wanda ya ganta ba zai ce ita ce Ameesha yar Abba ba, gaba ɗaya ta canza ta koma wata silet.

Tana zaune dai a wajen, tana kuma hango nafef ɗin amma ta kasa yadda zata tsayar da su,don bata saba ba, sunkuyar da kai k'asa ta yi wasu siraran hawaye suka zubo, hak'ik'a tana son Najeeb sai dai kuma bata jin sa kamar yadda take jin Asmad a zuciyarta, ta rasa gane wani irin abu take ji ɗin game da shi... Firgigit ta yi saurin ɗagowa da kai sakamakon jin hon na mota a gaban ta.

Kallon mai motar ta yi cikin rashin sani, murmushi ta cikin motar ta yi wanda suka amshi fuskarta, cikin Muryar ta mai sanyi ta ce

" In ba za ki damu ba muje na rage maki hanya?"

Lokaci ɗaya Ameesha ta ji tana son matashiyar matar, da bazata wuce shekara ashirin da biyu zuwa da uku ba

Saurin share hawayen ta yi , don kar ta fahimci halin da ta ke ciki.

" School fa zani." Ameesha ta bata amsa.

" Wane school ɗin? don nima can na nufa."

"B.U.K"

Ameesha ta bata amsa.

" Ok shiga muje , nima can zan shiga ina da laccan safe ne."

Shiga motar Ameesha ta yi , ta zauna tana mai ambaton Allah a zuciya.

" Sunana Khadija Yaseer amma an fi sanina da *Ni'eema* fatan zamu zama kawaye?

Murmushi ta saki ta ce

" Insha Allah ni kuma Maryam Taheer wacce a ka fi sani da *Ameesha*."

"Masha Allah Ameesha Allah ya bamu ikon zama da juna cikin amana, ina da aure da yara biyu asali mu yan Kaduna ne aiki ya dawo da mijina nan, in zan tafi makaranta ina yawan ganin ki da wata cikin mota kuna tafiya"

Murmushi ta saki don tana jin daɗin hiran da su ke yi ,gefe guda kuma tana mamaki da Ni'eema ta ce tana da yara biyu, don ba mai kallonta ya ce ta yi aure bare kuma a ce da yara, saurin kawar da tunanin ta yi ta ce

" Eh matar yayana ce , kuma kawata tare muke tafiya yau bata da laccan safe, ni bani da aure tare da iyayena na ke."

Da wannan hirar suka isa school ɗin, har a zuciya Ameesha ta ji tana son Ni'eema, har musayan number su ka yi da ita .

Da yake Ni'eema tana 300 level ne, Ameesha kuma na 200 level.

*********************************

Can kuma wajen ango da amarya an sha shagali sosai ko dinner sai biyun dare aka tashi, washe gari kuma aka buɗe asibitin Ango Asmad mai suna *A&A* special hospital asibitin da ya samu kwararrun likitoci.

Sai muyi fatan alheri ga wannan gudunmawa ga al'umma wanda Asmad da Alhaji Abubakar suka samar.

Amarya Aneesa buri ya cika fata ga Asmad matsayin miji da mata, sosai Asmad ɗin ya ke k'ok'arin sauke duk wani nauyi na Aneesa da ke kansa, duk wani tana jin farin ciki ya na bata, shi yasa cikin kwanaki kaɗan ta murje ta yi kyau sosai.

Meena ce ta haura saman Ameesha, ta kalli ta a tsorace cikin mamaki ta ce

"Meesha anya kina da lafiya kuwa?"

"Me ki ka gani?

"Meesha ki kalli yadda ki ka koma, baki magana baki cin abinci, baki da walwala ko yau she kina cikin daki ki zauna ki yi shiru, why why Meesha?"
Chapter 38 · 0% Book details