← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 76

Sashe 36

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Tun bayan ya baro wajen Yayan ya fice daga gidan, dan yana da abubuwan da zai yi masu yawa kafin ya fara aiki sosai dan tuni yayi accepting din offer din Air Canada, one of the best airlines in Canada. Aikin pilot yana bukatar time and dedication, with alot of commitments duk da haka dai shine burin sa, yanzu haka zuwan nan da yayi jinsa yake a takure, ya saba ko yaushe suna sama kamar tsuntsaye.
Yana hanyar dawowa Mama ta kira shi, ya daga yace mata baya gidan dan baya son haduwar su a dan wannan lokacin, dan baya son matsala tsakanin ta da Baba, yafi so ta kwantar da hankalin ta, shi zai yi abinda ya kamata.
Yana shigowa gidan suna kokarin komawa wajen Auntyn ita da Amira, a gaban su yayi parking bayan ya haske su da hasken fitilar motar, bud'e murfin yayi ya fito be ko kashe motar ba, Amira ta gaishe shi da sauri, ya amsa yana jiran yaji itama da gaishe shi, amma sai yaga ta share tana kokarin cigaba da tafiya dan barin wajen, ransa ne yaji ya baci, dama ga haushin abinda Yaya tace dazu wai idan jinin mutum be hadu da nata ba, bata magana, baya son raini sam me yasa ba zata gaishe shi ba, me yasa ba zatayi masa magana ba. Ganin tana kokarin barin wajen dan har tayi taku kusan uku ya sakashi sa hannu ya damko nata hannun ta, kamar wanda aka jonawa shokin haka suka ji a lokaci daya, ya kafe ta da idanun sa dake sata diriricewa

"Me..ne.. ne?" Tace a duburburce,

"Rainin hankali." Yace a hankali, bata ma san me tayi ba?

"Dan... Allah ka cikani zafi."

Ta nuna masa hannun nata da ido, dan sassauta mata rikon yayi,ya cigaba da kallon ta, shi sam yanayin da take zarya a cikin harabar gidan dake cike da ma'aikata da mutane mabanbanta shine be yi masa ba, ba kuma wai kishi yake ba, kawai dai be ga amfanin hakan ba tunda dai ai ko ba ya son auren dai amma akwai igiyar sa akanta, yanzu ma mayafi ne yalolo a iya saman kanta, duk da kayan jikin ta basu da aibu amma baya son hakan, ko su Fauwaz ne baya so suna mingling ta bari idan aka warware auren nasu sai tayi duk abinda ma taga dama be damu ba.
Tuni Amira ta cikawa wandon ta iska, dan ta lura Ya Tariq din ma ya manta tare suke da Jiddan, sake maimaita ya cikata tayi tana kauda fuskar ta, dan ta rasa dalilin da yasa yake shigar mata rayuwa, tana iya kokarin ta na ganin tayi nesa dashi amma yana sake shigowa yana dagula mata lissafi

"Anki a cikakin."

Yace yana hade rai, kokarin kwace hannun ta shiga yi, wanda ko zaa hada irin ta goma basu isa su kwace ba, dariya ma ta so bashi yadda take ta kicin-kicin kwace hannun nata, sai zuciyar sa ta raya masa wani abu, be yi dogon tunani akai ba, kawai ya bi umarnin zuciyar tasa, ya jata ya bud'e murfin motar ya tura ta a ciki, ya shiga ya juya ya sake ficewa daga gidan.
Uffan bata ce masa ba, ya dinga gudu da ita akan titin, kanta na kallon window lokaci zuwa lokaci tana saka hannu ta share kwallar da take zubo mata. So yake ta bude baki tayi masa magana, ta roke shi ya tsaya ko tace ya maida ita gida amma kemaimai taki cewa komai, kamar zai yi hauka haka yake ji, be taba ganin miskilanci irin wannan ba, duk yadda ake fadan nasa ta taka shi ta shanye dan shi ya rage kusan kaso goma a ciki bayan tafiyar sa. Gajiya yayi da zagayen ya samu gefen wani restaurant yayi parking, suka zauna a motar kawai, zaman da ya haifar masa da wani yanayi me wahalarwa. Karkata zaman sa yayi ya juyo yana kallon wajen da take zaune, ita kuma tana kallon waje taki yarda ko sau daya ta kalli ciki dan zuciyar ta, tayi masifar yin weak.

"Jiddaa..." Ya samu kansa ta kiran sunan ta, wanda shi kansa be san dalilin kiran nata ba, kasa amsawa ba kuma wai dan tana sani ba, sai dan ba zata iya amsa masa ba, tana bud'e baki kuka ne zai fito, ita kuma bata so yaga gazawarta.
Dunkule hannun sa yayi, ya daki sitiyarin motar, sautin kukan ta ya shigar masa har cikin kwakwalwar sa, baya son kukan ko kad'an, kuma be ga wani babban dalili da zai sakata kuka ba, tunawa yayi ranar da ya ganta a kitchen tana kukan nan, tabbas akwai babban abinda yake damunta, toh ko bata son shi ne? Sai yaji gabansa ya fadi, tsoro ya shige shi. Cigaba da kukan tayi a hankali bata san yana jin ta ba. Ji yayi kamar ana fuzgarshi zuwa gareta, ya dinga matsawa har ya matso daf da ita, har tana jin hucin numfashin sa, hade da kamshin turaren sa da ya kara karfi saboda matsowar da yayi kusa, bata san haka ya zo daf ba, ta juyo da nufin ganin abinda yake yi, ba tare da tunanin komai ba, ya rungumeta yana zagaye ta da hannun sa zuwa cikin fafffadan kirjin sa.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (28)

_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

***Kamar wanda aka dasa a wajen haka ya tsaya k'yem, tun da yake, tunda yake a rayuwar sa be taba ganin gashi irin wannan ba, yana yawan imagining mace da long hair amma not this long, daga ganin shi zai yi dadin tabawa. Sam bashi da cika bare yawa, sai tsayi da tsantsi da baki. Yana tsaye yana shawarar abinda ya kamata yayi, duk da ya gaza gasgata zuciyar shi cewa ita ce, that slim girl da yake ganin ko motsi tayi da yawa zata iya ballewa, duk da hr yanzu she's slim amma kuma she's curvy, irin yadda yake so da muradin matar da yake so, amma kuma ba wai son ita Jiddan yake ba, kawai dai she possess some qualities da yake so a wajen mace. Tunawa yayi da bata ko gaishe shi ba, bare ta bude baki tayi masa magana sai ma wuce shi da tayi kamar bata lura da existence dinsa ba, ransa ne yaji ya baci, ya bar kofar ya nufi hanyar da tabi ya tarar da daki daya a wajen, ya tabbatar nan ta shiga, knocking yayi a kofar jidda dake durkushe a wajen tayi saurin kallon kofar, tunanin ta Aunty ce, tayi saurin saka bayan hannun ta, ta goge fuskarta sannan ta bud'e kofar tana sauke kanta k'asa kar Aunty ta gano wani abu.

"Baki iya gaisuwa ba?" Yace bayan ya sake kare mata kallo, da sauri ta dago ta kalle shi, taga ya zura mata ido, saurin dauke kanta tayi bata ce masa uffan ba

"Kina kallo na, amma ko ki gaishe ni, ko ba'a koya miki gaisuwa bane?"

Nan ma dai shiru tayi masa, hakan ya sake kular dashi, ya fizgo hannun ta, tayi saurin janye wa tayi baya da sauri, ya samu damar shigowa dakin yana kallon ko ina a cikin dakin, idon sa ne ya sauka akan abincin dake saman bedside drawer, ya nufi wajen ya dauki tray din, ya samu waje daga gefen gadon ya zauna ya shiga cin abincin yana kurbar lemon kwakwan yana satar kallon ta, tana tsaye a wajen da take bata motsa ba, bata kuma ce masa ci kanka ba, yaci abincin sa ya koshi yana ci yana more kallon ta, ba tare da ta sani ba, haka shima ba tare da ya san abinda yake ba. Tunanin sa ne ya kawo masa, ya tuna me ma yake a cikin dakin ta, baya son raini kwata-kwata, sai gashi yana kokarin siya ma kansa raini da kudin sa, ficewa yayi be sake ce mata komai ba, tayi saurin rufo kofar yana fita, yaja dan siririn tsaki ya fice daga part din.

*** A zaune ya samu Fauwaz yana waya, ya watsa masa wani kallo yayi wucewar sa bedroom din sa, saurin katse kiran Fauwaz yayi, ya tashi yabi bayan sa, ya tarar dashi yana cire kayan jikin sa

"Ina ka shiga ne? Tun dazu nake jiran ka gashi wayar ka, ka barta a nan."

"Ina ruwan ka da in da naje? Yace yana rataye rigar sa a jikin hanger ya rage saura singlet kawai da dogon wandon

"Na zata wallahi ba zaka dawo yau ba, ina ta tunani gashi Mama tana ta jiran ka."
Chapter 36 · 0% Book details