← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 76

Sashe 44

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_"Me yasa nake kasa controling kaina when I'm with her?"_ Ya sake tambayar kansa. Tana da wani irin tasiri akansa, a kanta yake bude baki yayi magana sosai fiye da yadda take yi masa kuma shima yake yiwa kowa, baya tunanin komai da kowa a duk lokacin da take gabanta. Murmushi yayi yana jin taste din salivar dinta a cikin bakin sa, dama he has been longing for this , ya dade yana imagining kansa kissing her small lips, he never expected her to be this sweet, a dah kallon karamar yarinya yake mata wadda yake ganin ba zata iya masa ba, kuma ba zata iya da needs nashi ba, but ya fara proving kansa wrong, and he is developing feelings for her, duk da babu yawa amma kuma yasan ko yaya ne dai. Juyowa yayi da kansa yaga ta sake juyawa dayan side din, yasan kunya taji, sai ya kyale ta kawai ya juya ya rufe idon sa, ko minti biyar be kara ba bacci yayi awun gaba dashi.

***Da asubah ta riga shi tashi, ta kalle shi babu ko riga a jikin sa sai 3quater wando, duk kuwa da sanyin dakin, ta rasa dalilin da yasa ko sanyin baya ji bayan ita har hancin ta ya toshe saboda sanyi ya kure AC kuma ya cire riga, shi jin zafin nasa ma extraordinary ne, toilet taje tayi alwala ta fito ta sameshi ya tashi ya kunna hasken dakin,alwalar da tayi yasa sanyin da take ji ya karu, yazo ya wuce ta ya shiga toilet din shima, rage sanyin tayi sosai ta kudundune da blanket sai da taji sanyin ya dan ragu sannan ta tashi ta dauko Hijab din ta saka ta shinfid'a sallaya zata tada ikama ya fito da ruwa a jikin sa yana gogewa da towel alamun wanka yayi, jallabiyar ya dauka ya saka ya ciro hula irin wadda ake kira da tashi ka fiya naci fara ya dora akansa ya fice da sauri dan kar ya rasa jam'i.

Tana nan akan sallayar ya shigo dakin da sallama, ta amsa kanta na kasa bacci na fizgarta, zuwa yayi ya duka a gabanta ta dago jin shi a kusa da ita

"Baki bacci ba?" Ya kalli idon ta, da suka dan tasa, girgiza masa kai tayi

"Nayi."

"Ok, yau daurin auren yaran chan, munyi waya da Baba yanzu da wuri zan fita,dan Kano zamu a sumaila za'a daura auren ki kwanta kiyi bacci kinji?"

Ware idon ta, tayi da sauri taji ta nemi baccin ta rasa

"Ni ba zan je ba? Ba zani gidan ba?"

"Eh." Yace mata kai tsaye

"Ni kadai zan zauna?"

"Eh." Yace mata nan ma

"Dan Allah kayi hakuri, wallahi tsoro nake ji, kuma duk su Amira suna nan har kayan da zamu saka yau an karbo, dan Allah ka barni dan Allah."

Sai ta fashe masa da kuka wiwi, yana durkushe akan digadigin sa,yana kallon ikon ALLAH, abu kad'an sai kuka? Me zata je tayi toh kuma? Baya son duk abinda zai faru tsakanin shi da Mama ya shafe ta, yasan nata sai yafi zafi shiyasa yaga gwara tayi zaman ta.

"I'm sorry kinji, zan turo su Amiran sai su zauna dake."

"Ba zuwa zasuyi ba, biki ake fa."

"Toh shikenan, babu abinda zai sameki ai,akwai masu aiki a waje, Fauwaz zai kawo duk abinda babu a kitchen."

Sai ya mike ya isa wajen kayan sa, ya dauko sabuwar shaddar sa fara kal da babbar riga, ya dauki takalmi, agogo da hular sa, da sauran abinda zai bukata, dan a gidan zai shirya, mota yaje ya kai ya dawo har lokacin kukan take sosai, baya so ta karyar masa da zuciya har yace taje, sai kawai ya tsaya daga kofar yace mata ya tafi, ko dagowa batayi ba, yayi jim a tsaye sai kuma ya juya ya fita dan baya so Baba ya kuma kiran sa dan babban aiki ya sashi, kuma sune zasuyi gaba kafin su Baban su iso shiyasa ma ko breakfast be tsaya yayi ba.

_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*

_(Where every flavour tells a story .....)_

*_By HAFSAT RANO_*
_(Mother/wife/writer)_

_08030811300_
_IG:Rano_scrumptious_meal_

_INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*?  GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_

_MU NA YIN:_

*_FUNKASO_*
*_ALKUBUS_*
*_SINASIR_*
*_WAINA_*

*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_*
*_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_*
*_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*

*_LOCAL DRINKS:_*

_HIBISCUS (ZOBO)_
_GINGER_
_AMAANI FRUITY SHAKE_

_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._

_KADA KU MANTA MUNA  YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._

_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_

_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_

_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (35)

***Kasa daga kafarta tayi daga in da take tsaye, taji kamar ana sassara mata su, tsoro ne ya shige ta, tsoron abinda zata tarar idan har ta bishi, bata yi tunanin da gaske aunty take ba,da tace yau zata tafi, sai ta dauka kawai tsokanar ta sukeyi, a yanayin da ya shigo mata ta tabbatar ba da wasa yake ba, me ya kamata tayi? Ta tambayi kanta tana tsaye rike da Hijab din gashin kanta a barbaje dan ko ribbon bata saka masa ba.

"Aunty." Tace tana kallon in da ta ajiye wayar ta da nufin ta kirata a waya tazo tunda tana part din Baba. Babu wayar a wajen, dudubata ta shiga yi amma bata ganta ba, tasan kuma a saman gadon ta ajiye ta, cigaba da dubawa tayi tana rike da Hijab din tana tunanin abinda ya kamata tayi.
   In da yasan zai samu Auntyn ya nufa, yayi knocking a kofar ya tsaya rataye da hannayen sa a bayan sa. Bude kofar tayi,

"Tariq?"

"Aunty zamu tafi ne dama, shine nace bari na fada miki."

Wani irin sanyi taji a k'asan ranta, tayi murmushi tana gid'a masa kai

"Ba komai ai, akwai kayanta a wata trolly sauran sai a kawo mata da safe, Allah ya tsare ya taimaka."

"Amin , Baba be dawo ba?"

"Yana hanya, zamuyi magana dashi."

"Nagode Allah ya kara girma."

"Amin Amin."

Tace ta kasa boye farin cikin ta, wucewa yayi sai da ta daina hango shi sannan ta rufe kofar zuciyar ta cike da farin cikin Jidda zata samu nutsuwa da sauyin rayuwa irin wadda take mata fata.

Tana tsaye ta gama dube-duben wayar bata ganta ba sai gashi ya shigo, be kalli in da take ba, ya saka hannu yaja akwatin yayi gaba. Yanayin fuskar sa kadai ta ishe ta ta gane ba da wasa yake ba, dole ta saka Hijab din ta tura ribbon din a hand bag dinta tabi bayan sa a sanyaye.
  Har ya shiga mota tunda a gaban wajen yayi parking dinta dama, ta hasken da ya haska cikin motar ta hango shi yana kokarin tada motar, kofar gaban a bud'e take, ta karaso ta shiga a sanyaye ya yi reverse suka fita daga gidan. Babu wanda yayi ko tari a cikin su, tukin sa kawai yake har suka isa gidan dake dauke da me masu gadi da securities saboda yadda rayuwar ta zama yanzu. Gida ne madaidaci wanda be cika girma sosai ba, amma kuma ya yi kyau sosai ya dace da masu gidan. Idanun ta akan compound din gidan sanda yayi parking a gefen wata mota dake fake a cikin gidan baka me kyau. Kashe motar yayi ya fita, itama sai ta fito duk da be ce mata ta fito din ba, ya mikawa wani matashi car key din sannan suka haura saman balcony zuwa kofar da zata sadaka da cikin gida. Yana gaba tana bin shi a baya suka shiga cikin falon da yake a matukar tsare, ko ina fes fes komai na ciki sabo ne kal an kawata falon da kaya kalar golden masu daukar ido.
  Hular dake kan sa ya cire ya ajiye a saman centre table din dake tsakiyar falon ya wuce zuwa bedroom din da ya maida shi nasa, dan tuni duk ya tattaro kayan shi daga gida ya kawo su. Cire kayan da yake jikin sa yayi ya sauya zuwa doguwar sakakkiyar jallabiya milk colour ya fesa turare a jikin sa. Ya zauna yana ciro wayar sa da tata, ya bud'e ya saka number sa ya kira yaga tata number din yayi saving sannan ya jona su a jikin chargy ya kwanta a kan sofa yana mike kafarsa. Be san ko hukuncin da ya yanke yayi daidai ba, shi dai kawai yabi abinda zuciyar sa ta fada masa ne.
   Kiran wayar sa akayi, ya tashi yaje ya dauko sai yaga Baba ne yake kira, nauyin Baban yake ji a yanzu dan be san yayi abin kunya ba sai da yaga kiran Baban. Kamar ba zai daga ba ganin zata katse yasa ya daga.

"Baba barka da dare." Yace yana kokarin danne kunyar da yake ji

"Barka dai Tariq, ashe kuma kun wuce sai da na dawo nake samun labari."

"Na'am..." Yace yana sosa kai, dariya Baba yayi

"Shikenan ka shigo da safe inason ganin ka, kar kuma ka manta da maganar da mukayi akan zuwa gaida Baffan naku."

"In sha Allah ba zan manta ba."

"Toh madallah, Allah yayi muku albarka."

"Amin ya Allah, sai da safe."

"Mu kwana lafiya ango."

Baba yace cikin sigar tsokana, ai be san sanda ya danna power button ya kashe wayar gaba daya ba. Sai kuma yayi murmushi tunanin abinda ya aikata na dawo masa, da kunya matuka amma ya zai yi? Hakan ya kamata dama tun farko, ya kuma tabbatar hakan ya farantawa Baban rai dan yadda yake masa magana zakaji muryar sa a sake take cike da annashuwa.
Chapter 44 · 0% Book details