← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 76

Sashe 19

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yasmin is average.".

"That's not all."

"Ok ina jinka "

"I want a shy girl, me kunya sosai bana son wadda idanunta suke a bude,bana son yarinyar da zata ce tana so na, nafi son yarinyar da zata zama very very hard to get, bana son cheap girl"

"Ehen."

"Very beautiful with a soft and long hair, me addini sosai, mara son yawan magana da hayaniya, wadda ta iya girki me dadi...."

"Allahu Akbar."

Ishaq yace yana tura lomar chicken biryani

"Allah ya cika maka burin ka, amma fa banda hard to get din nan, dan za'a iya samun matsala."

"Haka nake so ba wata matsala."

"Toh Allah yabada sa'a Capt."

"Amin." Yace yaja bakin sa yayi shiru dan dama ba kasafai ya fiya doguwar hira ba idan ba da Ishaq din ba.
   Kallon sa ya dinga yi har ya gama cinye abincin tas ya sha ruwa yayi hamdalah sannan yazo suka shiga karatu wanda yawanci Tariq din ne yake guiding dinsa a duk abinda be gane ba, ya bala'in iya mathematics da physics shiyasa ma ya zabi bangaren aviation yana so ya gama yayi training din zama pilot in two years ya hada 1500 hours ya samu Airline transport pilot certificate. Target din shi kenan, kuma ya dauko hanyar cimma shi. Sai dare sosai ya kwanta bayan sun gama karatun Ishaq din ya tafi.

***Sabon part din da Baba ya siya aka soma ginawa wanda ginin yake sauri sosai, duk da cikin gidan aka shigo da ginin amma zai zama basu da wata alaka kowa zata zama tana bangaren ta. Mama ce zata koma sabon part din kowa ma yasan wannan, Aunty bata damu ba sam, tunda itama part din Maman za'a gyare mata a hade da main falon duk cikin nata, sai kuma a bawa su Fauwaz part din Auntyn. Sosai ginin yake sauri dan Baba so yake a gama da wuri Mama takoma a kalla ya san hakan zai rage wata matsalar.
Suna zaune tare da Malam Nura da Alhaji Adamu a harabar gidan, aka kira Baba a waya, ya daga ganin number ce ta PA din Mr President wanda ya kasance class mate din sa ne, tunda ya zama shugaban kasa yake kokarin jawo Baba jikin sa amma sam Baban yaki yarda har sai da ya gamsu dari-bisa dari da yanayi da tsarin mulkin nasa sannan ya amince har aka saka sunan sa a cikin sababbin ministocin da za'a nada, babu wanda Baban ya fad'awa ya dai ce musu zai shiga siyasa su taya shi da addu'a. Daga wayar yayi suka gaisa sannan yace an aiko masa da invitation ta email sannan an yi masa booking flight zuwa Abuja a ranar shima an tura masa e-ticket din. Tashi Baban yayi bayan ya sanar dasu dalilin wayar sukayi masa fatan alkhairi sannan ya shiga gida. Wajen Yaya ya wuce kai tsaye ya sameta da maganar. Rawa ta shiga takawa cikin farin ciki, dariya Baban ya dinga yi har sai da tayi rawar ta gama sannan tace

"Allah ya tabbatar da alkhairi,ya bada sa'a, ya raba ku da sharrin makiya ya baku ikon sauke nauyin da aka dora muku."

"Amin Yayah, Amin ya Allah. Adduar kenan."

Daga nan ya wuce cikin gida ya kira Aunty da Mama zuwa falon sa ya sanar dasu, tashi Mama tayi ta rungume shi da sauri saboda tsabar mamakin maganar, minister fa? Baban matsayi ne sosai wanda yayi daidai da ita, ya kuma dace sosai da ita. Murmushi kawai Aunty take duk kunya ta kamata, sai da Mamaan ta sake shi sannan Aunty tayi masa Allah ya sanya alkhairi. Ya amsa ya saka musu albarka gaba daya, sannan yace Mama ta hada masa kayan da zai tafi dasu kasancewar ita ke girki ranar, dakin sa ta shiga ta barsu su biyu, ya nuna mata kusa dashi yace ta dawo, ta koma ta zauna ya kalle

"Har yanzu akwai abinda yake damunki ko?"

Girgiza masa kai tayi,

"Babu komai."

"Gobe Safwan ya kaiki asibiti a sake duba ki a duba bp dinki, ban yarda da yanayin ki ba."

"Allah ba komai."

"Toh shikenan, in sha Allah kafin na dawo zaa yi kokarin a gama gyara gidan nan, sai kuyi min duk list din abubuwan da zaku bukata, duk da nasan yanzu zaman namu anan ba zai dade ba, amma dai bari muga abinda Allah zai yi."

"Allah ya taimaka ya bada sa'a."

"Amin Halimatu." Yace yana murmushi, fitowa Mama tayi fuskar ta babu yabo babu fallasa dan farin cikin da take ciki ya danne haushin Auntyn da take ji, ciki ya shiga da nufin shiryawa ya barsu a zaune suna jiran fitowar sa, babu wadda tayi magana a cikin su, har ya fito cikin shigar manyan kaya da shadda da babbar riga,ya dora dara akan sa,ya kira Safwan tun kafin ya shiga wanka yace yazo ya kaishi airport. Sallama yayi daga kofa sai da aka bashi izinin shigowa sannan ya shigo, ya russuna ya gaida Baban,sannan ya gaida su Mama.

"Airport zaka kaini." Baba yace yana daga tsaye, Mama ce ta tashi ta dauko suitcase dinsa ta mikawa Safwan din, ya karba ya fita da ita, sannan shima ya sake musu sallama ya fita. Ya rage sai su biyu, Mama ce ta fara ficewa tana bata fuska, sannan Auntyn itama ta fita ta rufo masa part din,da bawa Usman key din tace ya kai wa Maman.

***Sati Baba daya a chan akayi komai ya saka hannu yayi approving aka saka ranar da za'a yi taron nad'a su wanda zai kama kwana biyu tsakani, be dawo ba sai kawai ya aika Mama da Aunty suka zo,sai Kawu Rabi'u da Alhaji Adamu da Malam Nura aminan Baban, sai Safwan.
Jidda, Amira, Umaima da Maryam suka tattara suka koma part din Yaya, ta samu abokan yi aikuwa sukayi ta fama. Washegari suna zaune aka dauko maganar Tariq, Yaya ta zage tana fada musu matsalar sa ta rashin lafiya, ita a lallai sai ta yi convincing dinsu sun yarda ba kalou yake ba. Maryam ce tace

"Yaya fa ras yake wallahi, kawai yanayin sa ne haka yanayin Malam dinki."

"Yo wannan ai har yaci uban Malam wallahi."

"Bari dai kiga a samu wata tayi wuf da kalbinsa, ba ma zaki gane shi ba."

"Kayya, masu irin bakin halin nan fa basu ragawa kowa ba,matan nasu ma su suka fi shan wahala dasu."

"Aiko Ya Tariq zai baki mamaki Yaya, ai shi na zamani ne ba irin Malam dinki ba."

"Toh zamu gani ai, ni wallahi da ma wayata tana irin kiran nan da ake ganin mutum da sai na kirashi na sake jaddada masa maganar shan maganin nan, ku kuma duk ba waya gwara ma ni da yar karama."

"Sai dai na karbo ta Ya Safiyya." Umaima tace tana mikewa

"Yawwa karbo, kice tazo nan nace itama dole na tashi tsaye dan kusan bakin halin su daya da uban gayyaar."

"Yanayin su ne a haka." Jidda tace ba tare da ta kawo komai ba, wani kallo Yaya tayi mata sannan tace

"Eheee? Kare su kike jidda?"

"A ah Yaya, kawai dai.

"Kawai me?"

"Ba komai." Tace tana murmushi

"Yawwa, gwara ma dai karki kare shi."

"Toh Yaya."

Karbo wayar Safiyya Umaima tayi, ita kadai take bawa da taje ma bacci take sai kawai ta dauko ta taho. Ta kunna data ta kira shi ta mikawa Yaya wayar

"Idan ya daga kiyi magana, kar kuma kice ni na kira wallahi."

Karba Yaya tayi, ta mike rike da wayar tana jira ya dauka, tana kallon kanta a cikin wayar mamakin yadda al'amarin yake kasancewa na sake kamata. Ta dau lokaci tana ringing kafin a daga, fuskar sa ta bayyana a cikin wayar, dafe kansa yayi ganin fuskar Yaya ta cika screen din, kautar ta kansa yayi yana kokarin danne dariyar da ta taso masa dan duk abin mutum idan yaga fuskar Yaya a cikin wayar sai yayi dariya.

"Kana jina?" Tace tana daga murya da karfi,

"Ya Allah!" Ya motsa bakin sa, sai kuma yace

"Ina jinki?"

"Yawwa, baka iya gaisuwa bane ni wai?"

"Ina wuni?"

"Lafiya lou, naga ka kara haske ko mai kake shafawa ne?"

" A ah Yaya, bana shafa komai."

"Toh ai shikenan, baki yi min murnar Babanku ba."

"Allah ya sanya alkhairi." Yace kai tsaye dan shi fa duk abinda tace kawai ahakan yake biye mata

"Safiyya ce ta kira miki wayar?"

"A ah Umaima ce ta aro wayar Safiya ta kira min kai tunda kai ba zaka kirani ba."

"Ina Umaiman?"

"Gata." Yaya ta juyar da wayar zuwa bangaren da suke zaune

Da sauri ta dukar da kanta, Amira ma tayi kasa ya rage saura Maryam da Jidda kawai yake gani. Girgiza kai Maryam ta hau yi

"Wallahi Ya bani na kiraka ba."

Kallon su yake su biyun Yaya na sake hasko masa su a tunanin ta Umaima ce a zaune sam bata lura sun buya ba ita da Amira. Shiru yayi be ce komai ba, dan ganin figigiyar yarinyar nan ya saka shi manta abinda ma zai ce, tana nan yadda take bata sauya ba. Kashe wayar yayi kawai ba tare da yace komai ba.
__SL__**

      ©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (16)

***Da yamma Isma'il yazo daukar su, cike da zumudin ganin jiddah, shi da Farouk suka zo yayi parking a chan gefen gidan sabo da motocin dake wajen sannan ya kira Mom a waya yana fatan su fito tare da jiddah, dan haka ma yazo da Farouk dan ya ganta a zahiri ya daina cewa ya haukace akan yar karamar yarinya. Fitowa sukayi suka tsaya a jikin motar Farouk ya kalle shi ya kwashe da dariya

"Wai duk zumudin ne haka?"

"Ba zaka gane ba, kwana biyu da ban ganta ba, ji nake kamar na shekara ban ga cute face din ta ba."

"Uhum umm, sannu Romeo"

"Ai nafi Romeo sai dai baban Romeo."

"Ah lallai, sannu."

"Yaww, idan ka ga babyn zaka tabbatar na iya kamu, ni zan raini kayata, ta tashi ta tsarin da nake so."

"Gaskiya ne kuma, amma fa ana iya samun matsala irin haka, sai kaga karshe yarinya tace bata so."

"Think positive dan Allah, in sha Allah babu abinda zai faru."

"Allah yasa."
Chapter 19 · 0% Book details