← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 76

Sashe 59

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace tana kankame jikin ta, saurin kashe komai yayi ya bud'e kayan sa,ya dauko mata jallabiyar sa, ya saka mata sannan ya taimaka mata ta kwanta, kumburarrun idon ta ya kalla ya girgiza kai lokacin aka soma kiran sallar asubah, alwala yaje yayi yazo yace ta tashi suyi sallah, ta mike tana kin kallon sa ya bata Hijab ta saka har lokacin sanyi take ji sosai sukayi sallar sannan ta koma ta kwanta ya lullube ta ya fito zuwa kitchen ya hado mata tea me kauri ya dawo dakin ya tashe ta zaune tasha sannan ya bata magungunan ta,tasha suma sannan ta koma ta sake kwanciya, bata dade ba baccin ya sake dauke ta.
A gaban gadon saitin fuskar ta ya durkusar da guiwowin sa yana kallon kyakkyawar fuskar ta da tayi ja saboda tsabar kuka, saman dogon hancin ta ya kai hannu wajn wani ja ya taba kad'an yana girgiza kansa, a yadda take fitar da numfashin ya tabbata taji jiki sosai, dama kuma ga ciwon targaden da ya dinga kokarin hana kanshi akan hakan amma be san me ya hau kansa ba, ya kasa hakura bayan yasan tana bukatar tayi healing yazo ya kara mata wani ciwon akan wanda take fama, be kyauta ba sam, kuma zata iya yi masa wani irin kallo. Hannun sa ya kai ya shafi gefen fuskar ta.

"I love you Little Jiddah."

Sai yayi kissing dinta a saman goshin ta, sannan ya mike ya fita daga dakin ganin rana ta fito sosai.

***Wayarsa dake yashe akan kujera tun sanda Yasmin ta kirashi ya ajiye be saka bi ta kanta ba ya dauka ya ga missed calls da yawa, da sauri ya cire lock din ya shiga call log ya tarar da 15missed calls daga Yasmin sai 5 daga Mama sai Fauwaz guda biyu. Duk da dama yasan Mama zata kirashi amma be yi tunanin har missed calls haka ba, kiran ya bi yana kishingid'a a saman kujerar yasa hannun sa yana shafa saman kansa dake masa ciwo sama-sama.
Bata dauka ba har ta katse ya sake kira nan ma no answer sai kawai ya ajiye wayar yana tunanin yadda zasu kwashe da maman yana kuma fatan ta fahimce shi ko yaya ne. Wani tunani ne yazo masa sai ya sake daukar wayar ya kira Fauwaz bugu daya ya daga.

"Ya Tariq ina ka shiga?"

"Fauwaz, bacci nayi na bar wayar a falo naga miss calls din Mama da yawa, hope lafiya?"

"Ba kalou ba wallahi, akwai babbar matsala."

"Toh! Me ya faru?"

"It's a complicated case wallahi, ni dai da zaka zo gidan yanzu kawai."

"Jidda bata jin dadi ba zan iya barin ta ba, she needs me."

"Ayya, Allah ya bata lafiya, kaga Maman ma gasu nn sun fito ita da Aunty Nafi da Salma, bari naji zan kiraka."

"Ok, kace wa Maman na kirata bata daga ba."

"Okh ." Yayi hanging yana nufar wajen su,

"Mama,fita zakuyi?"

Wani kallo tayi masa ya sunkuyar da kansa k'asa dan yasan halin da Maman take ciki ba karami bane ba

"Tariq be kiraka ba?"

"Ya kira, ya kira ki ma baki daga ba."

"Good, idan ma yayi hakan ne dan kar mu hadu ni yanzu zanje har gidan nasa na same shi."

"Gida kuma Mama? Why not ki bari yazo, za'a iya solving issue din nan ba sai kinje ba."

Kallon shashen da Aunty Nafi da Salma ke tsaye tayi ranta ya kara baci idan ta tuno da abinda Salmar tace wanda tasan sharri ne kawai tayi wa Tariq din kuma da tainakon Nafin da tasan haka zasu yi mata da tun farko bata yarda da shawarar Nafin ba.

"Ina Sam?" Tace tana share maganar Fauwaz din, da sauri ya karaso ya duka ya gaishe ta,

"Muje."

"Mama bari na kaiku."

"Zaka iya biyo bayan mu, ku shiga muje."

Tace wa aunty Nafi ta shiga ita,zagaya wa sukayi Salma ta shige chan baya, security daya ya zauna a gaba sai Mama da Aunty N a tsakiya. Da sauri Fauwaz ya nufi wajen motar sa ya shiga yana kiran Ya Tariq din a waya amma sam taki shiga, key yayi ma motar ya bi bayan su yana cigaba da gwadawa.

Yana kwance a falo lokaci zuwa lokaci yana lekawa ya dubo Jiddan amma sai yaga tana bacci, sai ya dawo. Har bacci ya soma daukar sa yaji ana knocking a chan kofar main entrance din, Godiya ce ta fito daga kitchen taje ta bud'e sai ya mike ya fito daidai lokacin da Mama, Aunty Nafi, Salma sai Fauwaz dake bayan su suka shigo, da kallo ya bisu irin kallon mamakin nan, kafin ya karaso yana nazarin fuskar Maman da take a hade tamkar an mata mutuwa.

"Mama? Welcome."

"Ina ka ajiye wayar ka nake da kiran ka?"

"A falo na barta."

"Good, zauna." Tace tana nuna masa wajen zama ya zauna a darare duk jikinsa yayi sanyi dan be san dalilin zuwan nasu ba

"Salma, maimaita abinda kika fada mana ni da mamanki."

"Na'am?" Tace tana kallon TARIQ din da itama shi yake kallo

"Kiyi magana mana ba kallon sa zaki tsaya yi ba." Aunty Nafi tace tana tamke fuska

"Dama, dama ya Tariq ne."

Saukar da kai Mama tayi wani irin abu na taso mata tun kafin Salman ta yi maganar da ta gigita ta, ta kuma hanata bacci a daren jiya ko runtsawa bata yi ba.

"Muna jinki."

"Dama shine ya ke taba ni yana min wani abu shine jiya da ya dawo ya fara min wata irin magana ni kuma nace bana so sai ga jiddah nan ta fito shine ya kore mu yace mu bar masa gida."

Wajen sakwanni biyar maganganun nata suka dauka kafin su kai sakon zuwa kwakwalwar Tariq wanda ya kura mata ido kawai ya kasa furta ko kalma daya.

"Kaji abinda tace?"

Mama tace cike da kunya da takaicin hali irin na Nafi

"Ya Tariq kana ji kuwa?"

Fauwaz yace ganin kamar be san me ake cewa ba.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (48)

A hankali yanayin fuskar sa ya shiga chanjawa zuwa tsananin bacin rai, cikin kankanin lokaci kamannin sa suka sauya ya koma tamkar wanda be taba dariya ko murmushi ba a rayuwar sa, kallon yarinyar yake yana jin zai iya kakkaryata ya zubar a wajen idan har ya biyewa zuciyar sa.

"Baka ce komai ba." Mama tace tana kallon sa

"Me zai ce? Bashi da abin cewa ai, ni wallahi an cuce ni wallahi an cuci rayuwa ta."

Anty Nafi tace tana fashewa da kukan munafurci, be ko kalli in da take ba, ya cigaba da kallon Salman ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa dan kallon nasa ya fara bata tsoro, ba ita ba har Anty Nafin tsoro ya shige ta ganin yadda kirjin sa yake dagawa.

"Tariq!!!" Mama ta kwala kiran sa, ya juyo a nutse yana kallon ta tar,

"Na'am Mama."

"Baka ji me Salma tace ba?"

"Naji Mama." Yace yana kokarin daidaita calmness dinsa

"Amma ba zaka ce komai ba?"

"Bani da abinda zan ce Mama, in dai har wannan dakikiyar kazamar kuchakar yarinyar nan zata zauna ta tsara wannan maganar kuma ku zo dan tabbatarwa, bani da abinda zance akai."

"Tariq karka yi kokarin chanja maganar nan, kasan dai Salma ba zata maka karya ba ko?" Anty Nafi ta fada ganin kamar yanayin da yake ciki ya sassauta

"Da mahaifiyata nake magana ban sa dake ba!"

Yace mata a fusace, da karfi. Tsit tayi bata kuma cewa komai ba, ya maida hankalin sa kan Mama ya cigaba da magana

"Idan har yarinyar nan ta kara minti daya a gidan nan wallahi wallahi sai na ajiye alaka da komai na kakkaryata na zubar a wajen nan,."

"Saboda baka son gaskiya ko? Wallahi ba zan yarda dake ni sannan a hanani kuka ba, wallahi mahaifin ka zan gyayawa, ko ka auri Salma wallahi ko na fada masa, kunsan dai dan siyasa ne baya so sunan sa ya baci ko?"

"To hell with you!" Ya dake mata tsawa

"Ki fadawa duk wanda zaki fadawa wallahi, I don't care!"

"Fauwaz, take them out."

"Calm down Ya Tariq."

"Su fita nace!"

"Tashi Nafi, ma karasa maganar a gida." Mama tace tana kallon yadda yake huci

"Dole ya auri Salma wallahi dan ba zai lallata min rayuwar yarinya kuma yazo yace ba zai aure ta ba."

"Muje."

Tashi tayi tana cigaba da kumfar baki, Jidda da tun dazu take jin muryar sa a sama ce ta lallabo ta fito sanye da rigar sa sai yar hular da ta rufe gashin kanta,sun tashi kenan ta fito kallo ya dawo kanta, da sauri ta juya zata koma a tunanin ta basu ganta ba, sai jin Fauwaz tayi ya kira sunan ta

"Aunty jidda."

Tsayawa tayi ta juyo cikin matsananciyar kunya ta karaso falon ta duk'a kad'an tace

"Ina kwana?"

A gajarce Maman ta amsa tana kauda kanta dan kallo daya tayi wa Jiddan ta gano wani abu, Anty Nafi ta gaisar amma bata amsa ba sai Salma da ta banka mata harara, suka fice daga falon ya rage saura Tariq din da Fauwaz, zama Tariq din yayi yana tallafe kansa da hannayen sa biyu.

"Ya Fauwaz ina kwana?"

"Lafiya lou Jidda, pls ki kula da Ya Tariq bari na dawo."

Sai ya juya shima ya fice daga falon ya same su har sun shiga mota.

A gaban sa tayi kamar kneel down tana kallon hannun sa da ya tallafe fuskar sa dashi, hannu tasa ta kama hannun nasa ya dago idanun sa da suka rini sukayi jajawur ya zuba mata tsoro ya kamata ganin yadda suka koma.

"Ya kike jin jikinki?" Ya fada muryar sa a dashe kamar wanda yasha wani abu

"Naji sauki."

"Ok."

"Baka da lafiya ne?"

"I'm furious Jiddaaaa."

Sai ya saka hannu ya jawo ta jikin sa, ya rungume ta ko zai samu saukin abinda yake ji.

Fauwaz ne ya dawo ciki sannan ya cikata yana gyara mata jikin rigar

"Jeki ciki kinji? Karki damu."

Jiki a sanyaye ta shige ciki ya kalli Fauwaz yana tashi tsaye
Chapter 59 · 0% Book details