← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 76

Sashe 62

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru ne ya ratsa motar, duk yadda yaga ga kokarin ganin abinda ya faru be dame shi ba, ya kasa sam, baki daya ransa a dagule yake ya rasa me yake masa dadi, daurewa kawai yake dan baya so Jidda ta damu amma deep down zuciyar sa tafasa take. Ko kaf matan duniyar nan sun kare ba abinda zai yi da Salma, shi da yake da mugun choice ma ba komai ne yake masa ba, bare ita da bata da mara ba da katon gardi a gabansa, shine har zata iya masa wannan sharrin, bayan shi tunda yake ma be taba ko kama hannun mace ko kannen sa mata ba idan ba Jiddah ba, ita ma kuma dan yasan halilin sa ce, amma shine har zata ce yana taba ta which idan ya fahimta suna so suce tabawa as in having sex.
  Dafe kansa yayi jin wani irin bacin rai na sake taso masa, ba dan alakar da ke tsananin su ba, babu abinda zai hanashi rufe su daga ita har uwar tata, amma ko a yanzu ba wai ya hakura bane, dole sai ya dau mataki. Kawai dan dai duk abinda zai biyo ta bangaren Mama baya taba kokarin ketare shi, shiyasa a dazun ma suka ci darajar ta.
  Tunda suka shigo motar take satar kallon fuskar sa be sani ba, damuwar sa ta dame ta matuka musamman da ba taba ganin shi tayi a irin wannan yanayin ba, juyowa yayi suka hada ido ta marairace masa fuska kamar zatayi kuka, hannun ta dake cikin nasa tunda suka shigo ya shiga murzawa a hankali kafin ya jawota baki daya jikin sa.
   A harabar wajen Faisal yayi parking, ya daga kansa yana kirga floors din sai ya ciro wayarsa ya kira Madakin sukayi magana yace gashi nan. Bud'e kofar yayi yace ta fito shima ya fito ya zagayo ya gyara mata Hijab din ta sosai sannan ya rike hannun ta

"Ba zamu dade ba, marriage cert kawai zasuyi mana mu koma gida."

Gid'a masa kai tayi yayi murmushi kad'an ya maida kallon sa wajen Madaki da ya sakko yake nufo su,

"Oga da kansa." Ya mika masa hannu suka gaisa ya kalli Jidda kad'an

"Ina wuni?" Ta gaishe

"Lafiya lou amarya, ya gida?"

"Muje ciki ko?" Tariq yayi saurin shiga maganar ya katse mata hanzarin amsawa

"Muje toh."

Yayi gaba suka bi bayan sa, yana tafiya da ita a hankali. Lift suka hau zuwa office din madakin, ya zauna bayan ya nuna musu wajen zama sannan ya fito da takardun ya mika ma Tariq din da pen, ya cike ya mika masa, sai ya ciro cert din ya cike komai ya bashi sukayi signing sannan ya fita zuwa wajen da suke printing ya bada akayi printing nasa out bayan shima ya saka hannu da stamp akai, wajn witnesses ma aka saka hannu cikin kankanin lokaci aka gama komai abinda yake iya kai 3days ma wani lokacin har sati ko fiye. Suna zaune ya dawo ya mikawa Tariq brown envelope yace

"An gama oga."

"Haka da wuri? Thank you so much."

"Haba haba! Ba komai wallahi."

"Nagode sosai." Ya mika masa hannu

"Bari mu koma."

"Shikenan toh, sai na jika. Fauwaz yace min ka kusa wucewa ko?"

"Eh in sha Allah."

"Ok Allah ya bamu sa'a baki daya."

"Amin."

"Amarya? A gaida gida."

"Mun gode." Tace a hankali

Suka fice ya girgiza kai yana murmushi, Tariq ba zai taba chanjawa ba, shi be ma yi tunanin Tariq zai yi aure nan kusa ba ma, kuma to a very young girl haka, irin su dama Allah yafi kama su wallahi. Dariya ya sake yi ya cigaba da aikin da yake yi kafin zuwan su.

  Gidansu suka wuce ya kira Fauwaz tun suna hanya yace yaje wajen Aunty ya karbo masa passport din Jidda da important takardun ta ya jirashi a compound din gidan zai karba. A compound din suka same shi yana tsaye yana jiran su.

"Ba zamu shiga ba?" Ta tambaya ganin ya rike ta bayan motar ta tsaya

"Eh."

Yace daidai lokacin Fauwaz ya karaso , ya sauke glass din ya karbi documents din sannan ya rufe yace su tafi. Shiru tayi bayan sun sake daukar hanyar gidan su, ta tabbatar akwai babban dalilin da ya saka shi hanata shiga gidan, tunda taga sanda ya tsuke fuskar sa bayan sun shiga gidan nasu. Wayar sa ce tayi kara ya dauka ganin number Baba ya sashi saurin dagawa

"Tariq."

"Baba barka da rana."

"Barka dai, kuna lafiya?"

"Alhamdulillah."

"Toh Masha Allah, ya shirye-shiryen tafiyar? Duk da ma dai mun dawo muna nan Villa, so nasan zamu hadu kafin ka tafi sai muyi maganar."

"Dama jiran dawowar ka nake Baba, na dan chanja shawara ne."

"Toh ba laifi, mecece shawarar?"

"Dama so nake mu tafi da ita."

"Ita? Wa?"

"Um.. Jiddaaa."

"Toh! Toh shikenan, hakan ma yayi ai."

"Nagode Baba, sai dai kuma..."

"Ina jinka?"

"Maganar Visa din? Zaa iya processing dinsa a cikin satin?"

"Ba damuwa, kayi applying kawai sai ka fada min idan ka yi, ko a samu agent yayi applying din?."

"Na ma kusa gamawa."

"Toh shikenan, sai ka shigo da daddare in sha Allah."

"Nagode Baba, Allah ya kara girma."

"Amin ya Allah, Allah yayi muku albarka."

"Amin ."

Ya amsa yana jin nutsuwar zuciya, Baba ne kawai yake fahimtar sa, har ya saka masa albarka a komai. Mafiya yawan lokuta mata suna mantawa da wannan tsohuwar kalmar ciwon 'ya mace na 'ya mace ne a duk lokacin da wani abu ya hada su da mace yar uwarta da bata da wata alaaka da ita,musamman a bangaren aure sam basa daga kafa sai su futtuke su murje idon su kamar ba mace bace yar uwarsu kamar yadda suke yawan ikirari, duk da dai ma yanzu zamani ya chanja an daina fadin ciwon 'ya mace na 'ya mace ne sai dai a barshi a ciwon mace na namiji ne dan su suka fi fuskantar wadannan halittun duk da suma watarana idan suka botsare musu basa gane kai ko kafarsu.

  Taimaka mata yayi ta fito ya kwaso takardun suka shiga ciki. A falon farko ta cire Hijab din ta wuce kitchen dan dubo Godiya shi kuma ya shige ciki. Bacci ta sameta tana yi a dakin ta sai ta juyo kawai tazo ta dauki hijab din ta wuce ciki. Daga toilet ya fito fuskar sa a jike, ya nannade hannun rigar sa zuwa damtsen sa da yake a cike.

"Yi alwala muyi sallah."

Yace yana daukar sallayar ya shinfida, wuce shi tayi taje tayo alwalar ta same shi yana goge fuskar sa da dan karamin towel, mikewa yayi ganin ta fito ya hau kan sallayar ita kuma ta zura Hijab dinta tabi bayan sa. Juyowa yayi gaba daya bayan sun idar ya dora kansa a saman kafarta ta waro ido tana kallon gashin kansa, lumshe idon sa yayi yana so ya sake samun nutsuwa. Bata hanashi ba, ta cigaba da kallon gyararren gashin kansa da yake ta sheki a kwance yayi layi layi, hannun ta, ta kai ta shafa kan nasa a hankali, da sauri ya bud'e idon sa ya daga kansa sama ya kalle ta,tayi saurin janye hannun ganin yadda yake kallon ta idon sa a lumshe sun shiga ciki sosai

"Cigaba plsss karki daina."

"Na'am?"

"Yes! I love it."

Kasa daga hannun tayi duk kunyar sa ya kamata, kamo hannun nata yayi ya dora akan nasa yana maida idon sa ya rufe ruf. Bata da zabi illa ta cigaba da shafa masa kan har zuwa wajen keyar sa, wata iriyar kasala ce ta kamashi, be san cewa kan nasa zai zama weak point dinsa ba sai yanzu, ji yayi yana neman loosing control, sai ya riko hannun nata da hannuwan sa biyu ya mike zaune yana jawota jikin sa.

"An samu matsala."

Ya rad'a mata a kunne yana kankame ta, ya shiga sniping wuyan ta zuwa saman habarta. Tsananin tsoro ne ya bayyana akan fuskar ta, hannun sa ya kai saman eye lashes dinta ya rufe mata idon yana sake rad'a mata

"I promise to be a gentle man."

Da sauri ta janye jikinta tana kokarin tashi, wane irin gentle man ana zaune kalou? Yasan kuwa yadda take ji? Hanata tashi yayi ya rike ta k'akam, duk ita ta jawo shi wallahi bashi da niyyar zuwa again, ita ta kunna shi, shi kuma ba zai iya resisting ba. Tsoro ne ya shigeta ganin da gaske yake ba da wasa ba. Haka dama auren yake?

"Wayyo na shiga uku Baffa na."

Tace jikin ta na rawa kaamar mazari, dagata yayi daga rikon da yayi mata, yayi musu masauki akan gadon yana rufa mata jikin sa baki daya, ya tsura mata ido yana bin kyakkyawar fuskar ta da kallo. Saman idonta yayi kissing kad'an yana kara hango zallar tsoro da firgici cikin idon nata.

"Jiddanah."

Ya kira ta da wata irin murya, kin amsawa tayi dan bata da bakin da zata iya budewa gaba daya ya dora mata nauyin sa ya hanata ko da motsi ne

"Calm down and take a deep breath, ba abinda zan miki I promise."

"Zaka daga ni?"

"Eh in dai kika nutsu ba."

Ajiyar zuciya ta sauke ta bud'e idon ta kad'an ta kalle shi, tayi saurin maida idon ta kulle tana jan numfashi

"Zan hakura on one condition, idan kin amince."

"Me?"

"Tashi ki cire wannan rigar pls."

Ya daga ta yana zama a gefen gadon

"Dan Allah kayi hakuri wallahi zan mutu."

"Ba abinda zan miki fa, so nake kawai ki chanja ta, tayi zafi da yawa plus bana son ta, ko kuma na cigaba.."

"A ah zan." Tace ta mike tana ganin kamar ba Ya Tariq din da ta sani ba, kamar wani daban ne aka chanja mata shi. Kallon jikin ta yake har ta sauka ta nufi wajen kayan ta bud'e closet din ta tsaya tana kallon jerin kayan.

"Zaki iya barin inners kawai it's ok."

Yi tayi kamar bata ji shi ba, ta cigaba da daddaga kayan tana jan lokacin, yarfe hannun sa yayi ya mike ya karaso wajen tayi saurin jawo wata atamfa doguwa ya rike hannun yana bata fuska

"Ni ba wannan ba."

"Wacce toh?"
Chapter 62 · 0% Book details