← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 54

Sashe 47

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe uku ya taso daga office daret gidan Nenne ya wuce, har yanzu dai ba a cikin nutsuwarsa ya ke ba musamman yadda ya yi parking motar zai nuna maka haka, cikin falon ya shiga bakinsa dauke da sallama. Nenne dake zaune duk abin duniya ya dameta ta saki ajiyar zuciya ganin Asmad ɗin, ta tabbata zata samu rangwame cikin damuwarta, amsawa ta yi da sakin fuska. "Barka da yammaci Nennena fatan kin wuni lafiya?" "Barkammu Asmad lafiya lau ya Aneesa da Ameesha." "Duk suna lafiya." Ya bata amsa fuska babu walwala. "Asmad lafiya kuwa?" "Ummh Nenne me kika gani?" Ya yi tambayar bayan ya kalkalo murmushi dole.

"Babu shakka yau na san babu lafiya a gidanka, domin kallo ɗaya mutum zai yi ya fahimci haka kamar yadda nima na fahimta, me yake faruwa a gidanka?" Tambayar ta yi fuska ba alamar wasa. "Babu komai Nenne kawai bana jin dadi ne." Ya bata amsa yana shirin mik'ewa. Murmushin takaici ta yi ta ce "Na ji lafiya lau ina Ameesha?" Dawowa ya yi baya ba tare da ya shirya ba sai jinsa ya yi yana shirin faduwa, bai iya magana ba sai dafe kansa ya yi dake barazanar tsagewa. "Tambayarka na yi ina Ameesha?" Cikin tsawa ta yi maganar wanda har Ameesha dake bacci sai da ta farka.

"Ku gafarceni Nenne jiya mun sami matsala da ita da dare har na ce mata ta tafi gidansu..." "Kun sami matsala? Asmad dama kana daya daga cikin mazajen nan masu rasa hankulansu idan mayensu sun yi masu laifi? Ka bani mamaki ka tozarta mu a idon duniya, matarka ta aure ka kora da dare don kun samu matsala ko? Ya yi kyau tashi ka bani waje." Da zallar faɗa wanda tunda yake da ita bai taɓa sanin tana da fada ba sai yau ta dire maganar tana nufa hanyar bedroom. Duk yadda Asmad yaso tsayar da Nenne abin ya ci tura domin yadda ta haɗa girar sama da ta kasa, lallai yasan ya batawa mahaifiyarsa rai tunda har ta dau zafi da shi.

Jiki a sanyaye ya fita daga falon, haushin Ameesha ya kuma darsuwa a ransa tunda akanta har Nenne ta yi fushi da shi irin wanda bata taɓa yi ba, bayan kuma kowa ya ji yasan ita ke da laifi. Mtsww ya ja tsaki yana bama motar wuta.

Nenne na ganin Dr ya fita ta ɗauki wayarta layin Hafiz abokin Dr ta kira, ringing biyu ya dauka cikin ladabi ya gaidata kafin ta sanar masa tana son ya zo gidanta ya duba Ameesha amma kar ya sanar da Dr, cikin mintinan da basu gaza talatin ba ya isa gidan, bayan sun gaisa ta kaishi daki inda Meesha ke kwance. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗan saki murmushi domin kamar hasashen da yake ya tabbata. Don haka sai ya shiga mata tambayoyi sannan ya amshi fitsarin ta ya kuma debi jininta.

Kallon Nenne ya yi yana faɗin "Nenne bari na je lab a yi test bazan jima ba." "A dawo lafiya." Nenne ta faɗa cikin sakin fuska. A kalla Dr Hafiz ya yi kusan awa kafin ya dawo fuska cike da fara'a mai tsanani. Mika mata farar takadda ya yi yana faɗin" masha Allah Nenne Meesha na dauke da ci..."

😓 *Ba sai kun faɗa ba walle nima nasan ina da matsala sosai, na rasa abin da yasa nake jin kiwar typing gashi abin ya zo gangara, ku kara hakuri dai kaɗan ya rage in sha Allah.*

Ina son ki har cikin raina my fan's😘😘

*YAR MUTAN RANO*
*SANGARTA*

©
_*ZULAYHEART RANO*_

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*47*

"Masha Allah! Nenne Meesha na dauke da ciki har na wata daya da kwanaki." Wani irin farin ciki ne ya ziyarci Nenne wanda rabonta da jin irin wannan farin cikin tun lokacin cikin Asmad "Alhamdulillah! Ta furta a bayyane fuska cike da zallar farin ciki. "Sannu da k'ok'ari Hafiz na gode da wannan kyakkyawan albishir ɗin." Meesha kam tana gama jin bayanin Dr Hafiz sai wasu hawaye na farin ciki suka soma zubowa daga idonta, hakika wannan rana ta zame mata na farin ciki domin daga wannan rana ta fita daga zargin da Dr ke mata, tana son ganin farin cikin da Dr zai yi idan ya ji tana dauke da cikinsa, gaba daya sakin baki suka yi suna kallonta don hawayen da take ba na wasa bane "haba Ameesha ke da zaki yi farin ciki sai kuma ki ke hawaye?" Hafiz ne ya yi maganar cikin sigar lallashi.

Murmushi ta yi kanta a kasa, bata jin zata iya sanar da kowa sirrinta da mijinta, don haka sai kawai ta ce "Babu komai fa Hafiz farin ciki ne kawai." Ta dire maganar tana sinne kai cikin filo. Murmushi suka yi gaba daya, sannan Dr Hafiz ya mik'e yana faɗin "Nenne zan k'arasa gida anjima zan kawo mata wasu magunguna." "Allah ya kaimu." Nenne ta faɗa da murmushi. Bayan tafiyar Dr Hafiz sai Nenne ta tsare Ameesha akan sai ta faɗi abin da take so.

"Nenne ni fa bana jin cin komai." "A'a Ameesha kin ga ki daure ki faɗa min bana son zama da yunwa balle kuma ba ke daya ba ce yanzu." "Zan rika ci Nenne faten dankalin turawa nake so." "Yawwa Yar Nenne haka nake so." Nenne ta yi maganar tana mik'ewa, da kanta ta shiga kicin ɗin ta soma haɗawa Meesha abin da ta ce tana so, faten ta yi mata mai ruwa ruwa yadda zata ji daɗin sha har da alayyahu ta yanka ciki da hanta, lokacin da ta shiga har bacci ya soma daukar Meesha, don haka cikin hikima da dabara ta tashe ta. "Sannu da k'ok'ari Nenne." Ameesha ta yi maganar tana tashi daga kwanciya. "Yawwa ta shi ki sha da zafinsa." Ruwa ta bata ta kuskure baki sannan ta bata abaki, ba ta wani ci da yawa ba ta ce ta koshi.

Duk yadda Nenne taso ta kara dole ta barta, toilet ta nufa ta sakarwa kanta ruwa masu dan zafi don ta ji dadin jikinta, bayan ta fito kayan jikinta ta mai da domin bata da kaya a gidan, Nenne ne ta shigo ta kalli Ameesha ta ce "Har kin fito?" "Eh" Nenne sai dai "bani da kayan sawa." A shagwaɓe ta yi maganar. "Kuma fa bari na kira Asmad ya kawo maki." To kawai ta amsa tana ci gaba da wasa da zaren rigarta. Tana kallon Nenne ta fita tana waya.

Ba a fi minti talatin ba, tana kwance kewar jikin Dr take tana son ta ji dumin jikinsa, Kamar daga sama ta ji sallamar sa murya ciki ciki, da sauri ta tashi zaune tana amsa sallamar "Sannu da zuwa baby." Ta faɗa tana kallonsa. "Yawwa." ya amsa a takaice fuska babu walwala. "Ga kayanki nan da kika sanya na kawo maki, dama na kula tuni baki son zama da ni shi ne dalilin ki na shan magani, tunda ba ki son zama dani me ya kawo ki gidan iyayena?" Ya kai karshen maganar yana daka mata tsawa.

Tun kan ya gama maganar, hawaye ya soma wanke mata fuska domin maganar sa yana daga mata hankali, murya na rawa ta ce" Ka yi hakuri ba da wata manufa nazo nan gidan ba, kuma wallahi laifin da kake tuhumata da shi bani da masaniya..." Hannun da ya daga mata ne ya sanya ta yi shiru da maganar ta amma hawayen basu tsaya ba.

"Kinga ki yi min shiru ai kin sire min Ameesha yadda na daukeki kin bani kunya, sai an yi magana ki farawa mutane kukan SANGARTA." Mtsww ya ja tsaki kafin ya bar mata dakin. Ragaf ta faɗa kan gadon ta saki sabon kuka sam bata son irin abin da Dr yake mata, duk da yanzu tasan Allah ya wanketa to amma ai muggan kalamai Dr bai daina furta mata ba, haka ta ci gaba da kukan har bata san lokacin da Nenne ta shigo ba sai jin muryar ta ta yi "Ameesha lafiya kike kuka?" Hankali tashe ta yi tambayar.

Saurin share hawaye ta yi ta kalkalo murmushi ta ce "kaina ke min ciwo Nenne kamar zai rabe biyu." "Allah ya baki lafiya, fatan kin sha magani?" Ta yi tambayar badan ta yadda da abin da Meesha ta faɗa ba. "Eh na sha." Ameesha ta bata amsa. "Ki bar kuka zai daina." Nenne ta k'arasa maganar tana fita, cikin zuciyarta tana sanyawa Meesha albarka ta tabbata Ameesha suruka ce ta kwarai tunda har tana iya ɓoye matsalar ta da mijinta, kwafa ta yi a ranta ita kadai tasan abin da zata yiwa Dr.

Ameesha na ganin Nenne ta fita ta kuma sakin wani kukan, tana tausayin kanta da hukuncin Dr. Asmad kuwa yana fita gidan su Hafiz ya yiwa tsinke, har ya karya kwana zai shiga layin ya tuna kila Hafiz din baya gida, don haka sai ya dauko wayarsa ya kira layinsa, ringing biyu ya dauka bayan sun gaisa ne yake tambayarsa Allah yasa yana gida "Eh ina gida ban jima da shigowa ba." "Ok gani nan zuwa." Yana gama faɗin haka ya katse wayar.

Yana fakin motar ya kara kiransa, minti biyu kacal Hafiz ya fito musabaha suka yi kamar yadda suka saba sannan Hafiz ya kalli Asmad da kyau ya ce "mu shiga daga ciki mana abokina?" "A'a ba sai mun shiga ba, sam na rasa jin dadi na gaba daya bana cikin nutsuwa." Da damuwa Asmad ya gama maganar. " Subhanallah! Dr me yake faruwa haka? Mu shiga ciki zai fi." Ciki suka shiga a falo suka yada zango, ruwa mai sanyi Hafiz ya kawo masa bayan ya sha sannan ya soma magana "Wato Hafiz Aneesa da Ameesha suna neman caza min k'wak'walwa, ko kasan duk tsayin lokacin da muka dauka da Aneesa maganin hana daukar ciki take sha?" "Maganin hana daukar ciki?" Da mamaki Hafiz ya yi tambayar. "Sosai kuwa ina tabbatar maka har cikina Aneesa ta zubar wanda take tunanin ban sani ba." "Zubar da ciki?" "Sosai kuwa." Dr ya tabbatar masa.
Chapter 47 · 0% Book details