← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 54

Sashe 21

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dr na buɗewa Ameesha ta faɗa jikinsa tare da kamkame shi, cikin siririyar murya ta ke faɗin "baby sannu da dawowa." Bai amsa ba sai k'ok'arin yaki ce ta daga jikinsa ya fara, ita kuma ta ki sakin sai ma kukan sangarta da da fara yi masa, sam ya kasa tankwara zuciyarsa akan kar ya sauka daga fushin da yake da ita, daukarta cak! Ya yi ya k'arasa shiga falon da ita. Sam Ameesha ta ki barin kukan kuma ta ki dagawa daga jikinsa, shafa sumar kanta ya soma yi cikin wani irin salo ya kasa magana sai zuwa can ya ce "haba Cutie kukan ya isa haka kar ki bata min kwalliya ga yi ko gani ban yi ba." Da taushin murya ya yi maganar. Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyarta ta kara lafewa a kirjinsa tana ci gaba da shashsheka. "Ba na ce kukan ya isa ba?" Wannan karon adan hasale ya yi maganar.

"Ni dai ba zan yi shiru ba sai ka faɗa min laifin da na yi maka kake yin fushi da ni?" Da shagwaɓaɓɓiyar murya ta yi maganar. Kiss ya yi mata a kumatu ya ce "wannan maganar ya wuce tuni na bar yin fushi dake, domin ba zan iya ba duk kuwa da girman laifinki." "Laifi na wallahi ban san na yi maka laifi ba baby ka yi hakuri ka yafe min in sha Allah bazan kara ba." "Kin yi min laifi Cutie wanda yasa har na kasa ɓoye fushi na." "To ka yi hakuri ka yafen." "Na hakura Allah ya yafe mu baki daya." Amin ta amsa tana ɓalle masa botirar rigarsa, kwashe kayan ta yi ta kai masa bedroom sannan ta haɗa masa ruwan wanka, ita ta taimaka masa ya yi wankan ya shirya sannan suka fita falo.

Ameesha da kanta ta rika ciyar da Dr har ya koshi, kwashe kayan ta yi takai kicin sannan suka koma kan three sitter, soyayyar su su ke Ameesha ta kuma narkewa a jikin Dr ta yi kasa da murya ta ce "baby wai wane laifi na yi maka da ka kira shi mafi muni? Ina son sanin laifi na domin gujewa sake aikata maka irinsa nan gaba." Shafa kanta Dr ya yi cikin soyayyar ta da ta yi masa yawa ya ce "ki bar tuna min Cutie wannan fa ya wuce kuma bana fatan na kara kamaki da makamancin sa, a wajen ki ba babban laifi bane domin ban san manufar ki ta yin haka ba, amma ni a wajena babban laifi ne Maryerm." Ya ɗan takata da maganar sa, jin ya yi shiru sai ta ɗago kai ta kalleshi ta ce "in sha Allah bani kumawa amma ina son jin sunan laifin." "Hmmmm! Dr ya saki ajiyar zuciya ya ce "Maryerm kina shan maganin hana daukar ciki saboda karki wahala ko?" Wani irin zabura Ameesha ta yi murya na rawa ta ce "Maganin hana daukar ciki baby?"

"Yes Ameesha da idona na gansu ranar da kanki ke ciwo na je dauko maki magani ." Ya dakata da maganar yana kallon Ameesha, saurin mayar da hawayen ta ta yi sai dai duk da haka mamakin maganar Dr bai bar fuskarta ba, ta dai kasa magana don bata da kalmar kare kanta tunda ya gani da idonsa kuma cikin kayanta.

Ya zama dole ta amsa laifin duk da dai ba ita ta aikata ba, hasalima bata taɓa koda tunanin shan irin maganin ba, Wasu hawaye masu zafi suka sauko saman fuskarta muryarta na rawa ta ce "Na yi kuskure in sha Allah makamancin haka ba zai kuma faruwa ba ka yafe min." Kara rungumar ta ya yi yana hura mata iska a kunne ya ce "ya isa haka kukan, kar ki kara sha." Da kyar ya lallasheta ta yi shiru har bacci ya kwashe ta anan a jikinsa. Shiru Dr ya yi yana kallon yadda Ameesha ke saukar da numfashi duk da baccin ba na daɗi ba ne, amma ta yi kyau a cikin baccin. Sam baya kaunar damuwarta balle akai ga yin kuka.

Sun ci gaba da gudanar da rayuwar su, yau saura kwana ɗaya sunan Meena tun safe Meesha ta soma shiri domin kwana zata yi a gidan, in da Allah ya taimaketa ba ita keda Dr ba, karfe goma ta kammala shirinta ta dauki karamin kit ɗinta da ta sanya kaya kala uku a ciki sai kayan kwalliya, Number din Dr ta soma laluba don ta sanar masa ta shirya. Dr dake asbiti ya tabbatar mata da ga shi nan zuwa nan da mintina ashirin.

Bai wani jima ba ya iso, ganin kit gabanta ya sa shi zaro ido da mamaki "Cutie wannan kayan fa?" "Da su zan tafi." Ta bashi amsa cikin shagwaɓa. "Kuma har haka? Ina laifin kala ɗaya gobe zan zo ɗaukar ki fa?" "Gobe fa baby? Ba sai jibi ba?" "A'a ki dawo gobe plea.." Bata bari ya gama rufe baki ba ta yi saurin sanya bakinta cikin nashi tana yi masa wani shu'umin kallo mai kashewa lafiyayyen namiji jiki, sun dau kusan minti goma a haka kafin ta fara k'ok'arin zare bakinta daga na shi, shi kuma Dr ya ce bai san wannan ba bai barta ba sai da ya samu nutsuwa don kansa. Su ka shiga mai da numfashi jiki a mace Dr ya mike bai iya cewa komai ba sai daukar mata kit da ya yi ya kai mota sannan ya ce ta fito su je. basu nufi mota ba sai suka nufi bangaren Aneesa kusan a tare suka yi sallama. Aneesa dake zaune a falon da kyar ta iya amsawa tana jifan Ameesha da wani irin kallo, ita kam murmushi ta yi tana zama a kasa kusa da kafar Dr.

Dr ya kai dubansa ga Aneesa dake ci gaba da danna waya ya ce "Fatan kin shirya?" Ya mutsa fuska ta yi ta ce "Hamman na ce maka bani da lafiya fa, ba zan iya zuwa ko ina ba." Ran Dr ya ɗan ɓaci da maganar Aneesa ya aika mata wani kallo da yasa ta sunkuyar da kai kasa, ya ce "minti biyar na baki ki fito ina jiran ki." Daga haka ya mike. Ameesha ta bi bayan sa, da yake ranar zai koma ɗakin Aneesa sai Ameesha ta zauna a gaba. Cikin turo baki Aneesa ta isa wajen bata yiwa kowa magana ba ta shiga motar sannan Dr ya ja suka tafi. Bai zame ko ina da su ba sai gidan su Ameesha farin ciki sosai ya kama Ameesha, a parking space ya yi parking suka sanya Dr a tsakiya part din Meena suka shiga, har yan'uwanta sun fara zuwa Ameesha ta shiga cikin bedroom ɗin tana sanarwa da Meena zuwansu tare da Dr da Aneesa, cikin farin ciki ta fito da jaririn a hannu kamar kullum Dr ta mik'awa Yaron sannan suka gaisa, rungumar yaron Dr ya yi baya kaunar rabuwa da yaro, haka Aneesa ta ji zallar soyayyar Yaron ta ji tana son itama ta samu nata dan.

Sakin fuska ta yi sosai akai ta harkar arziki, domin Dr nan ya barsu da niyyar idan ya dawo zai dauketa. Ummi da Abba sun ji dadin yadda Aneesa ta zo barka kuma har ta saki jiki hakan ya nuna suna zaman lafiya, karfe biyu Dr ya zo ya ɗauki Aneesa ya yin da aka bar Ameesha, ba su wuce gida ba sai da suka biya gidan Nenne a can suka k'arasa wuni sai yamma suka koma.

Ameesha kam bayan tafiyar su Dr sai ta kwashi kayanta ta koma bangaren Ummi, Abba dake zaune yana karanta jarida ya bi Ameesha da kallo ganinta da kaya. "Uwata wannan kayan fa?" Turo baki ta yi ta ce "Kaya na ne Abba." "Shi ne kuma kika shiryo a cikin akwati?" "Eh! Abba ai kwana biyu zan yi." Wannan karon da sakin fuska ta yi maganar. "A'a uwata ki koma ɗakin mijinki gobe tunda ba wani abu za'a yi ba idan an gama sunan." "Abba ai shi ya ce na yi kwana biyu ka tambaye shi ka ji." "Ko shi ya ce gobe zaki koma." "Don Allah Abba ka yi hakuri wallahi shi ya bani kwana biyu Please Abbana." Ameesha ta k'arasa maganar tare da hawaye. "Je ki zamu yi magana da Asmad ɗin wannan ai shashanci ne." Ita dai tunda taga Abba ya barta da sauri ta haura sama, fes ta samu ɗakin kamar akwai mutum a ciki sai da ya gama zagaye dakin sannan ta shirya kayanta cikin wardrop, kwanciya ta yi tana tuna rayuwar ta na baya ga dimbin kewar Dr haka ta kwana, washegarin suna Yaro ya ci sunan Alhaji Abubakar suna masa lakabi da *(Sahal)* Aneesa da Nenne ma sun zo haka Ni'eema da mijinta Muhammad da yaransu Irfan da Yumna, ba su bar gidan ba sai daf da magriba.

Washegarin suna sai bayan magriba Dr ya zo ya ɗauki Ameesha, domin ranar ta amshi girki, ji ta yi kamar karta bar gidan su, domin a kwanaki biyu da ta yi ta ji bata son rabuwa da gida. A gajiye ta k'arasa falon a kan kujera ta zube tana faɗin wash! Kallonta Dr ya yi yana faɗin "Autar Ummi kin gaji kenan?" "Allah baby na gaji sosai." Ki je ki watsa ruwa sai na samo mana abinci."
Chapter 21 · 0% Book details