← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 76

Sashe 39

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tambaya ta kake me ya faru? Baka san me ya faru ba Tariq?"

Girgiza kai yayi

"Allah Mama ban sani ba."

"Menene hadin ka da yarinyar nan?"

"Mama?"

"Eh menene hadin ka da ita? Daga ina kuke ma tukunna? Kar dai kace min? Noo ba zai yiwu ba."

"Dan Allah ni dai Mama ki kwantar da hankalin ki."

"Ya zan kwantar da hankali na wai? Hu? Taya kake so na kwantar da hankali na ina ganin ku tare? Kasan abinda hakan ke nufi? Na rasa ka kenan,."

"Ba zai lasting ba mama, just give me sometime, bana so akai na ku samu matsala da Baba."

_"I'm doing it for Baba."_ Ya fadawa kansa da kansa k'asa-k'asa amma sai yaji kamar zuciyar sa bata karbi uzurin sa ba, so yake dole ya karfafa kansa cewa duk ma abinda yake saboda a samu maslaha a tsakanin iyayen sa ne, shi he has nothing to do with her, ba daidai dashi bace sai ya karyarta ma ai, amma kuma sam zuciyar sa taki bud'e masa kofar da zai aje irin wannan uzurin da har zai samu wajen zama a cikin zuciyar tasa

"Don't go far na gaya maka toh, Halima da yarinyar are cunning, idan baka yi wasa ba you will end up..."

"Nooo Mah..." Ya katse ta

"I don't think hakan zai faru, in sha Allah hakan ma ba zai faru ba."

"I hope so, fita zan amma ganin ku tare na ji ma na fasa, we only have few days sai kayi duk yadda zakayi kafin a shiga cikin bikin, bana son kuma silly excuse dan ba zan karba ba."

"In sha Allah." Yace amma kuma sai yake jin kamar ba zai iya aikata abinda Maman take so ba, amma kuma why not? Shi ai ba son yairnyar yake ba.
Fita yayi ya nufi bangaren su, yaje yayi wanka sannan yayi breakfast ya zauna yana hutuwa a falon har Fauwaz ya shigo.

***Kamar munafuka haka ta shiga part din nasu, aunty na zaune a falon taji kamar ta nutse saboda tsabar kunya, kanta a k'asa ta shiga ciki, ta gaida Auntyn tayi saurin shigewa dakin ta, tasa key ta kwanta rigingine tana kallon pop, ta kasa tantance yanayin da take ciki gaba daya,ta kuma rasa a wanne mataki zata ajiye abinda Ya Tariq din yayi, tunda ya nuna mata time kawai yake jira yayi ending marriage din nasu, kila dai kawai so yake ya dagula mata lissafi ya barta da ciwo a zuciyarta, zatayi duk yadda zatayi ba zata sake bari su hadu ba, ballantana har wani abu makamancin hakan ya faru. Message ne ya shigo wayar ta sai a lokacin ta tuna da wayar, baki daya kamshin turaren sa take kamar wadda tayi wanka da ruwan turaren, duk ya cika mata kofofin hancin ta, wayar ta dauko ta shiga message din sai taga Ya Fauwaz ne

_"I will take over daga nan, kamar yadda nayi miki alkawari Ya Tariq sai yazo da kansa ya kawo kansa wajen ki, ki barmun komai, ke dai kawai kiyi avoiding nasa."_

Murmushi tayi kawai ta goge text din, dan ita bata taba tunanin Tariq din zai yi abinda Fauwaz din yace ba, bata ki ba idan baya hayyacin sa ko kuma dai wani babban al'amari, itama tun farko tayi gangancin hada kanta dashi, banbancin su yayi yawan da zai yi wuya ya iya sakkowa zuwa level dinta. Har magriba tana kunshe a daki sau biyu Amira na zuwa suje wajn Yaya amma kemaimai taki, gobe za'a kawo musu ragowar wasu kayan kamshi na turara jiki wanda na kwana uku ne kachal zaa musu daga nan zaa shiga hidimar bikin wanda bata dauke shi yanzu da muhimmanci ba dan bata san matsayin ta a wajen wanda ake yi domin shi ba.
Da safe Amira tazo su tafi wajn Yayan da k'yar sai da Aunty ta bata rai sannan ta amince amma da cewa tayi ba zata ba ta daina zuwa, duk da Amira tasan dalilin amma basu taba maganar ba dan jidda zurfin cikin ta yayi masifar yi mata yawa, ganin bata fada mata ba yasa ta ki mata maganar gaba daya.
Ita aka farawa dan Ya Safiyya da Umaima basu ma tashi ba, ana gama mata ta sulale ta koma nasu part din dan tayi alkawarin ba zata yarda su hadu ba. Tana shiga Aunty ta tashi tana rike bakin ta kamshin irin mayatataccen kamshi ne me dadin gaske, kudi sosai aka kashe dan ita kanta daga wani state din tazo matar bayan wacchan ta gama musu ta tafi.

"Kinji kamshin da kike Jidda?"

Kunya ce ta kamata, ta rufe fuskar ta, da tafin hannun ta tana dariya, kod'a ta Aunty ta dinga yi ita dai kawai dariya take cike da kunyar Auntyn dan abinda ya faru jiya.

***Kwana biyu bayan sun dawo yana ta zuba ido babu ita babu alamar ta, sau wajen uku yana zuwa part din Yaya amma sai ya tarar bata nan, har sai da Yaya ta gaji tace wai lafiya yake mata safa da marwa a gida ne? Fita yayi kawai be sake dawowa ba, chan anjima ya tafi wajn Auntyn amma sai suka hadu da Auntyn a hanya zata fita, ya juya bayan sun gaisa ya samu waje ya zauna yana saka ido ko zai ga fitowar ta amma shiru har dare babu ita babu alamar ta. Be san dalilin da yasa ya damu da son ganin ta ba, shi dai kawai yaji yana so ya ganta ko ma ba zata masa magana ba. Kamar ya koma wajen Auntyn amma sai ya hakura ya fasa. Da safe ya sake saka ido amma shiru, a lokacin ne kuma gidan nasu ya fara cika da mutane, yawanci yan uwan Mama ne suka fara zuwa a ranar, silalewa yayi ya bar gidan dan baya son su ganshi kwata-kwata.

***Suna zazzaune dukka yan matan a falon farko su kuma su Mama na ciki, Salma ce tace tambaye Maryam

"Wai Ya Tariq baya nan ne?"

"Wa? Ya Tariq din zaki tambayen? Wallahi ban san in da yake ba."

"Har yanzu Ya Tariq baya son mutane, wallahi na matsu na ganshi naga yadda ya chanja."

"Ganin Ya Tariq sai kin cika Form, da dai Jiddaa ce." Amira tace tana dariya, bata fuska Salma tayi, taja tsaki tana mikewa

"Sai ana maganar mutane kuna kawo mana maganar wata chan dan Allah."

"Kinyi maganar mijin ta ai dole ayi maganar ta."

"Wai miji, tab!" Ta kwashe da dariya

"Kina mamaki ne?"

"Ba dole ba, dan Allah me ya Tariq zai ci da yarinyar nan? Yarinyar da aka taimakawa aka mayar mutum sai shegen girman kai ita ba yar uban kowa ba."

"Aiko baki san jiddah ba."

"Bana son ma na santa."

"Toh gaskiya ki bar maganar nan kar ma taji wallahi, kinga abinda kika taba yi mata din nan."

"Ai ku kome za'a ce akanta bakwa gani, sai kuyi tayi."

Turo kofar yayi, ya shigo fuskar sa a tamke,ya dan ji maganganun da suke sama-sama ya kuma fuskanci abinda suke magana akai, shi yasa ya tsani taron mata dan babu yadda za'a yi su hadu su tashi ba su tada fitina ba. Gaishe su sukayi a kusan tare duk sun rude Allah yasa be ji me suke cewa ba, be amsa ba yayi wucewar sa dan dama Mama ce tace yazo ya gaida su Aunty Nafi dasu Aunty Mimi, da ba dan haka ba, da ba zai shigo ba. A tsaitsaye ya gaishe su, ya fito yazo zai wuce Salma tayi tsagal tace

"Ya Tariq ina wuni?"

Ko kallon in da take be ba, yayi ficewar sa, yana fita su Ummi suka kwashe da dariya, kamar ta kurma ihu haka taji dan kunya. Dama Aunty Nafi ce ta saka ta, tace tayi kokarin shige masa,amma dan wulakanci ko gaisuwar ta be amsa ba bare tasa ran zai kalli in da take. Tsokanar ta suka dinga yi ta rasa ina zata saka kanta sai daki ta gudu saboda borin kunya.

***Shi baki daya baya jin dadin zaman gidan, a matukar takure yake gaba daya da zaman waje dayan gashi ba wani sanin wurare yayi a garin ba dan ma dai yana da saurin gane waje kuma yanzu an cigaba akwai map, gashi Baba yace dole sai ya kara wasu satittikan kafin ya tafi, Mama kuma ta saka shi a gaba tana so taji ya ake ciki, gashi ya rasa yadda zai ko wulgawarta baya gani sau biyu da aunty tana part din Baba yana zuwa ya murda kofar dakin ta amma a rufe zai ji, baya kuma magana yake juyowa dan baya son ta raina shi ko taga kamar ya damu da ita ne, so yake kawai yaga ta daina kukan ko har yanzu tana yi? Gashi ya rasa solution bayan yayi mata alkawari itama, gashi zuciyar sa ta hana shi kemaimai da ya fara tunanin yadda zai yi sai kawai yaga ta fara hasaso masa Jiddan.
Wajen Yaya ya nufa duk da itama jama'ar ta sun fara zuwa, wanda dama duk suna burin zuwa Abujan sai kawai Baba yayi amfani da damar nan aka ce duk me son zuwa ya shirya, aikuwa suka dinga tururuwa kafin kace me gidan dame d'am da mutane. Tun a kofar shiga yaji hayaniya sai fasa shiga ya bari idan dare yayi ya dawo.
Da daddare Baba ya dawo ya kirashi suka zauna yace menene shirin sa akan tarewar jiddaa, shiru yayi yana nazari har sai da Baban ya sake maimaita masa sannan yace duk yadda akayi yayi, dan jim Baban yayi da zai ce wani abu sai kawai ya fasa

"Shikenan, sai ka fara shiri, akwai gidan da zaku zauna, Incase ko baka nan dai muna kusa."

"Nagode Baba, Allah ya kara girma."

"Amin ya Allah, dan Allah Tariq karka wulakanta min 'ya, Dan Allah."

"In sha Allah."

"Kuma inaso kuje kai da ita ku gaida mahaifin ta, sai ka saka muku rana bayan sun gama bidi'o'in nasu na mata."

"In sha Allah zamuje."

"Shikenan Allah yayi muku albarka."

"Amin ya Allah."
Chapter 39 · 0% Book details