← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 54

Sashe 43

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amin." Dr ya amsa yana mikawa Ummi takardar sallama domin Abba ya fita daga dakin ya ce zuciyarsa zata iya bugawa matukar dai yana kallon Ameesha a irin wannan yanayin, ko a jiya da kyar ya kawo safe don yadda zuciyarsa ke masa wani irin zafi. Ummi kam amsa ta yi tana masa godiya, lokacin shayi ya ɗan huce.

"Auta amsa ki sha! Tayi maganar tana mika mata cup din amma fir taki amsa, juyin duniya amma ta ki, Abdul ne ya je ya kira Dr. Tare suka dawo da shi, yana zuwa ya amsa ya kai bakin sa sannan ya mika mata yana faɗin
.
"Amsa Princess ki sha kin ji?" Babu musu ta amsa tare da kaiwa baki kamar yadda Asmad ɗin ya ce.

Kafin ta gama sha har sun gama kwashe kayan su daga ɗakin.

Wajen tafiya gida ma da kyar aka lallaɓa ta, don tirjewa ta yi ita fa adole babu inda zata je sai tare da Asmad, to shi dinma yana alhinin rabuwa da ita, sai dai bai nuna ba don karda su yi tunanin wani abun.

"Please Dr ko zaka taimaka mana ne ka kasance gida?" Muryar ya Jaheed kenan.

"No babu damuwa, domin ni ma gida zan ta fi." Dr ya ba shi amsa.

"Mun gode sosai Allah ya bar zumunci." Ya ida maganar yana nufa inda su Ummi su ke.

"Ummi Dr ya ce zai kai ta gidan tunda kinga fa bata yadda da kowa sai shi."

"Kar ka damu mudai mu yi fatan Allah ya bata lafiya." Ummi ta ida maganar tana kamo hannunta. Fisge hannun ta yi. Ganin haka sai Dr ya iso wajen ya kamo hannunta a hankali suka nufi inda motarsa ya ke.

Suma su Ya Jaheed suka nufi mota, babu wani bata lokaci suka isa gida har falo ya kaita, lokacin Meena ta gama haɗa break ɗin da za'a kai Asibiti, tana ganin Ameesha ta yi saurin aje flask ɗin hannunta tana faɗin

" A'a Meesha har kun dawo? Dr ina kwana"

Murmushi ya yi itama Meesha ta yi murmushin ya ce

" Kin san da yake bata da wani ciwo shi yasa."

"To sannu Dr da k'ok'ari mun gode sosai." Dai dai da shigowar su Abba.

Kallon agogon hannun sa ya yi ya ce " Ni kam bari na tafi gida, Ummi kusata ta yi wanka don ta ji daɗin jikinta. Amma sai dai a sami wanda zai koya mata"

Da sauri Ameesha ta fadi yadda ya ce. Dan murmushi Ummi ta yi tana kara godiya ga Dr sannan taja hannunta zuwa bedroom ɗinta tana faɗin

"Mu je kiyi wanka yana jiran ki a falo." Kamar ta san abin Ummi ta ke nufi sai ko ta ci gaba da tafiya.

Yana ganin sun tafi ya yi sallama da su Ya Jaheed sannan ya nufi fita. Ko da ya shiga lokacin goma saura don haka gidansu ya nufa, domin dai yasan Aneesa bata tashi ba don haka gara kawai ya tafi can ɗin, dama jiya bai samu zuwa ba.

*************************

Da sallama ya shiga falon Nenne da Bobbo ne suke zaune a falon suna hira, da alama yau Bobbo ba zai fita da wuri ba.

(Ha leddi o rongini o hofni saro mako.) Har kasa ya tsuguna yana gaida iyayensa.

(Der fertare be notani moo.) Cikin sakin fuska suka amsa masa.

(" Nanne nyami mo noi Aneesa waldi.") "Ya Aneesa ta kwana?" Nenne ta yi tambayar.

("O jamo kolon. Kenya minani odon wi'a o waran hamon.") "Lafiya lau ta kwana, jiya na ji tana faɗin zata zo nan gidan."

(Usoko! Allah waddu mo jam.") "Madallah! Allah ya kawo ta lafiya."

("Ameen" o noti Nenne welo minanta fa!) "Ameen ya amsa. " Ummi yunwa nake ji fa!

("To hami hauta ne nyamdu man gam minin maa jotta min hasiti.") "To bari na hada maka, muma da yake yanzu muka gama yin break ɗin.

("Haba Asmad noi a wurtata sare a hasiti? Bobbo wolwi der mettam beram.") "Haba Asmad ya zaka fito gida ba tare da ka tsaya ka yi break?" Bobbo ya yi maganar cikin ɗan faɗa faɗa.

("A'a Bobbo daga jamdi jego mi wurti sare gam mid'o mari nyoudo, mi yahi milari noi o waldi, den mi yalti en hofni dira wali didi mi warai.") "A'a Bobbo ai tun shida na fita don ina da wata mara lafiya, na je duba jikin ne shi ne na biyo nan mu gaisa tunda jiya ban leko ba."

("Towo jotta minanai hala, mi tamma daga sare a wani a darai a hasiti, Allah wasu barka.") "Aiho yanzu na ji magana, ai nayi tunanin daga gida kake shi ne baka tsaya ka karya ba, Allah ya yi albarka."

( Hokkilo don wali Asmad nyamata kasitari mako ha o timmini, o warti falo ha Nenne en wonii.) Cike da kwanciyar hankali Asmad ya ke yin break ɗinsa har saida ya kammala, falon ya dawo inda su Nenne suke

(" Nenne mi hiran sare.") "Nennezan na k'arasa gida!

("Allah hore jam, hofnu Aneesa.") "To Allah ya kaika lafiya ka gaida Aneesa."

("O nanan insha Allah." Asmad jabi moo.) "Za ta ji insha Allah." Asmad ya bata amsa yana fita.

Lokacin da ya je gida a falo ya iske Aneesa da sauri ta tashi tana faɗin

"Hamma daga ina kake?

"Daga Asibiti nake don akwai mara lafiyar da na je dubawa." Ya bata amsa yana zama a kujerar da ke kusa da ita.

Gyada kai kawai ta yi, haka kawai ta ji sam bata so ya fita ɗin ba, domin ita har ga Allah tana tsoron ganin sa da yammata balle kuma ya ce zai kara aure, bata k'aunar ganin wannan lokacin.

"Aneesa tashi ki haɗa min ruwan wanka, kin yi break?"

Da kai ta amsa masa don dai jinta ya yi sanyi.

"Ok mu je in yi wanka, kema ki yi ko kin fasa zuwa gidan su Nenne ɗin?

"Lah! Hamma zan je, naga baka yi min maganar ba ne."

"Ok to ai yanzu na yi maki sai ki shirya har na faɗawa Nenne zuwanki."

Daɗi ya rufe Aneesa da jin zata je gidan Nenne, aiko cikin saura ta shirya, shi ma a lokacin Asmad ya gama shirin sa jerawa suka yi har mota.

*Gidan Alhaji Mansur*

"Kai Najeeb kana jina? Bai jira amsar da Najeeb ɗin zai bashi ba sai ya daura a maganarsa.

"Kana jina ko! Kai aiwatar da abu daya da nake so, sai abu na biyu, ina tunanin baka manta da maganar babu aure tsakanin ka da wancen mahaukaciyar yariyar ba?"

"Abba wacece mahaukaciya?"

"Kai bana son shashanci Wancen yarinyar da bata da wani aiki sai SANGARTA. Uban wa ya sani ko haɗa baki suka yi da likitan har ya ce ta samu ciwon mantuwa, don nasan halin Taheer tsaf ba zai bari a ce Yar shi ta haukace ba nikam nasan hauka take yi sam bata aikin masu hankali."

"Abba yanzu baka tausayin halin da Ameesha ta samu kanta? Wallahi duk wani mai imani in har yaga yadda Ameesha ta koma zai tausa..."

Tun kun kafin ya gama rufe baki Alhaji Mansur ya sauke masa wasu mahaukatan mari har biyu, wanda suka yi mugun shigan Najeeb.

_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*Saboda yadda ki ke son wannan Nobel din yasa na baki kyautar wannan page din na yau, MARYAM BINTU hakika kin cancanci fiye da haka, amma ki yi haquri da wannan, fatana Allah albarkaci rayuwarki Ubangiji ya rabani da sharrin makiya, YAR MUTAN RANO tana k'aunar ki har cikin ranta.*

```Masu korafin in bude groups, don Allah ku yi hakuri ba sai na buɗe group daban ba, a kawai groups na yan'uwana da yawa, irin su UMMYN YUSRAH NOVEL, MARYAM MUKHTAR FAN GROUP, da dai sauransu duk ina post a ciki, ba sai na buɗe ba, ina godiya da shawarwari Allah ya barmu da k'aunar juna.```

*19*
Sadda kai k'asa Najeeb ya yi, cikin zuciyarsa yana mai tsantsan jin takaici da halin mahaifinsa. Muryar Alhaji Mansur ya ji yana faɗin "tashi ka bani waje shashashan banza kawai, kuma dole ka yi yadda na ke so , ko kuma wallahi ranka ya yi mummunan ɓaci."

Jiki a sanyaye ya mike bai nufi inda sashin sa yake ba, sai ya nufi wajen motarsa ya ɗauka, cikin nutsuwa ya tashi motar bai zame ko ina ba sai gidan Alhaji Taheer. Ya yi parking sannan ya k'arasa cikin gidan.

A babban falo ya samu su Abba zaune suna hira da Ummi, gefe guda kuma Ameesha ce ke kwance akan three sitter. Cikin sakin fuska Abba ya amsa masa sallamar da ya yi.

Tsugunawa ya yi har kasa ya ce

"Ina kwana Abba ya mai jiki?"

"Lafiya lau Najeeb mai jiki ta ji sauki, ya su Alhajin?"

"Yana lafiya ya ce a gaida ku!

"Muna amsawa."

Kansa ya kuma saddawa da alama magana ya ke son yi. Abba ya fahimci haka

"Kamar kana son yin magana ko?" Alhaji Taheer ya tambaya.

"Eh! Abba. Ya bashi amsa

"Ok ina jinka." Ya ida maganar yana maida hankalinsa shi.

"Ehm uum! Dama kan maganar Ameesha ne, Abba don Allah karka fasa bani ita, wallahi zan iya aurenta a ko wane hali take."

Murmushi Abba ya yi cikin jin daɗi da maganar Najeeb ɗin, don har cikin zuciyarsa yana tunanin yadda lamarin zai kasance, musamman daga halin da Ameesha ta samu kanta a ci, amma yanzu Alhamdulillah tunda ga Najeeb yana jaddada masa son da ya kewa Ameesha ɗin.

"Haba karka damu da wannan insha Allah Ameesha taka ce, bata da wani miji da ya wuce kai."

"Na gode Abba." Ya yi furucin cike da jin dadi.

Kallon agogon hannunsa ya yi tare da mik'ewa, don tuni Ummi ta bar falon

"Najeeb zan fita! In ka koma ka gaida su Hajiyar." Ya kai karshen maganar yana fita.

Shi kuma matsawa kusa da ita ya yi ya ce

"Meesha ya jikin?"
Chapter 43 · 0% Book details