← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 76

Sashe 18

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dora tana yi wa jiddan murmushi abinda yayi matukar daure mata kai, toh ko dan dama bata cika magana bane shiyasa Jiddan ta zata ko bata da kirki ne? Jikinta a sanyaye ta zauna kusa da Maryam, sai Salma ta tashi fuuuu ta fice daga dakin.

"Yarinyar nan bata da hankali, amma zan yi maganin ta."

Safiyya tace tana mikewa, ta bar musu dakin ya rage daga Jidda, Amira, Umaima, Maryam sai yar gidan Aunty Mimi Nu'ayma. Sukayi zaman su har jiddah ta saki jikinta sosai dan dama Salma ce tasa ta darare da farko, tare suka ci abinci a dakin sukayi zaman su har lokacin tafiyar su Nu'ayma yayi Salma ta shigo tana kumbure-kumbure tace tazo su tafi. Biyo ta sukayi ya rage saura jidda a dakin tayi zaman ta, suna fita suka ji Aunty Nafi na fada

"Akan wata bare Safiyya zata wulakanta yar uwarta yanzu Ya Aisha"

"Kiyi hakuri zamuyi magana, duk wannan ba abin tada hankali bane dan Allah."

Mama da bata cika son irin wannan abubuwan ba, ta fada tana kallon gefen da Safiyya take akan dinning tana duba wata magazine kamar ba da ita ake ba. Ashe biyo Salman tayi ta rar rankwashe mata kai tace kuma kar ta sake musu irin haka, shine harda kukan ta, ta fadawa uwarta shine ita kuma taji haushi take ta banbami.

***Babban Album jidda ta hango akan wata akwati, ta tashi ta dauko ta bude ta fara kalla, hotunan su ne tun suna yara zuwa girman su, sosai wasu hotunan suka bata dariya, ta dinga dariya tana kalla, har tazo kan hotunan Ya Fauwaz da Ya Tariq, tsayawa tayi tana kallon hoton idanun ta akan sa, fuskar sa kamar sanda yazo part din Antyn a duk hotunan, kamar dole akayi masa baya so. Taba kofar dakin taji anyi, ta tsaya da abinda take tana kallon kofar, turo kofar Safiyya tayi ta shigo tana kallon hannun Jiddan

"Kina ciki dama jiddah?" Tace tana zama daga gefen ta, cikin rashin sakewa Jiddan tace

"Ina ciki hotuna nake kalla."

"Kin ganmu muna yara kanana ko?" Tace tana murmushi

"Amira duk tafi bani dariya."

"Ai Amira muguwar mummuna ce taana yarinya, ni da Ya Tariq ne kawai dama masu kyau."

"Gaskiya."

Tace tsakanin ta da Allah dan safiyyan kamar su daya da Tariq din hatta yanayin shirun su da yadda suke magana.

"Bari kiga sabon Album din kwanan nan." Ta tashi ta dauko mata sabon da suka yi ranar graduation din ta, ta dora akan kafar jiddan ta bud'e mata

Shine a farkon page yana sanye da dogon jeans da farar t-shirt, fuskar sa sake yayi murmushi wanda yayi matukar yi masa kyau,

"Dama yana murmushi?" Ta samu kanta da tambaya

"Kai sosai ma, sai dai ba kowa yake ma ba, wannan ma ni na saka shi yi wallahi."

Bata ce komai ba, ta bude next page ta cigaba da kalla, kusan dukka hotunan su ne shi da Safiyya, sai wanda Safiyyan da su Amira amma nasa yafi yawa. Hotunan sun yi kyau dukka kamar zaka yi musu magana su amsa ta ciki dan yadda ya dauku sosai.

Dawowa sukayi daga rakasu suka tarar da jiddan tana kallon hotunan suka zauna aka cigaba da kalla tare ana tuna baya,wanda zaa yi dariya ayi

"Kinga na Ya Tariq yana karami?" Maryam tace tana dariya

"A ah." Ta girgiza kai

"Ya Sofy ina album din Ya Tariq dan Allah."

"Salon kuyi masa dariya,ajiya ya bani ba zan baku ba."

"Dan Allah jidda ce zata gani, Yaya boss yana karami."

"Noo ba zan ci amana ba."

"Jidda kice kinaso ki kalla zata dauko, musha dariya"

" A'ah kar a dauko ni dai ba ruwana."

"Kin kwafsa, da mun sha kallo wallahi."

"Dan dai baya nan ne, kunsan da baku isa ba wallahi."

Ya Safiyya tace tana dariya, abinda ya sake bama jiddah mamaki ganin yadda ta sake tare dasu kamar ba ita ba.

Har bayan magriba tana wajensu,dan ji tayi ma kamar tayi ta zama a chan yadda taji dadin yinin ranar. Sai da Aunty ta turo tazo sannan suka rankaya tare da Amira suka koma wajen aunty, basu ga Mama a falo ba kamar ma bata nan dai.

***Kwana biyu Baba ya kara ya dawo cikin rakiyar mutane da yawa, a hanya sukayi magana da Tariq dan tun ranar be samu kansa ba, tare yake da sababbin masu kula dashi DSS har su hudu, sai wasu motocin, dole zaman sa a unguwar ba zai yiwu ba musamman yanayin aiki dole ya zama yana kusa da Mr President sannan kuma da yanayin yadda kasar ta zama dole yanzu sai an samu wadanda zasu zauna da family dinsa su kula dasu kafin ya tattara su dukka su koma chan saboda security purpose.
Gidan a cike yake taf, Baffa da Iya Lami sunzo duk da be so tahowa da ita ba amma ta nace a dole sai tazo ba yadda ya iya suka taho tare har da Innar su Saude da Sauden, duk sun zo taya Aunty murnaz Baffa kuma Baba. Kafin isowar Baban gidan ya cika ba masaka tsinke hatta bangaren Yaya a cike yake da yan uwanta da na Malam, Mama ma wajen ta aciken yake da kawaye da yan uwa. Mom din su Safeera ma tazo da kanwar Daddy da Safeeraan. Aunty ce fa gayyato su duk dai dan itama bangaren ta kar ya zama babu kowa tunda su ba yawa ne dasu ba, ba kuma ta san mutanen anan din ba
Duk girke-girken da akayi Mama ce ta saka akayi order ta fitar ma da Yaya na part din ta haka ma aunty sannan ta bar nata a wajenta. Ta shirya cikin shiga ta alfarma wadda tayi bala'in karbar zubi da tsarin ta, dama Mama yar gayu ce tun da bare yanzu da likafa ta daga ta zama matar minister wadda take jin a yanzu ne tayi daidai da level dinta.
Itama Aunty tayi shigar ta daidai da ita tayi kyau kuma abinka da dama chan kyayyawa ce sai ta fito fes sosai. Iya Lami tana ta zak'ewa a wajen Auntyn duk da taki yarda sam da ita, Jiddah kuwa daga gaisuwa ko kallon ta bata sake yi ba, tayi zaman ta a daki ita da Safeera.
Part din Yaya, Baban ya fara shiga kamar yadda ya saba ya gaggaisa da mutane. Yaya kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha, dan farin ciki. Daga nan ya shiga wajen Mama itama da nata mutanen suka gaisa sukayi masa Allah ya sanya alkhairi, sannan ya shiga wajen Aunty a karshe. Daga nan ya dawo wajen su Baffa da aka saka rumfa a harabar gidan suna zazzaune a wajen.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: __SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (14)

***Da sauri ya karasa gaban table din,ya zauna yana jawo system din, ya cigaba da bin lectures din har zuwa sanda malamin ya gama, ya zare headphone din dake kunnen sa ya mike ya tattare komai ya ajiye a gefe ya kashe system din ya zare flash din dake makale a jiki, ya nufi wajen da kayansa suke ya dauko dambun naman da ya taho dashi ya ajiye sannan ya samo chilled juice ya hada ya zauna yana ci yana browsing a wayar sa.
   Ya dade a zaune a wajen har lokacin sallah yayi, ya mike bayan ya zare socks din dake kafarsa ya nufi toilet yayi alwala ya fito ya wuce zuwa dan madaidacin masallacin da yake kusa da apartment din nasu, yana cikin dalilin da ya sakashi karbar apartment din saboda kasancewar masallacin da yake kusa da wajen, baya taba missing sallah duk da ba wai ana kiran sallar bane amma kuma yana amfani da wayar sa yaga time din idan yayi yaje yayi sallar.
    Ajiye takalmin sa yayi a cikin wasu lockers sannan ya dauki wani na shiga cikin masallacin ya saka ya haura sama in da ake sallah, ka'idar su ce baa cika cikin main building din da takalmi sai dai ka ajiye shi a farkon shigowa in da aka tanadi lockers masu kyau kowa ya ajiye nasa a wajen tunda ba wai yawa ne dasu ba, Ishaq ya hango a gaban sahu ya karasa kusa dashi sukayi sallar sannan suka fito a tare, anan yake tambayar sa abinda ya hanashi zuwa lectures yau, shafa kansa yayi kafin yace

"Haka nan naji bana so fita yau."

"Manyan kwari dama ai haka ne, ko basu yi attending class ba lafiya lou."

"Ba wani, kuma ma nayi following online, banbancin mu kawai zama a class din ne."

"Eh haka Mr David yace, kayi joining class din tun daga farko."

"Eh." Yace suna cigaba da tafiya.

"I'm hungry wallahi, ko kana da wani abun naci?"

"Muje ba za'a rasa ba ai."

Yace sanda suke haura stairs din maimakon lift, ba ko yaushe yake bin lift din ba musamman idan ranar be wani yi exercise sosai ba sai ya hau stairs din kawai ko ba komai ya motsa jinin sa.

"Da lift da komai amma ka bamu wahala,."

"Ka motsa jini ai."

"Duk wanda nake yi kullum."

"Ka kara wani." Yace yana manna card dinsa a jikin kofar, ta bude suka shiga ciki, kallon basket din Ishaq yayi kafin yace

"Wannan fa?" Ya nuna basket din

Tabe baki yayi kafin yace

"Yarinyar nan ce ta kawo."

"Yasmin?"

"Oh eh ita."

"Wai kace nazo adaidai, har abinci take kawo maka kenan."

Juyowa yayi da sauri ya harare shi

"This is the first and last time, nasan ba zata sake iyayin kawowa ba."

"Baka da kirki sam, yarinyar nan fa she's serious akan ka."

"She's not my type."

"Then wace type dinka? Kowacce kace she's not your type, sai ka fada mana type din naka muji ai."

Zura mishi ido yayi, be ce komai ba kawai ya girgiza kai

"Ehen ina jinka, fadi muji type dinka."

"Ok, since you insist."

"Ina ji?"

Ya bude basket din ya shiga fito da kayan dadin da Yasmin ta aiko yana jin kamar an sashi a aljanna, ko kallo basu ishi Tariq ba, ya kishingid'a akan couch din dakin yana yin kasa sosai da idanun sa

"I'm all ears."

Hannun sa ya ware kamar me shirin lissafi yace

"Bana son mace ta cika rama da yawa haka kuma bana son tayi kiba."
Chapter 18 · 0% Book details