← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 76

Sashe 68

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Tell me, waye wannan ismail din? How much did he know about you?”

“Ba zamu kyale maganar ba?”

“No it’s better ayi ta kawai Jiddaaaa.”

“Ok, yayan Safeera ne, both of them helped me alot a rayuwa ta, sun so ni a yar kauye ta da rama ta, basu taba kushe ni ba ko aibata ni.”

“OMG!” Yace yana kokarin rike ta, ta dan matsa kadan tana kin kallon sa

“He nuna interest akaina and I said no, be takura min ba, he left daga nan aka daura min aure, and I waited for good 1year, since then ban sake ganin sa ba coz dama a time din ya tafi karatu, this is the first time bayan long time da na ganshi, and yasan nayi aure, kuma nasan babu wani abu a ransa.”

“Jiddah!”

Ya kira ta ganin yadda mood dinta ya sauya. He misunderstood everything yazo yana ta fushi akan iska. Kin kallon sa tayi saboda yadda idanun ta suka cicciko zatayi kuka. Juyowa da ita yayi suna kallon juna, tayi saurin sauke kanta kasa ya sa hannu ya tallafo fuskar ta.

“I’m so sorry kinji? Dan Allah Kiyi hakuri ki daina tuna abinda ya wuce, nayi kuskuren fadan abubuwan chan Amma wallahi wallahi ba har zuciya ta ba, I was just looking for an excuse to hold on to, ba nayi ne don cin fuska ba, dan Allah forgive me! Wallhi nayi regretting, I regret everything har rashin dawowa ta,forgive me dan Allah!”

Kuka tasa masa ya jawota jikinsa ya rungume zuciyar sa na wani irin zafi, yasan zata dade bata manta ba, bayan ka zauna zaman jiran mutum ba shekara daya amma ya dawo yace baya son ka, dole da ciwo ontop of that kuma ma ya hada da kushe ka, dama zai iya dawo da lokacin baya ya goge duk abinda yace din, Amma Yanzu kam it’s too late. Ta dan dade tana kukan kafin tayi shiru sai ajiyar zuciya da take a hankali, tana da saurin kuka karamin abu yanzun nan zai sakata kuka sosai, bayan ta yake tapping a hankali ya kasa ce mata komai har tayi shiru din. D’ago ta yayi yana kallon yar fuskar tata, hannun sa yasa ya goge mata ragowar hawayen da take ya shafi saman lips dinta da yake ganin shine kawai last option dinsa da zai yi amfani wajen sake bata hakuri.

“I’m sorry.”

Yace muryar sa ta shige ciki sosai. Sai ya matso da fuskar sa daf da tata, ya dora hanci sa a saman nata yana gogawa kadan kadan yana kokarin saka mata idonsa a cikin nata saboda taga how sorry he is, a hankali ya kai bakin sa saman nata ya hade su waje daya, sannan ya sa hannun sa ya zagaye ta cikin ta ya matso da ita so so close.
Kusan minti biyu ya dauka yana kissing dinta a hankali, kafin ya cikata yana maida kansa ya hade goshin su waje daya, idon ta a rufe yake jikinta yayi wani irin sanyi, ya riga ya gano lagon ta. Kissing aaman

“Please Kiyi hakuri, ki daina tunawa kinji? Ya wuce ba zan sake ba. I love you so very much, bansan irin son da nake miki ba wallahi! Kukan ki is one of my weaknesses dan Allah ki daina kinji?”

G’id’a mishi kai tayi, ya rike hannun ta yana mata murmushi

“Did you love me?”

Ya tambaye ta for the first time cike da tsoron kar tace masa a ah.

“Umm? Kina son Ya Tariq dinki?”

“Eh…” ta daga kanta kunya na cikata

“Yes! Say it naji, pleaseee.”

Kasawa tayi, ta boye kanta a kirjin sa tana dariya kadan kadan

“Kunya kike ji?”

“Umm…”

“Ni dai sai kin fada min naji.”

“Ba zan iya ba.”

“Zaki iya, pleaseeee!”

Yawun bakinta ta tattaro fuskar ta har lokacin na cikin kirjin sa,

“Na rufe ido na, inajinki fada mjn, tell me you love me.”

Dagawa tayi kadan taga ya kulle idon sa, kallon fuskar ta dinga yi tana admiring din ta, ta dan kai hannu kadan ta taba gefen sajen sa, ya rike hannun yayi kissing dinsu still idon sa na a rufe

“I’m waiting…”

“I love you so much.” Tace da sauri kamar wadda aka tunkuda. Dariya ta bashi amma sai ya kanne ya bude idon sa

“Wow! I love you more baby.” Yace yana mata murmushi
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*

              Page (55)

***Kallon hanya take cike da murna da farin cikin zata ga Baffan ta, yana lura da yadda ta cika da doki yayi murmushi yana murza hannun ta kad'an da yake cikin nashi tun sanda suka soma tafiya. Suna baya a zaune sai driver a gaba da mutum daya.

"Bafa kwana zakiyi ba." Yace ta juyo da sauri tana kallon sa

"Yes!" Ya dage mata gira

"Na dade ban zo ba fa."

"Zaki dawo ne, banda yanzu amma."

"Dan Allah."

"Nah!"

"Dan Allah Dan Allah!"

"Um um naki, tare zamu koma. Nayi missing dinki."

"Missing?"

"Ehen, ba zan iya hakuri ba jiya dai kin yi min wayo amma banda yau."

"Please dan Allahhhhh." Taja muryar ta cike da shagwaba

"La la la la,na murza gashin baki."

"Pl...." Hannu ya dora mata akan lips din nata yana girgiza mata kai

"Don't beg me pls, or i will kiss you."

Hadiye maganar tayi tana yin raurau da ido, yayi kamar be gani ba ya juyar da kansa yana murmushi. Bata sake magana ba har suka isa cikin garin ta soma ganin mutane kad'an kad'an har suka karasa kofar gidan nasu da ya samu sauyi sosai fiye da yadda tazo ta ganshi a baya. Baffan ta, ta hango yana tahowa daga hanyar kasuwa sanye da shadda fara tas daga gani sabuwa ce hannun sa rike da leda baka fuskar sa dauke da murmushi wanda ya kasance sunna.

"Baffa." Ta motsa bakin ta a hankali tana murmushi, kallon wajen yayi ya kurawa baffan ido, kasancewar ya jima be ganshi ba tun wani zuwa wajen Baba da ya taba yi sai yaga ya sauya masa sosai, kamannin sa da nutsuwar sa sak na Jiddan sa,hatta da tafiyar ta irin tasa ce. Bud'e motar yayi da dan sauri ya fito ya nufi wajen baffan tun kafin ya kai ga karasowa ya durkusa har k'asa, sai a lokacin baffan ya lura da su dukka ma, ya fadada fara'ar fuskar sa zuwa ta musamman

"Baffa barka da warhaka."

"Barka dai d'ana, zuwan kenan? Sannun ku da zuwa."

"Zuwan kenan," ya mika hannun sa ya karbi ledar hannun Baffan, ya sakar masa yana jin dadi idon sa akan Jidda dake tsaye tana murmushi.

"Muje ciki kaji, sannun ku da zuwa maraba."

Mikewa yayi yabi bayan Baffan yana kallon idanun Jiddan da suka kawo ruwa kamar zatayi kuka, yadda yayi wa baffan yafi komai yi mata dadi, a kalla ya girmama mahaifin ta girmama mafi girman gaske.

"Baffa." Tace tana matsawa kusa dashi ya yi yar dariya yana cewa

"Kin ganki ko? Ba dai kuka zaki mana ba."

"Ka ganta nan bata girma Sam, duk sanda tazo sai tayi kuka saboda shirme."

"Murnar ganin ku ce Baffa."

"Kai dai kare ta kake."

Yace sanda suka shiga zauren gidan, kallon ta yayi ya girgiza mata kai a hankali k'asa kasa yace

"Don't waste my tears please."

Ta jishi sai kawai ta shige ciki da sauri ta bar su suna kokarin shigowa tunda Baffan a hankali yake tafiya ssosai duk da kafar sa ta samu sauki amma kuma yana dan lallabawa.
Iya Lami na zaune a kofar dakin ta da yasha fenti da duk dakunan da suke cikin tsakar gidan nasu in da taga sabon gini daga gefen dakin baffan, kafin ta gama tunanin yaushe akayi hakan sai ga wata mata farar dattijuwa ta fito tana duba abu a kofar dakin kafin dukka su lura da Jiddan da take kallon gidan nasu.

"Jidda!"

Iya Lami tace tana mikewa rike da gefen zanin ta ta hau gyara shi tana washe baki.

"Jiddan Bingel? Ah maraba lale da mutanen birnin taraiya "

Matar tace tana sakin murfin kofin da ta dauka a hannun ta tayo wajen Jiddan tana wuce Iya Lami da ta saki baki ta dakata da karasowa. Murmushi me kama da yake Jidda tayi ta gaida matar wadda ta cika da murnar ganin ta tamkar ta santa ko ta taba ganin ta.

"Sannu da hanya Hauwa'u, sannu da zuwa wuce muje ciki."

"Malama ki kyale yarinya da gidan ubanta ai tasan gidan ba sai kin nuna iyayi da kinibibi ba, uwar munafukan duniya."

"Shigo nan Jidda."

Tayi banza da maganganu Iya Lami din ta kama hannun Jiddah zuwa dakin da tafito, tayi saurin shinfid'a mata tabarma sannan ta debo ruwa me sanyi a randar ta dake gefen dakin ta, ta kawo wa Jiddan hade da mahuci saboda yanayin zafin da ake a garin da ya dan busa wanda ake kira da daure cikin dawa. Zama tayi a kubin Jiddan ta dauki muhucin ta hau mata firgita sai ga Baffa ya shigo Tariq na biye dashi har cikin dakin da Jiddan take ba tare da ya kalli ko da bangaren da Iya Lamin ke tsaye ba. Wata tabarmar ta mike ta sake shinfidawa kafin taja mayafi ta rufe kanta ruf sannan ta zauna tana amsa gaisuwar Tariq din.

"Yau dai ga yarki nan na tazo tare da Maigidan ta, shikenan sai murna."

Yace yana dariya

"Aikuwa yau ina cike da farin ciki mara misaltuwa, buri na kuwa ya gama cika."

"Baffa na ina wuni?" Jidda tace tana shagwabe fuska ganin kamar yafi damuwa da ganin Tariq din a kanta

"Lafiya Lou, alhamdulillah sannun ku da hanya."

"Baffa! Bakayi murna da gani na ba?"

"Nayi murna mana Jiddan Anty." Yace cikin sigar zolaya,

"Sai dai nafi murnar ganin dana Tariq."

Murmushi Tariq din yayi suka hada ido da Jidda ya kashe mata ido daya ta turo baki gaba tana kin sake kallon sa. Dago labulen akayi Iya Lami ta shigo ta samu gefen kofar dakin ta zauna

"Maraba sannun ku da zuwa."
Chapter 68 · 0% Book details