← Book details Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 54

Sashe 41

Sangarta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Duk yadda ki ka ce haka za'a yi uwata, dama muna da meeting da su Alhaji Mansur, in na sauke ki sai na wu ce."

"Yawwa Abbana! Shi yasa na ke kara sonka." Ta kai karshen maganar tana kiss ɗinsa a kumatu. Murmushi ya yi cike da farin cikin yadda Ameesha ta yi.

Ummi da ke gefe ta ce

"Alhaji kenan kullum dai kai ke kara shagwaɓa yarinyar nan."

" Haba Hajiya dole na shagwaɓa yarinyar nan, ita fa kaɗai gareni gata da sunan Mamana."

"To Allah ya k'ara taimakawa."

Tana faɗan maganar dai dai da zuwan Ameesha "Ummi sai mun dawo."

"Allah ya dawo da ku lafiya."

Rike da hannun Abba su ka fita inda motar ta ke, har ta buɗe sai kuma ta rufe ta soma tafiya

"Auta ina zaki kuma?"

"Abba zan yi sallama da Ummi ne."

Ta bashi amsa tana tafiya, kafin Alhaji Taheer ya yi yunkurin yin magana har ta yi nisa.

Ita kanta ta rasa me yasa ta ji tana son k'ara ganin ummin, shi yasa kawai ta fasa shiga har sai ta gano Ummi ɗin.

Ummi da ke zaune ta yi mamakin ganin Ameesha ta dawo

"A'a ya kika dawo kuma?"

"Ummi ganin ki na dawo yi."

Ta bata amsa tana zama, kallo ɗaya zaka mata kasan jikin ta ya yi sanyi. "Anya kuwa Auta lafiyar ki?"

"Lafiya lau na ke Ummi."
Ta bata amsa tana kwanciya a jikin Ummin.

"To kuma na ga kin dawo?"

"Eh zan tafi ban son rabuwa da ke ne fa?"

"To fasa zuwa kawai."

"A'a Ummi zan tafi." Ta faɗa tana mik'ewa. Tana tafiya tana ɗagawa Ummi hannu har ta fita, a motar ta samu Abba yana waya, shiga ta yi ta zauna. Sai da ya kammala da wayar sannan ya juyo inda Ameesha ta ke

"Uwata sai yanzu ki ka fito?"

"Abba ina fa wajen Ummi ne." Kamar zata yi kuka ta ida maganar.

Bai ce komai ba ya ja motar. Suka tafi a kofar makarantar ya ajeta shi kuma ya wuce.

********

Zaune da wayarsa a hannu,sai juya wayar ya ke Number din ta ya ke son kira sai dai kuma yana tunanin abin da zai ce mata, da kyar ya yi shahada ya danna kira.

Ameesha da ke tafiya har ta kusa shiga class ta ji wayarta na ringing, cirowa ta yi daga cikin jakarta ta duba Number din, sai taga bata sani ba har zata maida jaka sai dai ta ɗauka.

Wani irin faduwar gaba ya ziyarce su lokaci ɗaya, Ameesha shiru ta yi bayan ta yi sallama, shi ma a nashi ɓangaren haka ya yi bayan amsa mata sallamar.

Kusan minti biyar sannan ta yi k'arfin halin ce wa " Hello wa ke magana?"

Sai da ya dai dai ta nutsuwar sa kafin ya ce

"Haba Princess nine fa?"

Murmushi ta saki mai kyau, amma sai ta yi kamar bata gane shi ba ta ce

"Ban gane ka ba ai..."

Tun kan ta ida maganar har ya katse, ɗan dariya ta yi da ganin ya kashe wayar. Shi kam tsaki ya ja da maganar da Meesha ta faɗa masa "wai wa ye?" Wannan abu ya bashi haushi.

Ita kam ko a jikinta class ta shiga, bar fito lacca ba sai karfe uku, yau Meena bata shigo ba haka kuma kawarta Ni'eema bata zo ba.

Don haka sai kawai ta kama hanyar fita don ta hau nafef, a hankali cikin nutsuwa take tafiya har ta fita wajen makarantar ta hau titi da niyyar tsallakawa sai ji ka ke kiii. Mota ta banke ta sai da ta daga ta sama sannan ta faɗi k'asa.

Kafin mutane su yi yunkurin ceto ranta har mai motar ya gudu, da sauri mutanen suka ɗauke ta zuwa asibiti don wajen basu da nisa da police station, da taimakon yan sandan aka amshe ta a asibitin Malam Aminu Accident and emergency room aka nufa da ita don ceto ranta, Allah yasa cikin wanda su ka kaita asibitin akwai wanda ya ɗauki wayarta, duba contact ɗinta ya yi yaga Number din Abbanta da sauri ya kira, lokacin Abba suna zaune da Alhaji Mansur sai hira su ke yi , ya ji karan wayarsa yana dubawa ya ga Number ɗin Ameesha murmushi ya yi ya kara a kunne yana faɗin

"Auta sai yanzu kuka fit...?

Bai gama rufe baki ba sai jin, mai kiran ya ce "kaine Abbanta ko to tana asibiti ta samu haɗarin mota, tana asibitin Malam Aminu Kano."

A kiɗime Alhaji Taheer ya mika hankalinsa ya yi mugun tashi, su Alhaji Mansur har suna haɗa baki wajen tambayar me ya faru?

"Ameesha ce wai mota ta bige ta tana asibitin Malam Aminu Kano."

Yana basu amsar ne yana tafiya.

Ko da Abba ya isa asibitin kasa nutsuwa ya yi, da ba'a barsu ganin ta ba, sosai ya yi wa wanda suka kai Ameesha asibitin sannan ya kira Ummi yana sanar mata, kuka ta fara ta na cewa "Allah sarki Auta dama shi yasa ɗazun ta kasa tafiya? Wayyo Allah ka tashi kafadar Auta."

Kan ka ce me har asibitin ya cika da mutane, sai dai duk wani taimako da ake wa Ameesha bata farka ba, kusan awa uku kenan manyan likitoci suka duk'ufa akan ta, kowa aiki yake abin mamaki babu wani ciwo da yake jikinta sai wani kusa da kanta, amma yadda numfashin ya ɗauke shi ne abin tsoro.

Asmad na zaune sai hira suke shi da Aneesa cikin farin ciki, sai jin wayarsa ya yi yana ringing, Dan tsaki yaja tare da kara wayar a kunne. Jin abin da ake faɗa masa a wayarta sa shi saurin mik'ewa

"Please Aneesa bari na je asibiti akwai babban matsala." Bai ko tsaya jiran me zata ce ba kawai ya yi gaba. Cikin sauri ya auri motarsa, ko parking me kyau bai tsaya yi ba ya tunkari emergency room din.

Haka kawai ya ji hankalinsa ya tashi, da taimakon addu'a ya isa gaban gadon "inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un". Shi ne abin da Asmad ya faɗa ya yin da ya yi arba da Ameesha.

"Princess me ya faru da ke? Dazun fa mu ka yi waya da ke?" A rude ya ke maganar jikinsa har rawa ya ke. Da sauri cikin kwarewa ya soma bata nashi taimakon, duk sauran likitocin gefe suka koma suna kallon sa, ya dai ki manin awa ɗaya kafin ya samu numfashin ya dawo dai dai, wani dogon ajiyar zuciya ya ja tare da hamdala ga Allah.

Suma sauran likitocin sun yi farin ciki sosai,kuma sun yaba da aikin Asmad ɗin. Da kansa ya gungura ta zuwa ɗakin hutu. Su Abba ma har hankalinsu ya ɗan kwanta da jin an samu numfashin ya dawo.

Sai da ta yi awa uku tana bacci kafin ta farka, lokacin ɗakin daga Ummi sai Meena da Abba. Meena ce ta kulla da Ameesha ta farka

"Ummi kalli bestyna ta farka."

Meena ta yi maganar cike da jin dadi, tare da nufa waje ɗin kiran Dr domin ya ce in ta farka a yi saurin sanar masa, murmushin farin ciki ne ya mamaye su Abba, har suna rufe rigen matsawa inda ta ke

"sannu Auta ya jikin?"

Da wani Irin kallo Ameesha ta bisu ina rashin sani, sun yi mamakin irin kallon sannan kuma bata yi magana da Kowa ba. Dai dai da zuwan Dr ɗan fullo.

Kallon Ameesha ya yi ya ce

"Princess kin tashi ina ke maki ciwo?"

Abin mamaki sai suka ji ta ce

"Princess kin tashi ina ke maki ciwo?"

Dan Zaria ido ya yi tare da murmushi ya ce

"Haba Princess kuma da tsokana ki ka tashi?"

Itama ma ta ce

"Haba Princess da tsokana ki ka tashi?"

Mamaki ya kama su da yadda Ameesha ta ke, don zuwa yanzu sun fahimci Ameesha fa ba wasa ta ke ba. "To me hakan ke nufi?"

Dr Asmad ya wa kansa tambayar da babu amsa.

_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad my Besty*

_*Ina taya dukkan Musulmai murnar sallah, Allah ya amsa ibadunmu Ubangiji ya sa muna cikin yantattu da wadinda aka yiwa gafara Allahumma amin*_

_ina cigiyar Baseera Sabo Nadabo! Please baiwar Allah ina kika shiga haka?_

*My Besty ke kam dama ta dabance, a lokuta da dama har rasa kalmar da zanyi amfani da ita yayin nuna maki zallar farin ciki da kulawar da kike min nake yi, amma duk da haka ina maki fatan alheri, Allah ya baki miji na gari Ubangiji ya nuna min auran ki muzo mu kwashi shokiiii*

``` Happy sallah Uncle HASSAN ATK & Uncle HUSSAIN ATK``` inji Sweet *SAFWAN* fatan kunyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana na baɗinbaɗaɗa

*17*
Zuru Ameesha ta yi tana kallon sa.

Shima Asmad ɗin zuba mata ido ya yi cikin wani irin yanayi.

A hankali ya girgiza kai, a zuciyar sa yace " *Lossing memory?* " Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un. Ashe maganar a bayyane ya yi ta sai jin muryar Meena ya yi ta ce

"What Dr Meesha tayi lossing memory? Hasbinallahu wani'imal walkil, Inna lillahi!

Haɗa rai ya yi yace " Please Meena kiyi shiru domin ban tabbatar ba."

Faɗin haka ke da wuya, sai ya nufi kofa da niyyar fita, zuciyar sa cike da tausayin halin da ta tsinci kanta a cikin.

Bai ko kalli su Abba ba, ya ce

" Alhaji bari na ɗauko wani abu a office."

Ita ma Ameesha maimaitawa ta yi, tana mik'ewa tsaye da sauri ta isa inda Asmad yake tayi saurin rik'o hannunsa ta kankame, sai kuma ta bata fuska.

"Cike da mamaki, haɗe da mutuwar jiki, Alhaji ya bi Ameesha da kallo, saboda yadda yaga ta kamkame hannayen likitan. Wannan bakon al'amari ne a rayuwar."

A hankali Dr ɗan fullo ya zame hannayen sa daga rikon da ta yi masa, ya zaunar da ita bisa gadon ya kalleta zuciyar sa a karye kamar zai zubar mata da hawaye "Zauna ina zuwa kin ji ko? Ya faɗa a hankali cikin dakin fuka. Ita dai kallon da ta yi wannan karon bata yi magana ba.
Chapter 41 · 0% Book details