← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 76

Sashe 31

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh." Tace ta rike hannun sa suka nufi shashen da aka nuna musu,tun kafin ta karasa take admiring ginin bare kuma ciki. Wani security ne daga gate ya taso, ya dan russuna ya gaida Auntyn sannan yace ko akwai matsala, girgiza masa kai tayi tace babu, ya bata hakuri ta koma wajen aikin su, gwada tashin Yayan tayi ta dan tattabata sannan ta kira sunan ta, a hankali ta bud'e idon da kad'an kad'an har ta gama gaba daya,sai ta kalli motar da take ciki ta kalli Aunty

"Kar dai har mun karaso ina ta bacci."

"Eh Yaya, ai wai ashe tunda kuka dauko hanya kike bacci zuwan ku kenan, jidda tace kina mota kina bacci shine nace bari nazo na taimaka miki."

"Wai gaskia nasha bacci, awa nawa kenan ina baccin?"

Ta zuro kafarta waje ta sakko, sai taga kamar lokacin suka baro gida, kamar zatayi magana kuma sai ta fasa hango Fauwaz na nufo su da wasu mata kedaru su biyu, kana ganin su kaga karfafa.

"Ah ashe ma ta tashi."

Sai ya juya wajen su yace

"This is the second Madam, greet her."

"Good morning Ma'am."

"Good morning." Tace a takaice

"You can go." Ya ce suka juya zuwa in da suka fito, salati Yaya ta rafka tana tafa hannu

"Yanzu tsabar lalacewar ta kai lalacewa har da arna a gidan nan, na shiga uku ni Hajara yau naga abinda yafi karfi na."

"Kai Yaya, house help ne fa, kuma ba arna bane kawai dai basa jin hausa ne."

"Toh dan tsabar iyayi a rasa irin ma'aikatan da za'a dauka sai wannan zandara-zandaran zawarawa? Wai na shiga uku na lalace."

"Fito na rakaki bangaren ki, kin ga yadda aka miki kuwa, harda katuwar TV ta bango gas fridge dinki cike da kayan dadi, kuma Baba yace zaa dauko miki gwaggo kuyi zaman ku."

"Da gaske?" Ta washe baki tana fitowa gaba daya,

"Muje ki gani, Anty sai mun shigo."

Yace yana rike hannun Yayan, ita kuma Aunty ta nufi part din da jiddah ta shiga, wanda yake da yar tazara tsakanin su da wani hadadden part da yake a tsakiyar gidan wanda aunty ta tabbatar na matar gidan ne.
A tsaye ta samu su jidda suna karewa yar karamar daular tasu kallo, ita kanta Auntyn sai da ta jinina, yayi kyau sosai duk da ba wani katon gani bane, kayan su aka shigo musu dasu, sannan Auntyn ta lallaka dakunan ta nunawa jiddah nata ita ma ta shiga nata.
Amira ce kawai ta rage a gidan duk sun tafi school itama bacci ta koma bayan tayi sallah tunda tasan zuwan su jiddan ba lokacin bane. Wajen sha daya ta tashi, tana sakkowa daga gado tayo waje, suka hadu da Mama a falo tana duba wayarta, da kallo tabi Amiran kamar ta fuzgo ta, ta dake ta haka takeji dan yadda take son jiddah ko ciki daya suka fito sai haka. Bata dai kulata ba har ta fice ta kuma san in da zata dan taga shigowar su gidan ta window, ta kuma ga duk abinda ya faru tsakanin su da Yaya duk da bata ji me suke cewa ba, sakin curtain din tayi kawai ta cigaba da abinda takeyi.
Da sassarfa ta isa part din sannan tayi knocking, Jidda ta zo ta bud'e suka rungume juna cikin tsananin farin cikin ganin juna. Fitowa Aunty tayi da murnar ta, Amiran ta gaishe ta sannan suka kule dakin jiddah ta tayata hade kayan ta waje daya a cikin wardrobe suna yi suna labari, yawanci akan school din da zasu fara zuwa ne next week da kuma yanayin rayuwar garin da yadda zasuyi mingling da yaran manya, ita dai jiddah ta san matsayin ta, bata sa a ranta zatayi rayuwa irin ta su ba, saffa saffa dai kar ta zak'e, duk da haka tasan dole ne ko taki ko taso rayuwar ta sai ta sauya ta sake daukar ta zuwa wani bigire na daban.

***Dawowar su Abuja ya sauya abubuwa da dama daga rayuwar Jiddah, sati daya cif da zuwan su suka fara zuwa wata private university a abujan, course daya sukeyi sai ya zama kullum tare suke duk in da kaga daya zaka ga daya. Sai dai a wajen da Jiddan tasan zai iya shafar matsayin ta na matar aure, wanda ta rike hakan da matukar muhimmanci, bata kuma sakaci bare ta yi wani abu da ya sabawa Allah.
Sau biyu taje gaida Mama a satin da suka zo amma da kyar take amsawa, tayi saurin barin wajen, haka Jiddan zata tashi jiki a sanyaye ta bar part din, na farko aunty ce tace taje ta gaishe ta lallai dan da, da yanzu ba daya bane, akan haka taje amma sai data gwammace bata je ba, haka dai ta daure ta sake zuwa a karan kanta bayan Amira tazo wajensu tayi mata korafin zuwa nasu part din, nan ma dai same abinda ya faru da farko shi ya sake faruwa. Duk abinda ya faru bata fadawa Aunty ba, boye mata kawai tayi a matsayin babu komai dan taga yadda Auntyn take tada hankalin ta akan maganar auren.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (25)

1 year later
Bayan shekara daya

***Abubuwa masu yawan gaske sun faru a cikin shekara gudun nan, Jidda ta samu sauyi na ban mamaki, yanayin society din, da yanayin rayuwar school da mutanen da suke mingling ya taimaka kwarai wajen karuwar wayewar ta, ta goge sosai musamman da dama bata da duhun kai, mutum ce da take kokarin tafiya da yanayin da yazo mata na sauyi cikin nutsuwa da karantar rayuwa.
Rayuwar Abuja ba kamar rayuwar Kano bace musamman da suke mingling da mutane mabanbanta masu gogewa da wayewar sanin rayuwa, duk da haka bata yi wasa da martaba da darjaar da alalh ya dora mata ba, a matsayin ta, na me aure, dan iyakar kokarin ta, tayi wajen kare kanta da duk wani abu da tainakon aunty da nasihar Baffa da baya kwana biyu sai ya tisa mata matsayin ta, da ita din wacece. Bata da matsala kowacce iri ce, duk wani abu na jin dadin rayuwar Baba yana musu musamman ma ita da ya dauke responsibility din Tariq, hatta abinda bata ce tana so ba yi mata yake yi, tsakanin ta da Mama babu shiru daga gaisuwa shikenan shima ba wai tana amsa mata kai tsaye bane. Hakan tun yana damunta har ta hakura ya daina damun ta, bayan Aunty ta zaunar da ita tayi mata bayanin dalilin daukar zafin Maman na rashin sanar da ita komai sai bayan an daura, wanda Aunty tayi mata uzuri sosai dan tabbas tasan baa kyauta mata ba, hakan yasa Jiddah cire damuwar yadda Maman take mata cike da fatan watarana zata so ta, ta karbe ta kamar yadda sauran iyayen miji ke karbar matan yayan su.
Fitowar ta kenan daga wanka sun samu hutun end of semester saboda haka basa fita musamman ma ita dan su amira an samu kafar yawo ba'a zama kwata - kwata, tun wanchan satin labarin dawowar Ya Tariq ya sameta, sai taji gaba daya ta rasa nutsuwa da sukunin ta, duk abinda take tunanin yadda zata kaya take, duk da a kullum Ya Fauwaz da Amira na kara mata kwarin guiwar babu namijin da zai ki ta, a yadda take a yanzu, da haka ta samu dan peace of mind har take biyewa aunty da Yaya wajen shirya ta.
Riga da skirt na cotton material ta dauko ta saka, sai taji skirt din ya matse ta, kusan dukka skirt dinta sun matse ta saboda yadda ta samu sauyi a jikin ta, a lokaci daya, duk da har yanzu bata da wata kiba ta azo a gani amma babu laifi tana da front and back shape dinta me matukar kyau da daukar hankali shiyasa a kullum take cikin shigar kirki haka idan Ya Fauwaz zai shigo takan saka madaidacin Hijab akan kayan ta, ita kanta mamakin kanta take da yadda a lokaci daya ta ciko ta bayan amma cikin ta kamar bata zuba masa komai saboda yadda yake flat a koda yaushe. Zare skirt din tayi da kyar ta dauko doguwar riga plain ta saka kawai ta yafa medium veil a kan dogon gashin ta wanda ta nannade shi ta tura shi a cikin gashin saboda yadda yake sakkowa gadon bayanta duk lokacin da ta sake shi.
Part din Yaya ta nufa in da ake mata gyaran jiki, a chan ta samu su Amira dukkan su tare da me gyaran jikin. Bikin Safiyya da Umaima za'a yi, sai Baba yace sai a hada da na su Jidda din suma ayi shagalin bikin tare, sanda ya fada sai da fuskar Mama ta chanja sosai dan ko sunan Jidda bata so taji ana hadawa da na Tariq, dan dai ma ta shirya nuna musu itama nata karfin ikon akan Tariq din, shiyasa take bin komai a sannu kar ta bata goma biyar bata gyaru ba.
Tare ake musu gyaran jikin da matar da maman ta dauko tayi musu dan shirin biki take gagarumi, kasancewar bata son abun magana shiyasa tace su zauna a wajen Yaya anayi musu dukka a chan dan bata son shige da fice a part dinta.
Tana shiga Amira da Maryam suka hau tafi

"Kinga yadda kike glowing matar yaya, lallai idan Ya Tariq ya dawo sai ya kusan susucewa akan ki, ji yadda fa fataarki ta zama kamar ta jarirai."

Dariya ta saka, ta kai wa Amira dake kusa da ita dundu ta goce

"Kun cika sharri wallahi."

"Allah kuwa, dan Allah Aunty Yagana baki ga yadda skin dinta ya kara komawa ba?"

"Na gani fa."

"Toh kinji dai, ba wai zuga ki muke ba."

"Yo idan ma zugar ce kuyi tayi mana, nan gani da nan bari dumamen mayya."

Yaya ta shiga zancen tana hararar su

"Kai Yaya, me yayi zafi har da bakar magana."

"Anyi din, iyayi ne ni bana so." Tace tana yatsine fuska.

Harara ta Maryam tayi tana juyar da fuskar ta gefen da babu kowa amma da Yayan take, shewa tayi ta buga zani, ta taso har gaban su tace

"Bansan anayi ba, kunu a wani gida, idan an isa dai a yi a gabana mana."
Chapter 31 · 0% Book details