← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 54

Sashe 32

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salmah ce ta yi maganar, a dan hasale, d'aya daga cikin wacce suke zaune a wajen.

" Allah ya baku Hak'uri, ni fa bani da matsala, amma na fada maki gaskiya tun wuri ki cire shi a ranki Kar ya zame maki wata wahalar, ni shi yasa nake Alfahari da kaina domin kuwa Allah bai doro min san maza ba ko kadan."

Hango Dr dan fullo tayi yana parking motarsa, taja wani dogon tsaki wanda yasa duk suka maida hankalin su kanta

"Meesha lafiya kike tsaki?"

" wancen dan rainin hankali ne kalleshi fa, yadda yake wani tafiya yana tak'ama, gaskiya Dr bai hadu ba."

Dariyar rainin hankali kawai Meena tayi, don tasan Meesha fad'a kawai ta yi, ko mara ido ya shafa Dr dan fullo yasan, hadadden guy ne, balle kuma masu ido matashi mai jini ajika, gashi kuma billion naira.

" Tashi muje kawai tunda yau bamu da lacca, muje gida daga nan ma zan biya na gaida Ummi."

Meena ta k'arasa maganar tana mik'ewa, su dai sauran shiru sukayi suna mamakin yadda Ameesha take raina Dr dan fullo.

Najeeb dai na zaune a kofar school har sha biyu da rabi, baiga alamar wata Ameesha zata fito ba, don haka sai kawai yaja motarsa da niyyar anjima zai kai mata ziyara gidan su.

************************************

Bobbo ya gyara zama tare da maida hankalin sa kan Nanne dake zaune kusa da shi.

"Yawwa kina jina ko mun gama komai da Alhaji Bashir, sannan su Baffa ma sun shiga maganar, komai anyi na yadda auren zai tafi babu gargada."

Nanne ta dubi mai gidan nata, cikin sakin fuska da kulawa tace

" Masha Allah Ubangiji ya tabbatar da Alhairi, sai dai har yanzu baka sanar dani wa ka zab'awa Asmad din matsayin matar aure ba."

Duk da taji ya ambaci Sunan Alhaji Bashir, amma tana son gasgata hasashen ta.

" yanzu zaki sani kuma zakiyi farin ciki da zabina ba kowa ba ce illa.......... "

_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

``` sadaukarwa ga KHADIJA S MUHAMMAD my Cittah```

*7*

Nanne ɗan murmushi ta saki, tana mamakin yadda mai gidan nata yake farin cikin sanar mata da maganar, ita ma nan take taji ta kosa ya sanar mata zabin da akayi wa Asmad din ta.

"Aneesa na masa zaɓi, don nasan ita ce kadai zata iya zama da shi cikin mutunci."

Kara gyara zama Nanne tayi, da jin zaɓin da aka yiwa Asmad, wani kyakkyawan murmushi ta saki, wannan shi ne burin da ta jima da shi a ranta, sai dai tayi shiru ne don kar ta shiga hakkin su, sai ga shi mijinta mai dogon tunani, shima ya yi irin nata nazarin."

Murmushi ta kuma sakewa a karo na biyu, wannan karon bakinta yak'i rufuwa, cikin jin dadi tace

" Allah ya sa Albarka cikin wannan haɗin, Ubangiji ya kade fitina, Allah ya basu zama lafiya da zuri'a tagari."

" Allahumma amin, Hajiyar Asmad ga dukkan alamun dai wannan maganar ta yau tayi maki daɗi?"

" Sosai kuwa Alhaji, ai wannan abin farin ciki ne, Allah ya tabbatar da Alhairin sa."

Haka suka ci gaba da hiran su, cikin jin daɗi.

*************************

Ameesha ce zaune cikin falon su, waya ce a hannunta da alama game takeyi ko chat, Haidar ne wato Yayanta wanda take bi mawa ya shigo falon da sallama.

Tayi saurin ɗago da kai ta ce

"Yawwa Ya Haidar, wallahi tun ɗazun zaman jiran ka nake."

Harara ya banka mata cikin daure fuska, Allah ya yo Haidar da iya haɗa fuska, baya k'aunar raini ko kaɗan, balle kuma Ameesha da ta rawan kai.
" Kai Ya Haidar daga magana sai ka soma min harara to na fasa."

Zama ya yi yana faɗin
" Kin yiwa kanki, tashi ki kawo min abinci."

"Kai don Allah nifa game nakeyi, kuma ina tashi zasu cinye ni."

A shagwabe Ameesha ta k'arasa maganar.

"Ba zaki tashi ba kenan?"

Ganin mugun kallon da yake watsa mata yasa ta mike, komai sai da ta haɗo masa sannan ta aje masa a gaba, komawa tayi kan kujera ta lafe, cike da jin takaicin yadda Haidar din ya mata.

" Yawwa k'anwata kin san me? Zo kiji? "

Haidar ne ya yi maganar, wannan karon fuskar sa a sake, kamar ba shi ba.

Banza ta masa tare da ci gaba da buga game ɗin.

" Meesha my lovely sister zo kiji please? "

Kallon inda yake ta yi tare da turo k'aramin bakinta ta ce

" Ba yanzu ka gama min masifa ba, kuma kaki tsayawa kaji abin da zan ce."

" Oh! Sorry my sister, faɗi inji mai kike so? "

Murmushi ta saki ta ce

" Dama so nake in ce maka laptop ɗina ya lalace, jiya da zan dawo daga school."

" Yanzu ya kike son a yi?"

" Abba nake jira ya dawo, sai in amshi kudi sai ka sayo min sabo, tunda wancen ya tashi aiki."

" Je ki ɗauko." ya yi maganar yana aje plet ɗin.

Ta mike da zumar tafiya, sai taji sallama a kofar falo, amsawa ta yi tare da tambayar "waye? Dai dai sanda ta isa kofar.

Ganin mai bawa fulawar gidan ruwa yasa ta ce

" Lafiya kuwa? "

" Lafiya lau Hajiya dama bak'one ya ce a kira ki."

" Bak'o?"

Tayi tambayar tana kallon wanda ke tsaye gabanta.

"Eh Hajiya."

"To ina zuwa."

Shi ne iyakar abin da Ameesha ta faɗa, mamaki sosai ya rufeta, ita ai bata yi magana da wani akan yazo gidan suba "to waye wannan" ta yiwa kanta tambayar da babu amsa.

Bedroom ɗin Ummi ta nufa, don ko takan Haidar bata yi ba, akan sallaya ta samu Ummin, zama tayi gabanta tare da rika hannunta ta ce

" Ummi kinji wai wani yazo nema na? "

Shafa Addu'an Ummi ta yi ta ce" To ya baki tafi ba?

" To ni ai Ummi ban San shi ba, kuma ai da nasan da zuwan shi zai kira wayata."

Ameesha ta yi maganar ranta a ɗan ba ce.

"Haba Ummin Abba ba'a haka, tashi ki ɗauko gyalen ki, kije kiga ko waye daga nan ki hada masa abin sha kin ji ko?"

Daga kai Meesha ta yi, badon ranta ya so ba, amma tunda Ummi ta bata dama bari taje, ji take kamar ba ita ba, tunda take bata taɓa zuwa harabar gidan su da sunanan tsayuwa da wani ba.

Amma yau gashi wani ya tako har gidan su, tana jinjinawa ko waye wannan da kokari. Ko ruwa bata ɗauka ba, ta nufi wajen dama jikinta fes yake, fuskar ta shafe yake da powder.

Cikin nutsuwa ta ke tafiyar, jikinta ko ina iska ke kada ta, tunda nesa ta soma shakar daddar turaren sa, tsaye yake ya jingina bayan sa jikin motar, waya ce a hannunsa da alama waya yake, can nesa da shi ta tsaya, tana kallon sa.

Bai san ta iso ba har sai da yaji kamshin turarenta ya cika wajen, a hankali cikin nutsuwa ya juyo da fuskar sa zuwa gareta, fuskar nan tashi ɗauke da murmushi

" Barka da zuwa Gimbiya sarautar mata."

Shi ne abin da ya faɗa, yana kallon Ameesha, dan tabe baki tayi cikin jin kai ta ce

" bawan Allah ban gane ka ba, daga ina kuma wajen wa kazo? "

Murmushin dai ya kuma yi ya ce

" Haba Ameesha baki dai gane niba, da farko dai sunana *Najeeb Mansur* dan Alhaji Mansur abokin Abban ki."

Zaro ido tayi cike da mamaki ta ce

" oh! Sannu da zuwa Najeeb ya Alhaji da Momi? "

Ameesha ta tambaya fuskar ta ba yabo ba fallasa.

" Lafiya lau Ameesha, zakiyi mamakin gani na a gidan ku ko? To wannan ba'a bin mamaki bane domin kuwa mai son ɗan tsuntsu shi ke binsa da jifa, gaskiyar magana dai nazo maki da wata magana ne mai muhimmanci, sai dai tunda baki san da zuwa na ba, ina son ki bani lokacin da zan dawo mu tattauna."

Kallon sa take tunda ya soma magana, Najeeb dai kyakkyawa ne son kowa kin wanda ya rasa, da ganin sa kasan da nutsuwa a tattare da shi, sannan kalaman da ya yi amfani da su wajen yi mata magana sunyi mata dadi. Amma sai ta basar tace

" No nikam bani da wani time, don kullum ina school yau ma kayi sa'a ne ka iskoni a gidan."

" Haba princess Meesha ki taimaka, matukar baki bani dama na fayyace maki abin da ke raina ba, tom zan iya shiga wani hali, kiyi hak'uri ki bani dama? "

Da muryan tausayi ya k'arasa maganar.

Yadda ya yi maganar har ya kusan bata dariya ya yi, amma sai tayi saurin fuskewa ta ce

" kana iya dawowa nan da two weeks."

Zaro ido ya yi a ɗan firgice ya ce

" Haba princess ina laifin two days, wallahi two weeks ya min yawa."

Ta gaji da jin maganar, tana son ko mawa cikin gida don haka ta ce

" to one week ya yi? Don ina da test a school, a cikin week din nan."

"Allah ya kaimu amma ba haka naso ba, sai dai kuma tunda princess ce ta zaba bani da yadda zanyi."

Har ta kama hanya zata tafi ya ce

" princess baki bani phone number ɗin ki ba please ki bani? "

Wayarsa ta amsa tasa masa numbers ɗinta sannan ta wuce. Shi kuma a nashi ɓangaren wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, da ya gama da wannan, don yasan tunda ya samu number ɗinta ya yi mai wuya.

Maimakon ya yi farin ciki da ya samu ta ɗan Amince da shi, sai takaici ya rufe shi, don yasan abin da zai aikata ba abin kirki bane, tunda yaudara ce zaiyi, takaici sosai da tausayin ta suka rufe shi.

A gefe ɗaya kuma yana yaba kyaunta da nutsuwarta, tabbas da a ce bashi da Rufaidat tofa zai iya auren ta, sai dai shi yanzu Rufaida kawai yake kallo a matsayin mace.

Ko da yake jan motar haka ya yi ta tunanin abin da zai aikata, Allah ya sani umurni zai cika ba yin kansa bane.

*********************************
Chapter 32 · 0% Book details