← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 76

Sashe 30

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zamu zo sallah fa, ko weekend nasan ba wai mun tafi gaba daya bane, ni ma ba son tafiyar nake ba, kinga achan zamu fara school ni da Amira shiyasa ma."

"Ai shikenan, zan shigo gobe."

"Ok Allah ya kaimu, sai kinzo."

"Amin, bye."

"Bye."

Maimakon ta ajiye wayar sai ta samu kanta da shiga photos din wayar, ta bude hotunan sa, tana dubawa,tana tuna wai mijin tane,an daura musu aure, bata san me take ji game da hakan ba, kawai tasan tana jin ta at ease, bata da wata damuwa ko fargaba a zuciyar ta. Ba kamar idan taga Isma'il ba, ba kuma kamar ace Isma'il aka aura mata ba, ta tabbatar zata iya bori akan hakan.
Ya Fauwaz ne ya kirata, tana dagawa ya hau yi mata kirari

"Kaga amaryar Ya Tariq, kaga amaryar Captain Tariq, kaga amaryar international pilot, eh Masha Allah, ban taba ganin perfect couples irin ku ba, kun yi matukar dacewa, da za'a bada award za'a iya baku award din perfect couples of the year."

Dariya take tunda yafara maganar,

"Kai Ya Fauwaz." Tace farin ciki na mamaye zuciyar ta

" Allah da gaske Jiddo, auw Aunty Jidda."

"Na shiga uku, nice Auntyn?"

"Emana, kin zama matar Big B, ai dole ace miki Aunty."

"Kai dai Ya Fauwaz ka iya tsokana wallahi."

"Allah ba tsokana bace, da gaske nake. Har Allah, Allah nake ya Tariq ya dawo yaga amaryar sa, nasan ji zai yi kamar an tsunduma shi a aljanna."

"Hum umm." Tace tana giggling

"Toh ya ake ciki?"

"Alhamdulillah wallahi."

"Toh Masha Allah, dama nace bari na kira matar yaya, kar ya dawo yace mun bar masa mata babu kulawa."

"Ya Fauwaz ko?"

"Na barki lafiya toh."

"Nagode."

Wani irin dadi ne ya rufe ta, dan ba karamin dadin kalaman Fauwaz taji ba, ya bata kwarin guiwa sosai wanda har ta soma hasaso rayuwar ta anan gaba kad'an. Murmushi tayi tana lumshe idanun ta, ta furta a hankali.. Matar Ya Tariq

***Washegari da wuri Safeera tazo, suka shige daki suka shiga hira, har kusan azahar sannan ta je ta kawo musu abinci suka ci sukayi sallah, sannan Safeeran tace zata tafi dan Mom ma da kyar ta barta tazo dan dai tana son duk abinda suke so ne, mayafi ta yafa ta rakota gate in da driver gidan su yake jiranta. Hakurin abinda ya faru tsakanin ta da Ya Isma'il ta bata dan duk yadda taso dauko maganar da suna ciki Safeeran taki yarda da ta dauko maganar sai ta goce da ta sake daukowa sai ta shashantar da maganar ko ta nuna bata ma ji ba. Yanzun ma tsaki tayi kawai ta harare ta,ta shige mota. Part din Yaya ta wuce ta sameta kafarta na mata ciwo, ta dauko maganin da ake shafa mata, ta shafa mata a kafar sannn ta zauna tana rage mata zaman kadaitar.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (24)

***Kwanan ta biyu a gidansu, Baffa yayi mata nasiha da kashedi sosai akan abinda ya faru, ya kuma ja mata kunne sosai akan kar yaji kar ya gani, duk a tunanin sa zata bijire, be san da gaske take son abun. Wuni tayi ranar da tazo a gidan Saude wadda akayi bikin ta da kaka, bata samu zuwa ba lokacin suna examz, gashi hadda tsohon cikin ta, sun sha hira suka tuna da sannan ta dawo da la'asar sakaliya.
Iya Lami nata haba-haba da ita,ta share ta kamar bata san Allah yayi ruwan ta a gidan ba, dan ko kad'an bata son matar dan babu kalar azabar da bata gana mata ba, akwai wani duka da tayi mata har yanzu da ragowar shatin dukan a gadon bayan ta abunka da fara. Shiyasa taki sakin jiki da ita sam bare ma su zauna suyi doguwar magana. Ranar da zata tafi Aunty ta turo aka dauketa, dan ta karasa abubuwan da bata karasa, dan da safe zasu tafi washegari.
A tsakar gidan Yaya ta tarar dasu ana ta fama da Yaya tayi tsalle ta dire babu shegen da zai sakata shiga jirgi, idan kuwa akace dole toh ta fasa tafiyar, duk yadda Fauwaz da yazo yaso ya fahimtar da ita sam taki fahimta, kamar ma a tsorace take da al'amarin, gashi a wannan yanayi na insecurity babu yadda za'a yi a barta ta shiga mota, haka kuma a barta ita kadai ma matsala ce.

"Yaya menene?" Tace tana matsawa kusa da ita

"Yawwa gwara da Allah ya kawo ki, kiji dan wulakanci wai jirgi zamu hau idan zamu tafi."

"Eh Yaya, ba bata lokaci nan da nan zaki ga anje."

"Aikuwa banga uban da ya isa ya sakani hawa jirgi ba wallahi."

"Har Baba?" Fauwaz yace yana dariya

"Ko Kaka ne, ehe."

"Ah abun azimun ne, bari na kira Baban da kansa yayi miki magana, kila shi yayi convincing dinki."

"Duk ma me zakayi kayi, na gama magana."

"Muje ki zauna Yaya, ki daina yawan fada kina tada hankalin ki dan Allah."

"Toh yaran nan ne duk hanyar da zasu birkita min lissafi sun santa, ina dalili za'a ce dole sai na hau jirgi? Ai ba dole bace Habujan ko? A kyale ni dan Allah.".

Sai ta fara tari da karfi, saurin tallafa mata jiddah tayi, ta mika mata ruwa tasha tarin ya lafa, zata cigaba da sababi Jidda tayi saurin cewa

"Kiyi shiru karki sake tarin, ba in da zaki a jirgi, a mota zamu tafi ni dake sai su suyi ta hawa jirgin su."

"Yawwa toh idan hakan ne na amince."

Kallon Jidda Fauwaz yayi, kallon kunfi kusa ya juya yana ayyana yadda zai yiwa taurin kan Yayan. Be kira Baban ba kamar yadda yace, sai kawai yaje ya samo maganin bacci, ya ajiye a daki, da safe bayan sun shirya tsaf, sun fito ya dauko lemon exotic madaidaci ya saka mata maganin baccin dan daidai wanda ba zai bugar da ita ba, ya shiga part din ya sameta ta saka sabuwar atamfar ta, da sabon Hijabin ta fari kal, sai takalmin shima sabo tana cike da jin dadi ga sabon lalle a kafar yayi har ya soma duhu-duhu.

"Ya ka gani?"

"Kin fita fes fes ko ba sabula mutuniyar."

"Godiya nake kaji, kasan fa kakanku tsabar dunkum dinsa ko yaba abu bayayi, ni bansan dadin kayi abu miji ya yaba ba, sai bakin rai da turbune fuska kamar shi aka dorawa baki daya matsalar Nigeria."

"Innalillahi, wai Yaya ba zaki kyale bawan Allahn nan ya huta ba, ko me yayi ai yaci ace an yafe masa haka nan."

"Toh ubana, sai ka fada min abinda ya kamata nayi tunda kai ka haife ni, ko kai kake bani ci da sha."

"Allah ya huci zuciyar Hajiye Dije, ga exotic na kawo miki kisha idan kun shiga mota, sai mun hadu a chan dan mu dai jirgi zamu hau."

"Ah ka kyauta, kasan kuwa dama na kwana biyu ban sha ba, shegen likitan nan bakin mugu wai a hanani shan kayan zaki kamar shine ubana, shikenan Alhaji yasa akai daina siyo min."

"Yanzu dai gashi nan na kawo miki, kisha karki bawa kowa fa, naki ne ke kadai tawan."

"Uban yan dadin baki, naji ni kira min jiddah mu dau hanya, kar muyi dare duk da dai ance sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je."

"Gani ma Yaya." Ta shigo sanye da atamfa lemon green and orange tayi mata kyau sosai har sa da Yaya ta kasa dauke ido daga kallon ta

"Wai wai wai, chanchadi."

A kunyace ta karaso ciki, Fauwaz yayi mata signal da ido yana nuna mata juice din hannun, ya fita. Bata gane komai ba, sai ga message dinsa bayan ya fita

"Make sure tasha juice din nan, sai mun hadu a airport."

Kallon juice din tayi ta kalli Yayan,

"Kisha lemon naki Yaya sai mu tafi, an gama saka kayan a mota."

"Auw toh." Tace tana bud'e murfin, ta kwankwade shi tas da dan sanyin sa dama, jidda ta karbi kwalin ta jefa a dustin sannan suka fito harabar gidan, ta taimaka mata ta shiga motar itama ta shiga, sannan suka fita daga gidan, suna fita motar su aunty itama ta bi bayan su ita da Usman sai Fauwaz din a gaba.
Bacci ne ya soma daukar Yaya sama-sama, jiddah na kallon ta, ta gyara mata ta jingina sosai bacci me nauyi ya dauketa. Suna isa airport din aka samo wheelchair aka dora ta, aka sakata a cikin jirgin suka lula sai Abuja.

***Sabuwar Rayuwa! Sabon Shafi***

Baki sake Jidda take kallon garin yadda ya tsaro, bata dai taba hasaso haka Abujan take ba, ta dai san tana da kyau amma bata kawo haka ba,sosai yayi mata kyau kwarai, ta kalli Aunty sukayi ma juna murmushi, har lokacin Yaya tana ta sharbar baccin ta.
Unguwar da suka shiga ita ta sake rikita Jidda har ma da Aunty duk da tana boyewa, babbar unguwa ce da manya manyan gine-gine tsararru, cikin tsari gwanin sha'awa. Shiru babu motsin kowa ba zaka taba cewa akwai halittu da suke rayuwa a cikin wajen ba
A kofar wani babban tangamemen gate suka tsaya, gate din ya bude da kansa suka kutsa kai cikin katafaren filin gidan, wanda yake dauke da motici manya daga chan gefe, sai shuke-shuke masu ban sha'awa.
Wani matashi ne yazo bayan sun tsaya, ya bud'e musu kofar ya russuna ya gaida Auntyn sannan yace

"Ga part din chan."

Ya mika keys din, karba Jiddah tayi, Fauwaz ya zagayo ya leka Yaaya da take ta sharbar bacci, ya kalli aunty ya kwashe da dariya

"Ya za'a yi da ita yanzu Aunty?"

"Ai baka kyauta ba wallahi,."

"Aunty bansan ya za'a mata ba wallahi, kinsan kafiyar Yaya."

"Ni dai kar a samu matsala fa."

"Babu in sha Allah, peaceful bacci fa take, kuje bari na kirawo masu aikin nan na bq su taimaka sai a kai ta part dinta."

"Je ka kirasu dai ina nan, Jidda jeki ke da Usman gani nan."
Chapter 30 · 0% Book details