← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 76

Sashe 32

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya dai kina son tarewa Jidda abinda mu fa wasa muke tsakanin mu, amma kin hakikance kamar gaske, haba!"

"Cewa tayi tana son wasa ne, kaji min yara, ba matar yayanku bace, ku bata girmanta"

"Kai innalillahi, wallahi Yaya zama dake sai an shirya, duk dai take-taken korar mu kike daga wajen nan, ba kuma in da zamu wallahi."

"Sai kuyi tayi ai, jaraba. Taso Jidda muje kiga wani abu, irin hade-haden tsofaffi ne amma yafi shirmen da ake baku na wannan zamanin."

"Ahaap, dama duk munsan kwanan zancen, shiyasa kike korarmu, wallahi Jidda ki kiyayi concoction din da Yaya take hada miki, sai kinje ta zugar miki da ciki kafin karshen sati kizo duk ki rame."

Maryam tace tana yin hanyar fita dan tasan ko ta zauna ma Yaya sai ta mata dundu

"Ba ruwanku, tsakanin mu ne da Yayata."

Jidda tace tana dariya,

"Shikenan mu yan kallo ne."

"Muje Yaya ki bani." Taja hannun Yaya, suka shige bedroom dinta, ta karbi hadin a wata robar ruwan nestle, ta ce zata je tasha a daki, da wayo dai ta lallaba yayan ta raba ta dashi, sannan taje ta ajiye a kitchen din part din Aunty ta dawo aka shiga yi mata gyaran jikin.

***Mama na zaune suna waya da Aunty Nafi tana sake kasheda mata kar ta kuskura yarda da zabin da akayi ma Tariq gwara ko Salma ce su hada su. Shiru Mama tayi tana jin ta, duk da dai bata son jiddah amma ba zata yi wa Tariq irin auren da Baba yayi masa ba, zata bashi damar ya kawo wadda yake so da kansa tunda ba wai ta gamsu da tarbiyyar Salman bane duk kuwa da alakar su.
Sallama sukayi ta katse kiran ta kira Tariq din da Ishaq ya jashi zuwa yin siyayyar abubuwan da zasu taho dasu gida, da fari ki yayi amma da yayi convincing dinsa sai ya yarda ya bishi. kayayyaki ya sissiyo nasa sai kuma ya siya ma yan gidan nasu kaf har Aunty da Usman. Suna hanyar dawowa kiran Maman ya shigo, ya daga yana gyara Bluetooth din dake kunnen sa

"Tariq." Ta kira sunan cikin yanayin nuna kaguwa

"Mama barka da gida, kuna lafiya?"

"Alhamdulillah, ya shirye-shiryen tahowa?"

"Gashi fa, muna yi yanzu muke komawa gida daga shopping "

"Masha Allah, we all can't wait to see you "

"Nima Mama."

"Um um kai ai baka damu ka ganmu ba, tunda kiri-kiri kaki zuwar mana ko hutu ne, nima kuma ka hanani zuwa."

"Toh gashi Mama yanzu har an gama zan dawo ma."

"Still dai."

"Toh I'm sorry, ba zan sake ba."

Murmushi tayi me sauti ganin yadda Tariq din yake waya da ita, tabbas akwai sauyi sosai a dangane da mu'amular sa, yanzu kuma an kara girma dole abubuwa zasu chanja

"Shikenan toh, sai kun isa gida ka kirani akwai sakon kayan da nake so kaje ka siya ma sisters din ka."

"Ok Ma, ina komawa zan kira."

"Allah yayi maka albarka."

"Amin."
Ya amsa cike da jin dadin addu'ar da tafi masa kowacce.

***Sati biyu ya rage bikin gidan duk shirye-shiryen da ya kamata ayi duk an yi hatta wajen da za'a yi shagalin an kama komai dai cikin tsari dan ba karamin shiri akayi ba. Duk da kudurin Mama na ganin Tariq ya ki Jidda hakan be hana ta cigaba da duk shirye-shiryen tare da jiddan ba, hakan ma cikin kissar tace dan bata son ta sake nunawa Baba itace bata so, tafi so Tariq din yazo da kansa wanda tasan tilas ne yaki jidda.
Su uku ne a motar, Ya Fauwaz da yake tukawa, Umaima na gaba sai ita da Ya Safiyya a baya, hira suke gwanin sha'awa dan ita babu abinda zata ce tsakanin ta dasu sai godiya musamman tun bayan da aka daura auren ta da Tariq suka sake jan ta a jiki sosai.
A gajiye suke dan duk abinda suka san zasu bukata sun siya dan ba kuma sake fita zasuyi ba inji Mama, ita dai Aunty tana gefe tana kallon ikon Allah dan dai duk wani abu da ya kamata ayi wa Jiddan Mama da Yaya sun dauke, sai dan abinda ba za'a rasa ba. Kayan ta ta dauka a booth, Ya Fauwaz yayi saurin karbewa yana girgiza mata kai

"So kike Ya Tariq ya dawo ya hukunta ni kenan, na bar her royal highness da daukar kaya."

"Gaskia dai Ya Fauwaz." Umaima tace tana dariya

"Muje na kai miki dan nasan idan ya dawo gobe duk sai ya bincike mu yadda mukayi treating dinki idan ya samu daddad'an labarin nan."

"Ya Fauwaz kai ko?"

"Ai gaskiya ce." Safiyya tace suka saka dariya. Tare suka jera dashi yana sake tabbatar mata da yakinin sa na yadda zata sace zuciyar Ya Tariq a lokaci daya, duk da akwai tsoro sosai a k'asan zuciyar ta amma duk sanda Ya Fauwaz ya bata hope sai taji tana samun kwarin guiwa, sau tari ta kan hau kan profile dinsa tana duba shi, ta kan ganshi online wani lokaci duk da ba kasafai ya cika hawa ba, tasha gwada yi masa magana sai ta kasa, tayi hakuri sosai sai gashi har lokacin yazo.

Ajiye mata kayan yayi a falon Antyn, ya juya yana sake jaddada mata gobe ne fa, murmushi kawai tayi ta tattare kayan ta wuce dakin ta, ta ajiye su ta shiga toilet don yin alwala.

***Washegari da wuri kowa ya tashi a gidan, cikin shirye-shiryen tarbar shi, Mama ta kasa zaune ta kasa tsaye da gaske take cike da farin cikin dawowar sa, har ta gaza boyewa, sai da Baba ya tsokane ta. Bangaren Hajiya Yaya ma tana cike da farin cikin dawowar sa, wanda ko ba'a fada ba a cikin jikokin nata tafi son Tariq din, saidai yanayin sa tasa suke rigima sosai har ka zata ko bata yin shi ne.

Tsaye take a kitchen ita da Aunty suna shirya masa girki, mai rai da lafiya, baki daya ta bada dukkan attention dinta akan girkin, duk da sun fara da wuri amma har aka zo tafiya airport dauko shi bata gama ma bare ta samu tayi wanka, Amira ce ta leko kitchen din da ganta da doguwar riga zurum tana ta aiki ta kwashe da dariya

"An shirya fa, har ma mun fito nace bari na leko ki."

"Ai dama ba zuwa zan ba Amira, sauri dai nake naje nayi wanka."

"Auw har Ya Fauwaz yace ki fito."

"A ah kuje, sai kun dawo."

"Ok matar Yaya."

Dariya sukayi a tare ta fice ita kuma ta maida hankalin ta akan aikin, ganin lokaci na tafiya ya saka aunty cewa taje tayi wanka zata karasa ita da Badiya me aikin ta. Wanke hannun ta tayi a sink ta fice da sauri ta fada toilet.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (27)

***Chan wajen gate ya nufa, fuskar sa a hade,ya tambayi ina driver, ya taso da sauri ya bud'e masa motar ya shiga, ya tada motar suka fice daga gidan. Jingina kansa yayi a jikin kujerar ya saka hannu zai ciro wayarsa ya tuno ya barta a daki sanda Fauwaz yake masa magana, tsaki yaja kawai ya maida kansa da yake sara masa, daga dawowar sa sai a nemi a hanashi sukuni haka kawai, ya rasa me yasa Yaya take son kure shi, idan ba haka ba har shine za'a yiwa aure irin wannan? Shi da ko tunanin rayuwar auren ma baya yi yanzu yake son settling ya fara neman yarinyar ma.
  Yasmin ce ta fado masa, ya tuna sanda ta rike masa suitcase tana hawaye, wai a dole bata so ya tafi, shi dariya ma ta bashi yadda ta hakikance ita tsakani da Allah take son shi, bayan yasan irin wannan soyayyar bata existing sam. Shi be ma yadda da irin wannan ba, kamar wani wason kwaikwayo haka ya dauki abun, yawo sukayi tayi akan street din Abujan daga wannan su sauka wannan sai da ya gaji kuma ya tuna Baba zai iya dawowa ya nemi shi sannan yace su koma gida.
   Baba na harabar gidan tare da wasu mutane suka shigo, zuciyar sa ce yaji ta dan ragu da zafin da take masa ganin Baba, kallon motar Baban yake har suka samu waje sukayi parking ya fito da saurin sa, ya nufi wajen su. Fuskar Baban ce ta fadada da fara'a ganin Tariq din.

"Tariq..."

"Baba barka da warhaka."

Ya russuna k'asa yace

"Ina wuni?"

"Lafiya lou bakon turai."

"Ina wuni?"

   Ya gaishe da wadanda suke tare da Baban, suka amsa sai sukayi masa sallama suka tafi. Hannun sa Baba ya kama ya rike suka shiga takawa zuwa part din Yaya suna tafiya yana tambayar shi hanya da sauran abubuwan da ya kamata ya tambaya.
   Tare suka shiga Tariq kamar ya kwace ya gudu dan baya son abinda zai hada shi da Yaya a wannan lokacin, so yake ma yaje yayi tunani sosai akan maganar da Fauwaz yayi masa. Hannun sa da yake cikin na Baban ya kalla kamar ya kwace ya daure dai suka shiga falon. Tana kwance tana gyangyad'i suka shigo tayi firgigit ta tashi pretending kamar ba bacci take ba

"Yaya bacci kike ne?" Baba ya tambaya

"Um um, ba bacci nake ba, kallo ma nake abina."

_"Musun me bacci."_ Tariq yace a k'asan makoshin sa

"Dunkum sabon ango ashe tare kuke."

Gimtse fuska yayi, Baba kuma yayi dariya ya zauna ya gaida Yayan sannan Tariq ma ya gaishe ta da k'yar.

"Wai Yaya ya akayi ne ranar baki bani labarin jirgi ba, ya kika ji?"

"Jirgi ni Hajara, ai ban hau ba, su dai chan suka hau ni da Jidda muka bi hanya nan da nan muka isa mu ma."

"Baki hau jirgi ba Yaya? A ah ko dai bacci kikayi dai bayan kun shiga?"

"Da ido na biyu sarai ni banga an hau jirgi ba."

"Ah toh inaga hakan ne, toh shikenan."

"Yawwa." Tace tana gyara daurin kallabin ta

"Dama kawo miki shi nayi Yaya, gashi nan tunda Allah yayi ya dawo, sai a sanar dashi abinda yake faruwa ba sai an wani jira ko bata lokaci ba."

"Tabbas, tunda dai yarinyar nan dai tayi hakuri zaman jiran shekara guda ai ba wasa bane."

"Tariq..."
Chapter 32 · 0% Book details