← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 76

Sashe 40

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Duk yadda Mama taso Tariq ya yi botsare akan maganar auren nan sam yki, ta ma kasa gane in da ya dosa kwata-kwata, kamar ma so yake kawai ta kwantar mata da hankali shiyasa ma yake biye mata da nuna mata shi ma baya son abun. Babu yadda za'a yi baya so kuma ya hakura har a kawo yanzu, wanda nan da kwana biyu zata tare daga nan kuma bata san ya zai yi ba. Yanayin hayaniyar bikin da dumbin mutanen da suka taru yasa ta hakura da maganar ba wai dan ta hakura gaba daya ba, yanzu zatayi focusing kawai akan su Safiyya idan aka gama zata dawo kan Tariq din ne dan ba zata yarda a lalata mata rayuwar dan ta ba.
Baki daya gidan idan ka cire bangaren Yaya kowa ya yi shirin tafiya wajen hadaddiyar dinner din da aka shirya, Mama bata nan sun fita da Aunty Mimi daga chan zasu wuce ita da wata babbar kawarta da suka hadu a taron da suke na matan ministoci. Su jidda na wani babban gidan makeup ita da su Ya Safiyya wadda da k'yar akayi convincing dinta ta yarda zaa mata amma yar kad'an dan bata son irin heavy makeup din, ita kadai take budirin ta dan me gayya me aikin kamar ma be san anayi ba, shiyasa Amira zata tsayata su tafi tare driver ya kaisu su kuma Ya Safiyya miijin kowacce ne zaizo su tafi abun su. Su Umaima ne suka fara tafiya sai Ya Safiyya ma ta tafi ya zama sai su kadai dama kuma sune karshen gamawa. Driver Amira ta kira tace sun gama ya matso da mota, yace mata ya dan fita daga cikin wajen zai shigo da Oga yana waje. Yana cewa oga ta gane Ya Tariq yake nufi dan haka yake ce musu shi da Ya Fauwaz dan dama ba bahaushe bane ba. Kin fadawa jiddah tayi sai da ya dawo ya kira sannan tace su taso su tafi.

Yana tsaye jikin sabuwar motar sa, wadda Baba ya bashi gift dinta jiya na kammala karatun sa da kuma aure, kaftan ne a jikin sa fari me hade da navy blue collar da jikin hannun, takalmi da hular kansa duk navy blue ne,dinkin da kad'an ya wuce guiwar sa. Kallon wajen yake a tsanake har suka fito, Amira ta hango shi suka nufi wajen da yake a tsaye, sai da suka kusa karasawa sannan Jidda ta ganshi, tsayawa tayi chak cike da mamakin ganin sa, juyowa yayi suka hada ido ya tako ya same su a wajen da suke tsaye

"Kije Sam ya ajiye ki,mu ba zamu je dinner din ba."

"Ok." Amira tace tayi gaba da sauri,

"Muje ko?" Yace yana nuna mata hanya

"Tafiya zamuyi da Amira fa." Ta fada idon ta nayi raurau kamar zatayi kuka

"Na sani ai, cewa nayi ba zaki je ba, babu wata dinner da zaki oya shiga mota mu wuce gida."

"Dan Allah ka barni naje."

"Ba zaki ba."

"Dan Allah." Ta sake cewa already har ta soma kukan bakin ciki, kukan ka gama saka rai a abu ace ba zaka ba, da tun farko da tace ba zata ba da sun kyale ta shikenan, amma sai da ta hakura har tazo make up sannan yace ba zata ba..

"Oya, muje ko na daga sama, kinsan kuma zan iya."

Waigawa tayi ta hango wasu saurayi da budurwa a chan gefen su, ta sake waigawa dayan barin shima wasu ne a zaune suna hira, sai kawai ta nufi motar tana had'a hanyaa.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (32)

***Kofar motar a bud'e take, taje ta shiga ta sunkuyar da kanta k'asa zuciyar ta na tururi, agogon hannun sa ya kalla ya kalli cikin motar, ya kad'a kansa ya tako zuwa wajen motar, ya rufe mata kofar ya zagaya ya shiga ya zauna.

"Ki daura seatbelt."

Yace yana jan tasa ya daura, ya kunna motar, hawaye ne ya shiga sauko mata na bakin ciki, duk kawayen su na school zasu je Amira ta fada musu Safeera ma zata wuce daga chan dan ta shigo tana gidan aunt dinta. Sake kallon ta yayi yaga bata daura seatbelt din ba, matsowa yayi jikin ta,ta dago ya kalle ta yayi mata murmushi, irin murmushiin na ci karfin ki, kauda kanta tayi ya jawo belt din ya daura mata, ya tsaya daf da ita bayan ya daura matan, k'in juyowa tayi tana jin ji daf da ita, k'ashin wuyan ta ya kalla, yaga rami, hannu ya kai ya taba ta juyo da sauri

"Har ajiya za'a iya yi a wuyan nan naki."

Yace hannun sa yana kan wajen, fuskar sa a sake yana so ya kure ta, banza tayi masa tana jin yadda yake tafiya da hannun sa akan wuyan nata, wani irin take ji amma ta fuske dan sosai take cikin bacin ran hanatan da yayi wanda bata ga dalili ba.

"Kina wannan kamshin turaren zaki shiga wajen da yake da garadan maza? Baki san darajar aure bane?"

Yace yana kokarin saka idanun sa acikin nata,

"Haramun ne, ki bari mu samu solution sai kiyi ma duk abinda zakiyi, amma dai yanzu na hana,."

"Sai ayi sauri a samu solution din, I'm sick and tired, na gaji."

Sai ya fashe masa da kuka dan ba karamin haushi maganar sa take bashi ba, kullum sai yayi kokarin shiga rayuwarta haka kullun sai ya jaddada mata jiran lokaci yake, ta gaji kawai ya yanke hukuncin da duk ma zai yanke dama ta riga ta shirya. Tsayawa yayi chak yana kallon ta, kukan take bil hakki da gaskiya, ya rasa kwakkwaran dalilin da zai saka ta dinga irin wannan kukan, be sani ba ko zama kusa dashi ne bata so, ko ganin shi ma gaba daya ne bata so. Gashi shi kuma yana jin shi very comfortable duk sanda suke tare, yanzu ma yana samun labarin zasu dinner ya taho hankalin sa ba a kwance yake ba, baya so taje wajen ayi ta kallon ta, ba kuma dan yana so ko kishin ta ba a nasa tunanin, sai dan kawai ya kare martabar auren sa da yake kanta.

"Komai kuka, kuka baya maki wahala ne?"

Ya tambaya yana maida kansa ya jingina a jikin kujerar motar yana duban ta, kamshin turaren ta, na fuzgarshi zuwa gareta, sai dai yayi matukar kokarin hana kansa, yana jaddadawa kan nasa cewa . Kokarin daidaita kanta tayi, ta goge fuskar tana hana kukan cigaba da zuwa, kukan bakin cikin abinda yake mata ya kuma nuna sam be san ma me yake ba, yanzu da tayi magana maimakon ya amsa mata sai ma ya tsaya kawai yana kallon ta, ya kuma sauya zancen zuwa wani na daban. Jin tayi shiru ne yasa shi tashi ya sake kunna motar ya ja suka fice daga wajen.
Kasancewar babu nisa tsakanin nan da gidan ya saka su saurin isa, hakan ya kara tabbatar mata da ba zata je din ba kenan. Sai da ya shiga har cikin gaban part din Auntyn sannan yayi parking, bata jira komai ba, ta bud'e kofar ta fice, maimakon ta shiga nasu bangaren sai ta chanja hanya zuwa part din Yaya. Parking ya gyara ya bi bayan ta da sauri dan ya hango wasu samari a wajen suna zaune, kasancewar da sauri yake tafiya yasa yayi saurin cimmata, ya rufa mata baya yana kakkareta. Ta ganshi sarai amma tayi kamar bata ganshi ba, suka cigaba da tafiya tana daga kafa yana sauke tasa har suka shiga. Yaya na zaune ita da Gwaggo da wasu a falon ta shigo, ta shige dakin Gwaggon da saurin ta, bude baki Yaya tayi zatayi magana sai gashi ya shigo

"A ah, tare kuke ne?"

"Eh." Yace yana shigewa ciki shima bayan ya gaishe su a gajarce

"Ina wajen bikin kuma?"

"Ko har an dawo? Gwaggo tace

"A ah be isa an dawo ba, bari naje naji dan yadda Jidda ta shigo kamar ba kalou ba."

"Toh Allah yasa lafiya."

"Amin." Tace tana mikewa da k'yar dan kafarta ta fara matsa mata sosai. A tsaye ta same shi daga kofar ita kuma jiddaa na saman gadon ta rufe fuskarta, duk kwalliyar da akayi mata ta baci ga shi sai kiran wayarta su Safeera suke Aunty ma ta kirata ta kasa dagawa.

"Ya akayi me ya faru?" Yaya tace tana kallon sa

"Wai dan nace ba zata je dinner ba, shine take kuka."

"Kamar ya ba zata je b? A wanne dalilin yasa ba zata ba?"

"Menene amfanin zuwan toh?"

"Abinda suka dade ana shiryawa zaka hanata fisabillillah, gaskiya baka kyauta ba wallahi, Jidda tashi kinji, daina kukan haka nan kiyi hakuri, kai kuma sai ka gaya min kwakkwaran dalilin da ya sa ka hanata wallahi, dan ni banga dalili ba."

"Ni ba wani dalili, kawai bana so ne, ta bari taje idan babu aure na akanta."

"Ahayyye!"

Tayi shewa tana tafa hannu, kicin-kicin yayi da fuska Yaya ta rasa me ma zata ce

"Ai be kamata ba, tunda dai shi aure daraja ne dashi, kuma ni bana son irin wadannan abubuwan, ta bari a samu hanyar da za'a kawo karshen komai."

"Kai tafi chan, wacce hanya ce da ba za'a iya samar da ita ba har sai an ta maganar ta, ai kawai yanke hukunci ake idan har da gaske har zuciya ana neman hanyar, ba a fatar baki ba.".

"Tashi kinji Jidda, ki rabu dashi bakin hali ne yayi masa yawa da mugunta, idan ba haka ba a gama shirya abu dan gadara ya hanaki zuwa haba."

Tashi tayi idonta har sun daga saboda kukan bakin ciki, gaba Yaya tayi tazo zata raba ta gefen sa ta wuce ya tare hanyar yana mata wani irin kallo da idanun sa suke a shanye,

"I'm sorry."

Ya samu kansa da furtawa dan da gaske yaji babu dadin abinda yayi mata, kin amsa wa tayi zata wuce ya sake tarewa

"Please kiyi hakuri."

"Zan rungume ki idan baki hakura ba."

Kallon sa tayi da sauri, ya gid'a mata kai,

"Da gaske nake Allah."

"Na hakura."
Chapter 40 · 0% Book details