← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 76

Sashe 48

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Tsokanar mu dai kawai kike Yaya."

"Yo Allah ,shima munafukin yana fuffukar baya so baya so ashe duk munafurci ne."

"Me zan samu ne Yaya? Yunwa nake ji."

"Na shiga uku ni Hajara, ba dai horon yunwa yaron nan yayi miki ba, kai ni sai naga ma daga jiya zuwa yau kin fada sai uban fari da kika kara, gaya min gaskiya me yayi miki?"

"Innalillahi, Yaya ba komai fa, kawai dai abincin gida nake son ci, shiyasa, amma a kwana daya Yaya sai mutum ya chanja? Jiya ma fa muna tare."

"Toh ai abun nasa ne, kinsan kan sa da motsi har yanzu, sai kin yi hakuri dai."

"Hajiya Yaya kenan."

"Iya gaskiya ta na fada miki, tashi ki duba kitchen akwai flasks din abincin da Babar taku ta aiko, sai ki zuba ki cika cikin ki."

"Yawwa yanzu naji batu."

Ta mike ta shiga kitchen din ta zubo fried rice da chicken tazo ta zauna tana ci a hankali suna hira da Yaya.
Har magriba tana wajen Yayan sannan su Amira suka shigo suke cewa Baba ya dawo ya saka a kira masa Ya Safiyya da Umaima part din sa, dan yi musu final nasiha tunda har masu zuwa daukar amaren sun fara zuwa. Kira ne ya shigo wayarta, ta kalli screen din taga an rubuta Capt.T, kai tsaye ta gane shine, ta daga a kasalance ta saka a kunnenta

"Ina kofar part din Baba."

"Na'am?"

"Kizo."

"Ok."

"Ba zai shigo nan din ba? Ko da yake ina yaga idon da zai hada dani? Ai be isa ba."

"Hajiya Yaya ta Ya Tariq." Amira tace tana dariya

"Na Jidda dai, wace ni?"

"Ai kece ta karfen."

"Jeki dai dadi miji, daga kira har kin mike jiki na rawa, ba dan jan ajin nan, ko ni da nake ba yar zamani ba na iya jan ajin nan tun zamanin kakanku, shima yasan Dije ba ta wasa bace, shiyasa ya kasa yi min kishiya."

"Yo ai ke Yaya surutun ki kadai sai ya kori kishiya."

Amira tace tana dariya, ita dai jidda fita tayi ta bar su suna gamzawa, ta hange shi tsaye a kofar part din Baban tsaye shi da kaamar Mama, suna magana amma idonsa na kan ta tunda ta nufo su, a tsorace take dan bata yi zaton zai kirata Mama na wajen ba, bata san me zata tarar ba, shiyasa ta dinga jan kafar ta, har ta isa wajen kanta a k'asa tayi sallama, shi kadai ya amsa ta kalli Maman wadda fuskar ta, take a matukar hade kana gani kasan ranta ya kai kololuwa a baci, bud'e kofar tayi ta shige, ya girgiza kai kawai yana kallo na, fuskar sa babu yabo babu fallasa amma ya nuna kamar ransa babu dadi.

"Muje." Yace yana nuna mata hanya, a tunanin ta part din Baban zasu shiga, amma sai taga ya nuna mata hanyar wajen da akayi parking motar, jiki a sanyaye tabi bayan sa, ya bud'e mata bayan motar ta shiga sannan shima ya shiga, sam yazo ya shiga wajen driver ya tada motar suka bar gidan.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (39)

***Cikin yanayin bacin rai Baba ya rufe ta da fada, ta in da yake shiga ba tanan yake fita ba, sosai ran sa ya baci akan abinda Maman tayi, shiyasa ya ki bari a kira Jiddan yace kuma Tariq ya dauki matar sa su wuce gida, ya kuma kafa masa sharadin duk abinda ya faru da ita sai ya basu mamaki shida mahaifiyar sa.
Ranta a bace yake matuka bayan ta dawo ciki dan da Tariq din ya fita bin bayan sa tayi, ta tambaye shi dalilin da zai wulakanta ta haka har ya dauki Jiddan ba tare da sanin ta ba, hakuri kawai ya bata dan be san me zai ce ba, bata sake magana ba ganin Jiddan ta nufo su, sai kawai ta koma ciki in da ta tarar da Baban na yiwa Safiyya da Umaima nasiha. Tana shiga yace su tashi su tafi Allah yayi musu albarka, sai kawai tabi bayan su, suka fito yayi kwafa yana cike da haushin Maman, dan ta kaishi makura a yau zai kuma nuna mata shi yake da iko da ita da Tariq din, ba zai tsaya ta zubar masa da girma akan son zuciyar ta ba.
Tafiya akayi dasu kowacce a nan Abujan zata zauna, duk da bacin ran da Maman ke ciki haka ta daure har aka tafi dasu, sannan tunanin ta ya dawo kan abinda ya faru, da irin maganganun da Baban ya gaggasa mata a gaban yaran.
A daki suka sameta bayan sun dawo daga kai amaren, Aunty Nafi ta zauna a kubin ta, tana kallon yanayin ta

"Wai Yaya me ya faru ne? Ko duk tafiyar yaran ce?"

"Rai na ne a bace Nafi, wallahi."

"Me ya faru?"

"Kinsan wai ashe Tariq tun jiya ya dauki yarinyar nan suka wuce gidan sa?"

Zaro ido tayi

"Ba dai Jidda ba?"

"Ita, ace ya kasa fada min sai yau zanji a wajen ubansu, tsakani da Allah me Tariq yake so ya zama ne?"

"Gaskiya ba haka aka bar shi ba, Tariq din da muka sani daban wannan Tariq din daban, gaskiya an samu matsala, kema Yaya kin yi sanyi da yawa har kika bari haka ta faru, yanzu suna ina?"

"Sun tafi."

"Kika bar su kuma?"

"Ya zan? Baban su yace wallahi komai zai iya faruwa idan nace zan wani abu."

"Tab! Amma gaskiya da matsala, shikenan haka zamu zuba ido kishiya ta mallake miki babban d'a?"

"Ba zai yiwu ba ai, wallahi ba zan amince ba, duk tsoratarwa kawai yake shima, dole na tashi a tsaye."

"Gaskiya dai, ai ba zai yiwu ba."

"Menene shawararki?"

"Eh toh, tunda dai a yanzu ran Honourable ya baci sosai, zai iya aikata komai, ta karkashin kasa zamu biyo musu, tunda dai ke bakya son dan tainakon nan na wajen malamai."

"A ah bana so, wani abun dai daban."

"Yaushe Baban zai yi tafiya?"

"Jibin nan zasu tafi tare da Halima."

"Wannan karon kuma? Ah lallai kinyi sake wallahi."

"Ni duk wannan baya gaba na, ta d'ana nake."

"Toh kawai mu tura musu Salma da Amira gidan, tunda dama hutu suke dukkansu, sauran aikin sai mu barwa Salma tasan me zatayi duk zan dora ta akan komai."

"Kina ganin hakan zai yi? Amira fa bata da aminiya irin ta."

"Duk wannan ba matsala bace ai, ke dai ki bar komai a hannu na."

"Shikenan, dan Allah ayi duk yadda za'a yi, kafin ma a samu matsala wani abu ya shiga tsakanin su, yazo shima ya tattara ya tafi dan inaga a karshen satin nan zai koma Canada, dan naji Baban yana maganar suna ta masa mail ya ma kara sati,."

"Toh kinga in da aikin ki zai shigo, ki masa lamfo-lamfo ki nuna masa komai ya wuce zaki kula da ita ko baya nan, daga nan ita kuma sai mu nuna mata shege."

"Shikenan zan daure, yanzu ke yaushe zaki koma?"

"Ai ban ga ta tafiya ba, sai naga yadda aka yi, ba a barki ke kadai ba, amfanin dan uwan kenan."

"Toh kar mu bar Mimi taji maganar nan, zata bata komai."

"Wa?* Ta kama bakinta

"Ba zata ji komai ba, uwar iyayi sai ta hau fada mana magaana, kyaleta kice wani taro zan rakaki."

"Shikenan, Nagode sosai, sai kuyi magana da Salman, shi kuma Tariq din nasan yadda zan masa, Dan ba karamin aikin sa bane suna zuwa ya koro su wallahi."

"Zai aikata, musamman yanzu da baya ganin kowa sai figaggiiyar yarinyar nan, me zubin yunwa."

"Wallahi ko ganin ta kusa dashi bana son yi, dan dai yaran yanzu ne, baka isa dasu ba."

"Ba a hayyacin sa yake bane aj."

"Toh Allah yasa ya dawo hayyacin nasa, kar a samu matsala kiji ana amai an samu juna biyu."

"In sha Allah hakan ba zata faru ba, ina Allah ma ya kiyaye."

"Toh Amin." Tace a sanyaye
Chapter 48 · 0% Book details