← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 76

Sashe 8

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka hau tsallen murna, murmushi kawai Anty take cike da jin dadi, a kalla zuwan Jidda ya kara mata shakuwa da yaran sosai. Duk da tasan ba lallai Maman ta bar su ba, amma ko a hakan ita taji dadi sosai ba kadan ba.
   Tunanin yadda Amira zata fadawa Mama takeyi gashi har ga Allah tana son zuwa taga yadda garin yake da labarin da Jiddah take basu.

"Idan na fadawa Mama zata yarda?"

Ta tambayi Maryam, dage kafada tayi alamar oho sannan tace

"Kema kinsan wace Mama, da hakura kawai kikayi."

"Ba zan hakura ba, i will try my luck."

"Allah ya bada sa'a toh." Tace tana mikewa

"Bari kiga naje na aro wayar Ya Safiyya nayi game."

"Tab! Allah sa ta baki."

"Zata bani ai tasan nima an kusa siya min tawa."

"Sai dai haka, moha taso ka rakani wajen Mama kaji, Allah yasa ta bar mu."

Rike hannun sa tayi suka nufi bangaren Baba da suka san zasu samu Maman achan, kuma tasan in dai Baba yace yes Mama ba zata hana ba sai dai zata sha rakwashi da kallon banza, duk wannan daga baya ne in dai har sun tafi.

Sallama tayi daga kofar Muhammad ya kwace hannun sa ya shige ciki ita kuma ta tsaya tana jira a bata izinin shiga.

"Uwata shigo mana."

Baba yace yana gishingid'e yana duba wayar sa, shiga tayi kanta a kasa gabanta na dukan uku uku, ta ki yarda ta hada ido da Mama kwata-kwata, ta zauna a gaban Baban sannan tace

"Em em dama."

"Dama me? Ina jinki."

"In dai kaga Amira na haka ai akwai abinda zata tambaya."

"Ina jin ki toh."

"Dama Baba, so nake na bi Anty nima."

Da sauri Mama ta ajiye abun hannun ta, ta kalli Amiran da kanta yake kasa, ranta yayi masifar baci, ta kalli fuskar Baban ta karanci yanayin sa, fuskar sa a sake yana shirin yin magana ta rigashi

"Kin manta da bikin ummul? Ko ba zaki ba?"

"Wannan satin ne bikin?"

Baba ya tambaya yana kallon Maman

"Eh wannan ne, har sun yi anko ma fa, inaga dai ta manta,ummul ba zata ji dadi ba idan baki je ba."

"Ummul ba sa'ar Maryam bace ba? Ko Safiyya ma, ba komai sun wakilci uwata, ki shirya ki bisu kinji."

"Nagode Baba, Allah ya saka da alkhairi."

Sai ta tashi da sauri ta fita, ba tare da ta hada ido da Maman ba, tana fita Muhammad ma yace zai je, shima Baban yace toh. Kasa karasa abinda Maman take tayi a dakin, ta fice da sauri dan idan ta zauna ba zata iya rike bacin ranta ba.
[11/25, 3:54 PM] Rano2:             SL

        *7*

©®Hafsat Rano

****A tsakiyar falon ta tsaya ta shiga kwalawa Amiran kira, a tunanin ta, tana cikin wajen Antyn, bata san direct wajen Yaya ta gudu ba dan tasan haduwar su ba zatayi kyau ba, shiyasa ta salallaba ta gudu, ba kuma zata yarda su hadu ba sai gobe , dan duk bala'in Yaya sai dai ta barta amma a wajenta zata kwana ta san kuma Mama ba zata taba biyo ta wajen Yayan ba,gaisuwa safe ce kawai take hada su kuma shima kwana biyun nan da daminar ta dan ja baya zafi ya sako kai tsakar gida take fitowa tun sassafe ta basa baza tabarma.
    Dakin ta, ta shige ta san duk daren dadewa zata zo ta sameta ne, bata amince ba babu in da zata bi Halima dan har yanzu bata gama yarda da ita ba, duk yaron da zaka dauke shi aiki karshe ya aure maka miji ba kuma zaka taba amince masa ba har duniya ta nade, duk da idan da zaa saka mata wuka ace ta fadi aibun ta ba zata ce gashi ba, amma ita sam bata amince da ita ba, ba kuma zata fara daga yanzu ba, ta bar yarta ta bita garin da bata san me zata tarar a chan ba.
    Da la'asar fita ta kamata, ta shirya ta fice daga gidan ta manta shaf da batun Amiran, shagon ta ne aka kawo kaya, abinda ya fitar da ita kenan tare da Fauwaz, wanda basu suka shigo gidan ba sai dare. Kasancewar a gajiya ta dawo bata bi ta kan ta ba, ta kwanta dan da wuri zata sake fita washegari akan ragowar kayan da basu riga sun iso ba.
   Shirin su suke hankali kwance, murna wajen Jidda da Amira baa magana, Maryam a kasan ranta tana son bin su Amma bata shiryawa fadan Mama ba, shiyasa kawai ta hakura tana kallon su. Kitso akayi ma Jiddan me kyau duk da tsananin santsin gashin kanta amma da ya hadu da bahijja me kitso sai gashi ta kama mata shi, yayi kyau sosai dan sai da taji kunya yadda su maryam suka dinga koda ta wai kamar kan larabawa.

Cikin dare ta kasa bacci saboda zumudin tafiyar ana kiran sallah ta mike kamar wadda aka tasa, ta hau shiryawa tana sake hade kayan da zata tafi dasu. Tun dare dama tayi shara saboda haka babu datti, sai yan kayan da ba zaa rasa ba suma ta tattare kowanne ta saka shi a in da ya dace. A haka Anty ta sameta, batayi mamaki ba dan idan da sabo ta saba da wannan, sam Jiddan bata da son jiki kuma duk abinda ta san ya kamata yi kawai take ba sai an ce ba, bare kuma yau da take da zumudin ganin baffanta.

"Sannu Jiddah, Allah dai yasa kin yi bacci?"

"Nayi." Tace sai kuma ta dan russuna tace

"Ina kwana Aunty?"

"Lafiya lou Jidda, bari na dora mana ruwan wanka dan da wuri zamu fita in sha Allah, idan kin gama kije ki ga Amira ko ta tashi."

"Toh..." Tace cike da zumudi ta karasa abinda take ta nufi wajen Yayan dan Amira ta fada mata anan zata kwana saboda Mama.
   Ta tashi har tayi sallah ma,amma kuma yanayin ta be nuna wa Jiddah tana cikin walwala ba, kallon fuskar ta tayi, sai kuma ta zauna a gefenta tana mata kallo me dauke da alamar tambaya

"Na fasa zuwa." Tace a cikin yanayin da yake nuna kusa take da ta fashe da kuka

"Mama?" Ta tambaye ta

Daga mata kai tayi alamar eh

"Ok kiyi hakuri."

"Dan Allah mene dan na biku? Gaba daya Mama bata so taga muna harka daku bansan me yasa ba, yanzu ta turo Safiyya wai kar na soma bin ku."

"Bakin kishin ta na tsiya ai bazai barta ta hakurar wa zuciyar ta, ta karbi abinda Allah ya riga ya kaddara ba."

Yayah tayi maganar tana shigowa dakin rike da charbi a hannun ta, duk suka kalleta sai ta dora

"Nace dai duk ba akan kishi ake wannan abun ba? Idan akan shi ne yaci ace an ajiya ko? Shekarar Halima kusan takwas a gidan nan harda arzikin Usman, idan hakan be zama ishara ba sai yaushe?"

"Ba haka bane Yaya, tace wai bamu saba zuwa irin wajejen ba."

"Uwarki ce bazan hanaki kareta ai, me zai sameku a chan da ba zai same ku anan ba? Kin taba ganin an yi wa Allah wayo? Ba hujja bace bakin kishi ne kawai."

Mikewa Amiran tayi tana jin babu dadi, bata son maganganu irin haka akan Maman, musamman daga wajen Yayah, a kullum so take taga komai ya zama normal Mama ta yi hakuri ta bar komai ya wuce

"Idan kun gama shiryawa zan shigo."

Ta wuce kawai ta bar part din ranta duk babu dadi

"Yarinyar nan ba dai hankali ba dan tafi uwarta wallahi, dama uban yan girman kan chan da safiya sune suka yo uwarsu, amma sauran ba ruwan su."

"Uhum." Jidda tace itama ta mike, tafice ta bar Yaya na cigaba da mitar zancen.

A gurguje tayi ma Usman wanka tayi nata ta shirya cikin riga doguwa ta atamfa ta sallah da Baba yayi musu ita da Maryam da Amira. A shirye ta samu Aunty tana zaune tana waya a gefen gadon ta, yadda take wayar ya tabbatar mata da Baffa ne, zumudin ta ne ya karu sanda taji Antyn tana cewa sai sun zo. Bayan ta gama wayar ne ta dauko mata sarka da dankunne me kyau ta bata ta saka sannan tace ta jirata a falo. Fita tayi ita kuma ta yafa mayafin ta ta nufi sashen Baban, ta same shi ya shirya shima, da mamaki take kallon sa

"Ba dai fita zakayi?" Tace tun daga kofa, kafin ya bata amsa Mama ta turo kofar ta shigo, ya kalle ta sannan ya maida kallon sa wajen Auntyn yace

"Tare zamu, inaso zan ga Yaya."

"Yaran sun shirya?" Yace yana kallon Mama, dan dam tayi amma sai ta kame tace

"Sun kuma chanja shawara kasan abun yara."

Gid'a kansa yayi yace

"Taimaka min da hula ta akan bedside Halima."

"Toh." Tace ta wuce ciki, yana ganin ta shiga ya maida kallon sa kan Mama yace

"Minti goma sha biyar na basu su shirya, Muhammad ma yace min zaije dan haka kar abata min lokaci."

Wani kallo tayi masa, ya daga mata kai alamar haka yace, bata ce masa komai ba ta juya ta fice daga shashen. Dakin su Amiran ta wuce ta sameta a kwance a gado ta lulluba da bargo ranta babu dadi, a kanta ta tsaya fuskar ta a hade tace

"Sai ki tashi ki shirya yana jiranku, saura ki tsaya bata lokaci yace ni na hana kuma."

Da sauri ta mike zaune, tana kallon fuskar Maman cike da zumudin murna

"Ki shirya Muhammad ma, ki daukar masa sababbin kayan sa."

Daga haka ta juya ta bar dakin, da sauri Amira ta tashi ta hau ciro kayan ta a wardrobe da ta maida su, ta saka a trolley taje dakin Maman ta dauko na Muhammad ta hada, sannan ta shiga wanka ta watsa da mugun sauri sannan ta fito ta zura kayan ko shafa mai batayi ba,ta fita zata kira Muhammad Maryam tace mata ta masa wanka har ya tafi falon Baba, komawa tayi daki da sauri ta gyara fuskar ta, ta daura dankwali sannan ta dauko kayan nasu ta fito.
Chapter 8 · 0% Book details