← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 76

Sashe 52

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*

_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*

*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (41)

***Ya dade a zaune a falon dan anan ya kusa cinye fiye da rabin daren sa hoping ko zata bud'e amma har ya gaji ya tashi ya shiga ciki ya gyara pillows din dake kan doguwar kujera dake dakin ya kwana dan baya jin hawa gadon.
Juye -juye ya dinga yi yana tunanin maganganun, ya fadi dukka kuma ko kad'an yasan be kyauta ba, ya yi kuma dana sanin furtasu duk da be yi tunanin Fauwaz zai fada mata ba, tunda shi dai ba a gabanta yayi waccar magaanar ta farko ba, ko shine dole yaji babu dadi ita ta ma yi hakuri sosai. Kunya ce ta lullube shi tunawa da yadda ya gama cika baki kuma yazo yana kissing din yarinyar mutane bayan ta san duk abinda yace a kanta. Fauwaz ne ya cuce shi tunda dai da be fada mata ba fuskewa kawai zai yi duk da ya taba fada taji ya san kuma taji din amma maganar bata kai munin wannan din ba.
Da wuri ya tashi bayan ya samu yayi baccin kad'an, ya fito falon ya zauna sanye da jallabiya me gajeran hannu yana jiran fitowar ta. Bayan kusan awa daya da zaman sa sannan yaji ana murd'a key din dakin, yayi saurin dauke kansa daga kallon dakin ta fito fuskar ta a gaba bata ko kalli bangaren da yake ba, ta fice zuwa dayan falon na farko in da ta shiga kitchen ta duba abinda zata duba ta dora ruwan tea, falon ya dawo ya zauna idon sa na kan kitchen din yana jin motsin ta, ya kunna TV pretending kaamar yana kallo ne amma rabin hankalin sa yana wajenta.
Godiya taje ta kirawo tazo ta tayata ta soya musu doya da egg sauce ta dafa ruwan tea me kayan kamshi ta jera akan saman Iceland din ta zuba ma Godiya nata tace taje taci sai tazo ta gyara kitchen din. Karba tayi ta fita daga kitchen din ita kuma ta d'aga cikin wajen oven din zata saka ragowar man da tayi amfani dashi ya shigo ya tsaya daga jikin island din yayi folding hannuwansa a kirjinsa yana kallon bayan ta. Dagowa tayi ta juyo ta ganshi tayi saurin dauke kanta ta dau plate din da ta zuba nata rike da cup tazo zata wuce shi.
Saurin tare hanyar yayi ta dan ja baya da sauri

"Goodmorning tunda baki iya gaisuwa ba."

"Ina kwana?" Tace a gajarce ta nuna masa hanyar

"Zan wuce."

"Fushi kike dani?"

Girgiza kanta tayi,

"Ni ba fushi nake ba."

"Toh menene, kika chanja all of a sudden."

"Ba komai, zan wuce."

"Ba in da zaki, sai kin fada min."

Ajiye abun hannun ta tayi a gefen Iceland din ta wuce gaban sink ta soma wanke kayan da suka bata da ta barwa Godiya ta wanke. Jan daya daga cikin kujerun dake jikin Iceland din yayi,ya zauna ya soma cin doyar daga cikin plate din da ta ajiye a gefen yana shan tea din yana kallon ta, sai da ta gama tatas ya goge hannun ta, ta fice daga kitchen din ba tare da ya sake tsaida ta ba, ya kuma cinye mata abincin da ta zuba duk dan tayi masa magana amma sai ta nuna kamar ma bata san me yayi. A rayuwar sa ya tsani silent treatment duk da shi yafi kaurin suna a wannan bangaren amma ya tsani wani yayi masa sai yaji kamar kansa zai yi bursting, ta gwammace ta zauna bata ci komai ba akan ta yi masa magana kenan. Ransa ne ya dan sosu, a kalla yayi kokari har yake bin ta tana botsarewa bayan be taba hakan ba, zai gwada kyaleta yaga iya gudun ruwan ta.
Wanka ya shiga ya shirya ya fito yana daura links a jikin hannun rigar sa Mama ta kirashi tace Amira zasu zo da Salma gidan su kwana biyu, wani banbarakwai yaji har ya kasa hakuri yace;

"Kwana Mama?"

"Eh kwana, ko kar suzo?"

" A'ah, amma..."

"Mahaifin ku shi kadai kake ma biyayya Tariq, ba zan ce kayi min ba, ba kuma zan hana ba, shikenan ba komai."

"A ah, i'm sorry, kiyi hakuri,sai sunzo."

"Shikenan, yaushe zaka tafi?"

"Nan da kwana hudu ko in sha Allah."

"Ok sai su zauna har sai ka dawo."

"Toh Mama."

Hula ya saka bayan ya gama wayar ya fice daga gidan a tunanin sa hakan sai sa ya manta da ita da tunanin abinda ya addabi zuciyar sa. Kai tsaye gidansu ya nufa dan so yake ya samu Fauwaz yaji yadda akayi ya fada mata maganar da sukayi sannan ya samu Hajiya Yaya.
Sabani sukayi da Fauwaz din yana fita shi kuma ya na shiga gidan. Wajen aunty ya fara zuwa ya gaishe ta sannan yace yana so ayi Jidda lefe kamar yadda akayi wa kowa, mamaki ya bawa Aunty amma a k'asan zuciyar ta dadi take ji, ya soma siyan wasu kayan online amma wasu dai zai bar Auntyn ta siyo. A haka suka rabu ya nufi wajen Mama, bata nan ta fita sai Aunty Nafi da su Amira dake shirin tafiya gidansa wanda ba asan ran Amira zaa baka dan dai tana shakkar Mama ne sannan kuma ba zata bar Salma taje ita kadai ba dan tasan dalilin zuwan ba na Allah da annabi bane, so take ma ta fadawa Ya Fauwaz yasan yadda zai sanar da Ya Tariq din ko Mama ta kirashi kar ya yarda amma sai ji tayi suna waya da Maman kamar ma kuma har ya amince.
A tsaitsaye ya gaida Aunty Nafin da wasu mata su biyu ya fice yana jin tana maganar ya tsaya Salma ta kawo masa breakfast amma yayi biris ya ja dan siririn tsaki dan baya son yadda matar take masa sam, ya kuma lura ita ke zuga Mama dan dazu ya jiyo sautin muryar ta,tana cewa Maman kar ta raga masa idan yaki amincewa kawai sharewa yayi amma ya jita, baya son munafukan mata kuma sai yasan yadda yayi yasa ta tarkata inata tayi gaba dan ba zai iya tolerating dinta ba.

*_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*

_(Where every flavour tells a story .....)_

*_By HAFSAT RANO_*
_(Mother/wife/writer)_

_08030811300_
_IG:Rano_scrumptious_meal_

_INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_

_MU NA YIN:_

*_FUNKASO_*
*_ALKUBUS_*
*_SINASIR_*
*_WAINA_*

*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_*
*_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_*
*_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*

*_LOCAL DRINKS:_*

_HIBISCUS (ZOBO)_
_GINGER_
_AMAANI FRUITY SHAKE_

_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._

_KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._

_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_

_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_

_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*

*ZAFAFA BIYAR BACTH A*

1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*

2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*

3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*

1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*

_Duk biyar 1500_

*______________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)*

2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)*

3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)*

4... _INAYAH_
*(Mamu gee)*

5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*

_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*

*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (43)

***Kad'a kansa yayi zuwa ciki ya rage kayan jikin sa, ya shiga ya watsa ruwa ya fito, ya saka gajeran wando da bakar t-shirt ya nufi dakin nata. Murd'a kofar yayi ya shiga da sallama a ciki sosai. Tana tsaye gaban mirror fuskar ta da ruwa alamun alwala tayi. Takawa ya shiga yi har zuwa daf da bayan ta, suka hada ido ta cikin mirror din ta turo baki tana kokarin barin wajen ya riko ta, ta baya ya zura hannuwan sa ta, ta tsakanin cikinta ya rungume ta a tsakanin chest dinsa.

"Me nayi miki?"
Chapter 52 · 0% Book details