← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 54

Sashe 37

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ikon Allah ba'afi minti goma ba sai zafin jikin ya ragu, sai a sannan ya samu dan nutsuwa har ya fita, yana fita Ummi ta yi saurin ta sowa tana tambayar sa jikin Ameesha.

Kallon Ummi ya yi take ya gane ita din ce mahaifiyar Ameesha, don muguwar kamar da su ka yi. Murmushi ya saki mai kwantar wa da mutum hankali ya ce

" Karki damu Hajiya ta samu sauki don yanzu ma bacci takeyi, Kuma zazzabin ya sauka, insha Allah sanda zata farka zata koma normal, gajiyar da tayi na aikace aikace ne wanda bata sababa shi ya haifar mata da zazzabin . "

(Hmmm abin mamaki su Ameesha *SANGARTA* na damunki, daga aikin biki sai ciwo? Kodai kodai damuwar wani akasa a zuciya? )

Bayanin da ya mata ne yasa hankalin ta dan kwanciya, sai a lokacin ta samu damar kiran Alhaji Taheer tana sanar masa da rashin lafiyar Ameeshan. Sosai hankalin sa ya tashi don haka cikin sauri ya dauki hanyar hanyar ko mawa kano don yana garin Abuja, jirgi ma yabi don yana sauri.

Ameesha yar gata cikin lokaci kalilan har asbiti ya cika da mutane, Najeeb ma ya zo hankalin sa a tashe, domin fa yanzu Allah ya jarabci Najeeb da mugun son Ameesha, wanda har yake mamakin yadda son nata ya shige shi sosai.

Sai bayan la'asar ta farka, lokacin Alhaji Taheer ya daɗe da bayyana a asbitin, koda ta farka tuni zazzabin ya sauka, amma ganin Alhaji Taheer sai ta wani kuma narkewa.

" Sannu Uwata ina ke maki ciwo? Me kike so? Mai zaki ci? "

Alhaji Taheer ya ke jero mata wandinnan tambayoyin.

Girgiza kai ta yi tace

" Ni dai Abba bani son komai, bacci nakeji kawai."

" Haba Uwata ki daure ki ci wani abun mana? "

Allah ya yo Ameesha bata son jan zan ce, don haka sai ta ce " To Abba."

Asmad shigowarsa kenan ya ji Abban Ameesha na lalla6ata, a zuciyar sa ya jinjina girman son da mahaifan ta suke mata. "lallai dole ki yi *SANGARTA* har rashin kunya ta samu wajen zama.

" Babyn Ummi ya k'arfin jiki? "

Najeeb ne ya ke magana idon sa akan Ameesha.

Murmushi ta saki tare da lumshe ido, ta buɗe ta ɗaura idon ta kan fuskar Najeeb ɗin a hankali ta furta

" Jiki da sauki."

" Allah ya k'ara sauki."

Ya fada.

Wani takaici ne ya rufe Asmad, ganin yadda ta saki jiki da Najeeb ɗin, har take masa murmushin da ba kowa ya kamata ya gani ba. Don haka cikin sauri tun kafin zuciyar sa ta buga kawai sai ya masu sallama.

Don duk wani abu da take buk'ata ya gama, sai dai bai gaji da ganin kyakkyawan fuskar ta ba, amma sakamakon ganin Najeeb sai da ya yi dana sanin zuwan sa asbitin, duk sai yaji ya tsani Najeeb ɗin.

Asmad ne zaune da tare da Nenne da Bobbo a babban falon gidan su, hira su ke yi cikin kwanciyar hankali, Bobbo ne ya kira shi don su tattauna wani muhimmin abu, al'adar su sai sun fara hira kafin ya gabatar da abin da ya hada su.

To yau ma kamar kullum suna zaune, a babban falon gidan , domin kuwa tuni gidan ya soma amsar baki daga waje daban daban, kasancewar yau saura kwana biyu ɗaura aure, Yan Adamawa tuni suka bayyana, muskutawa ya yi tare da gyara zama, sannan ya kai hannu ya bude wata jaka dake kusa da shi.

Wasu takardu ya kwaso cikin jakar tare da mik'awa Asmad ɗin, hannu biyu yasa tare da amsa cikin rashin fahimta

" Buɗe ka gani Asmad, yau kam alkawarin da na ɗauka Allah ya bani iko na cika shi."

Buɗe takardun ya fara cikin wani irin mamaki ya mik'e tsaye baki na rawa ya ce

" Bobbo na ga takardan asibiti ne?"

" Eh Asmad! Sune takardun asibitin dana gina maka ba tare da saninka ba , dama na ce sai lokacin da za'a ɗaura aurenka zaka san da shi."

" Masha Allah! Ina matuk'ar godiya Bobbona, Allah ya saka maka da Alhairi ."

Farin ciki ya cika Nenne da irin kyautar da mai gidanta ya ba ɗan nasu guda ɗaya da Allah ya basu.

Sai sanyawa abin albarka take yi

Farin ciki hana shi magana ya yi, sai kallon Bobbo ya ke, wayar sa ce ta dawo da shi daga tunanin da ya lula number ɗin da ya gani ne yasa shi ɗauka tare da karawa a kunne, cikin zuciyarsa faɗi ya ke yar matsala

Saurin fita daga falon ya yi yana faɗin me...?"

_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*
*13*

" Lafiya kuwa?"

Daga can ɓangaren Aneesa ta ce

" Hamma ina yini?"

"Lafiya."

Ya yi maganar fuskar sa ba yabo ba fallasa.

" Ehm daman..." Sai kuma ta yi shiru.

" Aneesa ina jinki akwai matsala ne?"

Dan murmushi ta yi ta ce

"Dama so nake na ce muna da buk'atar kuɗi, wanda zamu yi amfani da shi."

"Ok"

Shi ne kaɗai abin da Asmad ya faɗa ya katse kiran.

Aneesa kuwa sororo ta tsaya da waya a hannu, tana mamakin Asmad ɗin , sai kuma ta saki murmushi da ta tuna kwana kaɗan ya rage su kasance matsayin miji da mata, tana alfaharin kasance wa da Asmad a matsayin miji.

Da wannan tunanin ɓacin ran da ya ɗan sa mata ya gushe.

Asmad kuwa falon ya koma inda iyayen sa suke, zama ya yi tare da kallon Bobbo ya ce

" To Bobbo yau she za'a buɗe asibitin?"

Asmad ya yi tambayar yana kallon Alhaji Abubakar.

" Ranar ɗaurin Aure ina kamar zai fi."

Bobbo ya bashi amsa.

" A'a ko dai washe gari, don kasan fa kafin a dawo gida za'a daɗe a hanya."

Nenne ta faɗa.

" Tom a barshi haka ɗin, tunda muna da buk'atar mutane."

Allah ya sa albarka ya taimaka, Ubangiji ya ida nufi ka kula da kyau Asmad ka taimaki bayin Allah, domin kaima Allah ya taimake ka ."

"Insha Allah Nennena zanyi yadda kika umurta, kudai ci gaba da yi mana addu'a."

Kullum muna yi maku Allah ya yi albarka.

********************************

" Abba wai ni kam sai yaushe za'a sallame ni?"

"Ina zan sani uwata? Ki bari dai har ki kara samun sauki."

"Nidai gaskiya na gaji, shi mutumin nan tunda ya aje mutum babu wanda ya kuma ganin shi."

Ameesha ta karasa maganar kamar zata yi kuka.

Harara Ummi ta watsa mata ta ce

"To ai ko yanzu kina iya tashi ki wuce, tunda ke kamar karamar yarinya ki ke ji."

"A'a Hajiya me kuma na harara? Baki ganin ba lafiya ne da ita ba?"

Kai Alhaji sai kayi ta goyon bayan Ameesha, duk maganar da taga dama shi take yi, yanzu don Allah ina laifin yaron nan?"

Dan murmushi yaja ya ce

"To naji amma dai lallaɓata ya kamata kiyi."

Su Alhaji Mansur ne su ka yi sallama, shi da matarsa fara'a sosai Alhaji Taheer ya saki da ganin abokin nasa.

" Sannu da zuwa Alhaji ku ne a wannan lokacin?"

Faɗa ɗa murmushi Alhaji Mansur ya yi ya ce

" wallahi mune muka ce yau dai tunda mun samu lokaci bari muzo mu duba mai jiki."

" Masha Allah ai mai jiki ma ta samu sauki sosai."

Zama su ka yi kafin aka hau gaggaisawa, Ameesha dai kanta a kasa ta kasa ko da kallon su, wani karin haushi ya rufe Alhaji Mansur, ganin yadda ya tasa Ameesha a gaba sai *sangarta* take masa ga uban kaya da ya zuba a ɗakin na kwaɗayi, kamar ba asibiti ba " yanzu da nine bani lafiya sai dai yazo gaishe ni, zanyi maganin ka"

( "Kai dai Alhaji Mansur hassada ta yi maka yawa, baka san hassada kan meshi ya ke komawa ba? Ubangiji ka rabamu da hassada don bata yi ba a rayuwa")

Hajiya Salaha wato mahaifiyar Najeeb ita ce ta kalli Ameesha da murmushi ta ce

"Daughter ya jikin?"

"Da sauki." Ta bata amsa.

Sun ɗan daɗe a asibitin kafin su ka yi sallama.

Asmad ne zaune ya jingina bayansa a kujerar da ke office ɗin sa , zuwan sa kenan daga gida, tunanin Ameesha ne ya addabe shi har ya kasa jurewa , yana son ya bata sallama sai dai kuma bai gaji da ganin ta ba.

Sannan yana jin haushin yadda yake ganin ta tare da Najeeb, domin ko da yaushe yana shigowa asibitin sai dai baya zuwa ɗakin da take, da yake ɗakin nata na musamman ne, ya kula kuma Najeeb ko da yaushe yana cikin asibitin.

Tsaki yaja a karo na barkatai ya faɗa a fili

" Ya zama dole na sallame ta domin gobe ne zan tafi Adamawa don jibi daura aure, kuma idan na bar asibitin a yau ni da kaina ban san ranar da zan dawo ba."

Da wannan tunanin ya mik'e ya nufi hanyar ɗakin da take, tun da ya doshi wajen ya hango motar Najeeb, sai ya ji wani kululun bak'in ciki ya tokareshi a zuciya , tabbas yasan yana cikin ɗakin yasa ta a gaba tana masa murmushi.

A kofar shiga ɗakin ya haɗu da Meena gaisuwar mutunci su ka yi ta ce

" Dr mukam yau she za'a bamu sallama? Mun gaji da zaman asibitin nan fa?"

Murmushi ya yi ya ce

" Yanzu zan baku sallama ku kwantar da hankalin ku, bari na shiga na kuma dubata."

Ya ida maganar yana shiga ɗakin .

Sai da suka gaisa da Ummi da Abba sannan ya dubi inda take kwance.

Najeeb ne zaune kusa da Ameesha suna hira kasa kasa,sai ka saurara da kyau za ka ji abin da suke faɗa, wani kallon ya yi wa Najeeb mai cike da ma'anoni daban daban, Malam ɗan bani waje zanyi aiki."

" Tom" Najeeb ya faɗa tare da tashi ya ce

" Babyn Ummi ina tunanin na tafi, idan an sallame ki tom sai nazo gida."

Gyada kai tayi kawai, don tunda taga Dr ɗan fullo ya shigo ta rasa nutsuwa, don haka sai ta kasa masa magana.
Chapter 37 · 0% Book details