← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 76

Sashe 24

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

***Kusan sati guda kenan da zuwan su Isma'il amma babu wani information daga wajen Jidda, sun yi waya da Safeera da sabuwar number ta amma ba wadda tayi wa wata maganar a cikin su, hakan ya kara tada hankalin Ismail ya samu Safeera da magaanar sai kawai ta bashi sabuwar number din Jiddan da bata so ta shiga abun nasu sosai azo a samu akasi tazo tana jin haushin Jiddah. Samun number ya dan rage masa damuwa ya koma daki ya kirata sai dai har ta gama ringing bata daga ba, tana chan kitchen tare da Aunty ta bar wayar a daki tunda dama babu me kiranta daga Amira sai baffan ta, sai kuma Safeera idan tana so tace mata tazo WhatsApp suyi hira. Sake kira yayi ya dinga jera kiran tunanin sa tana gani ba zata dauka bane dan shine, sai kuma wata zuciyar ta tuna masa ai bata da ma number dinshi bare taki dagawa saboda shi ne, shafa kansa yayi yana mata uzurin kila bata wajen yana kokarin hana waccan zuciyar tashi ta farko tasiri a tunanin sa. WhatsApp yayi login sai ya duba number din yaga tayi registering WhatsApp din sai kawai ya shiga kai ya tura mata kalamai masu dadi da sanyin gaske, hoping zata duba ta bashi time suyi magana ko da a wayar ne ba sai a fili ba. Cigaba da zama yayi rike da waya yana dakon kiran ta ko kuma zuwan ta online wanda yasan tabbas za'a yi dayan biyu, ko ta biyo kiran ko tazo online.
Dakin ta shigo bayan sun gama aikin da Aunty, ta dan gaji dan abinci sukayi na mutane da yawa da za'a fita dashi waje duk da akwai masu aiki amma kuma ya zame musu jiki duk irin wannan aikin tare sukeyi da ita da aunty, kasancewar aunty zata je taga Baffa duk da bata fadawa Jidda in da zata din ba dan bata so tace zata shiyasa ta bar mata aikin ta cigaba da kula dashi ita kuma taje ta shirya, ta fito ita da Usman suka tafi tare da Driver.
Gama aikin kenan an zuzzuba a manyan kuloli ta baro wajen tasan Abu zata karasa sauran aikin a fidda shi, wanka ta fara yi tana shiga dakin, ta maida doguwar rigar dake jikin ta mara nauyi sosai ta kwanta lamo tana jin kanta na dan sara mata, tasan alamun period dinta ne shiyasa duk take moody ga wata irin kasala da take ji, farko da bata gane ba sai da Safeera ta fada mata sannan ta ganar da ita duk abinda ya kamata ta gane ta sani. Pillow ta daga ta ciro wayar ta duba, missed calls din da ta gani rututu ya sakata saurin cire lock din sai taga bakuwar number, da saurin ta, ta kira number back dan tasan duk wanda zai kirata ya san tane sosai kuma irin wannan missed calls din da yawa sai kaji tsoron ko ba kalou ba.
A firgice ya dau wayar da take ajiye da a saman chest dinsa yayi rigingine yana jiran kiran gashi yana da fita zai je ya samu Daddy a office dinsa amma duk sai yaji baya son fita kwata-kwata. Yadda yayi mata saving sunan haka ya bayyana akan allon wayar sa, ya daga ba tare da bata lokaci ba yana manna wayar a kunnen sa sannan yace

"Bari na kiraki Jidda."

Sai ya katse kiran, muryar sa tar a cikin kunnenta, bata kawo shi zai daga ba kwata-kwata, sai tayi sakalo da wayar sanda ta dauki burarin shigowar kiran nasa, ganin zata katse ya sakata katsewa ta dan karata kadan a gefen kunnen ta kamar me tsoron shocking tace

"Assalamu alaikum."

"Jidda ,wa alaikisalam. Ashe zaki daga."

"Ina wuni?"

"Lafiya lou, kina lafiya? Ya gida dasu Aunty?"

"Alhamdulillah."

"Ina kika shiga ne, aka bar wayar bawan Allah tana ta neman agaji."

"Ina kitchen ne."

"Ah kice dai ashe da babbar chef nake magana, shikenan kinga ni lafiya lou."

"Uhum." Tace

"Me kika dafa mana? Nazo na karba dan nasan zai yi bala'in dadi."

"Abincin sadaka ne da akeyi."

"Oh okh, next time sai ace muzo muyi tasting ko? Nasan komai kika dafa zai yi dadi sosai."

Dan gajeren murmushi tayi me dan sauti, hakan ya sake bashi hope ya cigaba da zuba kamar be san yanayi ba, so yake dole sai yayi impressing dinta, ko ba komai a hankali zata saba dashi ta saki jikin ta dashi, shawarar da suka tsara kenan shi da zuciyar sa, ya fara kokarin saba mata da kanshi kafin komai ma yazo daga baya, duk maganganun da yake a gajarce take masa masa kanta na cigaba da tsananta mata da ciwo gashi bata so ta katse shi amma kuma maganar tashi ta ishe ta, sai da yayi ya gaji dan kansa sannan ya hakura yace zai kira anjima. Da sauri ta rigashi katse kiran ta kwanta tana tura kanta cikin filon ta yadda zata rage ganin hasken da yake kara mata ciwon kan.

***Ran Baba a bace yake sosai har Aunty ta gama masa bayani da abinda take so yayi idan Baba yazo masa da maganar Jidda, sai da ya bari ta gama tsaf sannan ya kalleta yace

"Kin gama?"

Sai a sannan taga yanayin fuskarsa, sai taji kamar an dake mata guiwowi, ta tabbatar ba zai goyi bayan ta ba kenan duk da yadda tayi ta kokarin tsara masa maganganun yadda zai fahimce ta

"Kin bani mamaki Innajo, kin bani mamaki sosai."

"Na'am?"

"Yanzu har kece zaki budi baki kice na hana Alhaji auren Jidda? Kenan ma Jidda tana da wani uban bayan shi ban sani ba?"

"Yaya baka fahimce ni ba."

"Bana so na fahimce ki, ni ba butulu bane mara godiyar Allah, me Jidda tafi shi yaron da har zaki dage kai da fata? Wacece Jidda ma? Ke kina ganin ke da yar taki har kun kai wani matsayi da zaku yi abinda kuke so ko me?..."

"Bari na tuna miki idan har ke kin manta, sanda Alhaji ya aure ki ke kanki kinsan ke ba sa'ar auren sa bace, haka yace yaji ya gani ya aure ki ya rufa miki asiri da ni kaina, sannan kika dauki yar taki da kike ganin karan ta ya kai tsaiko da har zaku butulce, kika kai masa ya karba ya rike babu banbanci da Yayan cikin sa, ko akwai banbanci?"

Yace yana kafe ta da ido cikin bacin rai

"A ah." Ta girgiza kai da sauri duk kwalla ta cika mata ido dan bata taba ganin bacin ran Baffa irin yau ba

"Sannan karki manta adalcin Alhaji lokacin da ya rasa Muhammad, kina ganin idan wani mahaifin ne ba shikenan ba kuma maganar auren ku ma zata iya lalacewa akan haka, amma me yayi? Shine ma yake kokarin kwantar miki da hankali ya kuma hana uwar yaron nan yin wani yinkuri, wannan shine mutumin da kike kin dan sa kike ganin be dace da yarki ba tunda ita din yar gwal ce."

"Dan Allah Baffa kayi hakuri, dan Allah."

"Ki barni na gama tuna miki tunda ke kin manta, sanadiyyar waye na samu lafiyar kafata? Idan kin manta sai ki tuna, dan haka..."

Ya nuna ta da yatsa

"Jidda ba 'yata bace, haka kike ba taki bace, yar sa ce dan haka yana da damar yayi duk abinda yaga dama akan rayuwar Jidda, ke ko mutuwa nayi wallahi ba zan yafe muku ba idan kuka kiyi masa biyayya."

"Dan Allah kayi hakuri Yaya, nayi laifi babba, amma dan Allah kayi hakuri."

"Toh kar na sake jin wannan maganar kin daga ta, sannan idan kinsan kin bata masa rai saboda magaanar nan, lallai lallai ki bashi hakuri, sannan ita ma Jiddan zan saba mata idan har tace zata zo min da shashanci."

"Ita bata ma san da maganar ba."

"Idan ma ta sani din, kuma ko yanzu Alhaji yake so ayi auren sai anyi."

"Allah ya huci zuciyar ka Yaya."

"Amin."

Yace a kufule, sum sum sum ta tashi ta fice zuwa gidan su Saude, daga nan bata wani jima ba tayi sallama ta tafi, dan da tasan ma abinda zai faru ne da bata zo ba, sai bayan Baffan ya karanta mata duk abubuwan da ta manta sannan ta dawo hankalin ta, tasan bata kyauta ba kuma dole zata bawa Baba hakuri akan maganar.
Chapter 24 · 0% Book details