Sashe 49
Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau dai Dr ya dau aniyar komai rintsi sai ya ga matarsa, domin a halin da yake ciki baya jin zai iya kwana a yau ba tare da ya yi arba da Ameesha ba, don haka cikin sauri ya yi wanka ya shirya cikin kananan kaya jeans da T-shirt kayan sun yi masa kyau sosai sai zuba kamshin turare ya ke. Key ɗin motarsa ya ɗauka sannan ya fita daret gidan Nenne ya nufa yana addu'ar Allah yasa Nenne bata gidan, ko sallama bai yi ba ya shiga falon.
"Hee ya dai?" Nenne ta yi maganar ganin yana niyyar bude kofar. Dan sosa keya ya yi cikin jin kunya kafin ya dawo baya tare da zama kasa kusa da Nenne yana faɗin "ina wuni Nennena?" "Lafiya lau." Ta amsa tana jifansa da kallon tuhuma. Kara kasa ya yi da kai ya ce "don Allah Nenne ki yi hakuri ki barni na ga Ameesha please." "Ka ga Ameesha? Sai yanzu kasan da zamanta?" "Hakuri nake kara baki." "To ban amsa hakuri, tashi ka bani waje." Da fada ta yi maganar. Kin tashi ya yi ya zauna sai magiya ya ke mata amma ta ki ko da kallonsa.
****
Watan cikin Ameesha biyar kenan, har ya fito ya yi mata das da shi gwanin sha'awa, jikinta ya murje sosai ya yi kyau irin ta masu ciki, sanye take cikin doguwar riga wanda suka amshi jikinta ta yi matukar kyau da ka ganta kasan bata da matsala, cikin nutsuwa take takawa har ta fita falon ganin Nenne sai ta shagwaɓe fuska, sam bata kula da wani Dr ba duk kamshin turaren sa ya cika falon hakan bai sa ta yi tunanin shi ne a ciki ba. Don haka sai ta ce
"Nenne ashe kina falo shine ba ki tasheni ba gashi har an gama dadin kowa." "Wayyo mantawa na yi Autar Ummi." Turo baki ta yi tana zama kusa da Nenne. Dr kuwa tunda Ameesha ta fito ya zuba mata ido kamar wani mai son gano wani abu, ya cika da mamakin yadda ta sauya, idan ma ba gizo idonsa ke masa ba sai ya ce ciki ne da ita.
Sosai ya lula duniyar tunani, muryar Nenne ce ta sanya shi juyowa "Tashi Autar Ummi ki ɗauko abinci ba ki ci komai ba fa." "Nenne na koshi ne." "Oya tashi bana son musu je dauko, kuma fa abin da kike so ne na yi maki." Ai da sauri Ameesha ta tashi ta nufi kicin, da kallo Dr ya bi ta kamar wani maye har yana hadiyan miyau ya ke har ta shiga "ba za ka tashi ka tafi bane dare na yi fa." Nenne ta tsinka masa tunani.
"Eh, Nenne yanzu zan tafi dama." Ya dire maganar yana sosa keya. "Mik'ewa tsaye Nenne ta yi tare da nufa hanyar bangaren Bobbo tana faɗin "ka gaida Aneesa." "Za ta ji." Ya bata amsa yana dan sakin murmushi, yana ganin ta shige ya nufi hanyar kicin, Ameesha ta bude firij zata ɗauki C-way Apple sai ji ta yi an rungumota bude baki ta yi tana niyyar kurma ihu, Dr ya yi saurin toshe mata baki ya rada mata cikin kunne "Cutie ni ne fa yi shiru." Wani irin yanayi ta shiga da jin muryar Dr, duk da sai ta soma kokarin kwace kanta, amma sam ta kasa. Ganin ta ɗan nutsu ne ya sanya Dr sanyaya murya ya ce
"Wai Cutie ba za ki koma gidana bane?" Ya yi maganar yana sassauta rikon da ya mata, wasu hawaye ne suka taru a cikin idonta, ganin haka Dr ya girgiza kai alamar kar ta bari su fito. Murya na rawa ta ce "Please baby ka yi hakuri ka yafe min..." Saurin sanya bakinsa ya yi cikin nata, don ba ya son ya ji abin da zata faɗa sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa ya sakin bakin "Kar ki kuma cewa komai Cutie kin ji na yafe maki." Murmushi ta yi har tana kara rungumarsa ta manna masa kiss a kumatu.
Hannu ya kai saman cikinta yana taɓawa a hankali ya ce"Cutie wannan menene?" Cikin kunya ta sadda kai kasa ta kasa furta komai. Ganin yadda ya yi ya sa ya yi sujadar shukur a fili ya bayyana "Alhamdulillah! Cutie dama kina dauke da cikina kika bari har zargi ya shiga tsakanin mu? Me yasa baki fargar da ni ba?" "Baby kai ne ka ki saurarata, kuma ni ma ban san da shi ba sai da Hafiz ya dubani." "Hafiz? Kina nufin yasan da cikin?" "Eh." Ta amsa tana murmushi.
Kara matseta ya yi yana kara jin kaunarta yana shigarsa "I love You Maryerm." "I love You to Dr Asmad." Ameesha ta yi maganar cikin murya mai sanyi. Sun daɗe rungume da juna kafin Dr ya ce "Baby mu je ki ci abinci bana son ki bar min yarinya da yunwa." Daukar ta ya yi daga ita har kayan sam ya manta da wata Nenne a kan dining ya yi mata masauki.
Da kansa ya rika ciyar da ita har ta koshi, bedroom ya kaita lokacin karfe goma har da mintina "Cutie zan tafi ko za ki bini?" Zaro ido ta yi waje ta ce "Ina zan bika baby?" "Gidanmu mana." Girgiza kai ta yi da sauri ta ce "a'a Allah ya kaika lafiya ina nan." "Please mana Cutie." Ya yi maganar yana jawota jikinsa, kafin ta yi wani yunkurin har Dr ya soma fitar ta nutsuwarta domin sako yake bata da zafi zafi.
Sun dau lokaci a haka sannan Dr ya sassauta mata rikon bayan ya samu nutsuwa, kwantar da ita ya yi tare da lulluɓa mata blanket yana fadin "Cutie ki kular min da kanki da babyna ina son ku." "Kar ka damu baby za ka sameni yadda kake so." Kiss ya manna mata a kumatu sannan ya gyara mata sumar kanta da ta barbaje ya ce "Sai da safe." "Amin baby Allah ya kiyaye hanya." Idonta a lumshe ta yi maganar sam sai ta ji bata kaunar tafiyar Dr, tana jin ya buɗe kofa ya fita ta saki ajiyar zuciya tashi ta yi ta nufi toilet sai da ta yi wanka sannan ta gyara jikinta ta kwanta bakinta ɗauke da addu'a.
A daren da Dr ya koma gida yake sanar da Aneesa cikin dake jikin Ameesha, da farko ta shiga shock amma da ta tuna duk abin da ya faru ita ta jawo sai kawai ta taya Dr murna, sai dai ta ji haushin yadda Dr ya mai da maganar cikin Ameesha wani babban lamari, baya magana daya sai ya yi maganar cikin, musamman ya dauketa ya kaita ta duba Ameesha a ranar kam da bakin ciki ta kwana don sai ta ga kamar Meesha na yi mata wani irin kallo na rainin wayau don tana da ciki ga wani uban sangarta da ya fi na baya, Dr da Nenne sai biye mata suke, nadamar abin da ta aikata ne ya shige ta sosai tabbas tasan ta yi kuskure mai tsanani da yanzu tarairayar da ake wa Ameesha a bayan tata yake.
Yau juma'a kuma a yau Dr yake muradin matarsa ta koma gidansa, shi ya sanya tun biyu ya baro office, Allah ya sa Bobbo na gida don haka bayan sun gaisa sai Dr ya yi kasa da kai cikin ladabi ya ce "Bobbo don Allah a taimaka min a bani Ameesha." Harara Nenne ta aika masa da ita. Shi kam Bobbo murmushi ya yi ya ce "haba Asmad ai Ameesha matarka ce don haka ko yanzu kana iya tasa ta gaba ku koma gidanku." "A'a Alhaji sai ta haihu zata koma." Na yi ta yi saurin katse Bobbo. "A yi hakuri dai Hajiya." Sam Nenne ta ki yarda da kyar suka shawo kanta da sharadin duk abin da ya samu Ameesha za su ji a jikinsu. Take Dr ya amsa zuciyarsa cike da farin ciki.
Bobbo da Nenne faɗa sosai da nusiha suka yi masu Ameesha sai aikin kuka take sam bata son rabuwa da Nenne, amma ya zata yi dole ta koma gidan aurenta ko a mota sai sharan hawaye take Dr na aikin lallashi, da kansa ya dauketa bayan ya yi fakin motar su a falo ya yi mata masauki "Cutie KE fa yau amarya ce, bari na samo maki wani abin ki yi wanka kafin na dawo." "A dawo lafiya." Ta yi maganar cike da kulawa. Da farin ciki Dr ya bar bangaren, tana ganin ya fita ta nufi bedroom ɗinsa duk inda ta kai hannu sai ta ji k'ura don haka cikin sauri ta soma tsaftace bangaren nata, duk watannin da ta yi bata gidan yadda ta tafi ta barshi haka ta dawo ta taras. Cikin lokaci ƙalilan har ta gyare ko ina na bangaren ta turare shi da turaruka masu sanyin kamshi, sai dai ta mugun gajiya shi yasa ta zube a falo ta kasa ko da motsin kirki, a haka Dr ya sameta.
Sosai ya cika da mamakin aikin da ta yi, faɗa ya soma mata akan ba ya son tana wahalar da kanta, ban da murmushi babu abin da take, shi ya taimaka mata ta yi wanka ta shirya cikin rigar bacci, shi ma wanka ya yo ba yan ya kammala shiryawa cikin kayan bacci sai ya soma ciyar ta har sai da suka koshi, wanke baki suka yi kafin suka kwanta a wannan rana sun nunawa juna zallar sosai da kewar da suka yi na juna, ba su samu kansu ba sai daf da asbah sannan bacci mai nauyi ya ɗauke su.