← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 76

Sashe 74

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Personal welcoming suka samu a cikin jirgin kasancewar a first class zasuyi tafiyar me full suite dake hade da private bathroom daga nan akayi musu introducing flight attendant din idan suna da bukatar wani abu. Kujerar su irin wanda ke dauke da pod ne da zaka iya converting dinsa zuwa flat bed hade da fluffy duvets. Gefe kuma amenity kit ne da pyjamas sai slippers.
Tafiyar almost 13hours ce zuwa Toronto, kanta na saman kafadar sa cikin yanayin gajiya da kosawa saboda bata taba irin wannan doguwar tafiyar ba, an kawo musu menu sun zaba abinda zasu ci amma bata wani iya ci sosai ba sai juice kawai da sandwich. Gyara musu kujerar yayi suka mike sosai ya lullube su da duvet yana sakata jikin sa sosai. Bacci take ji duk da tana tsoro amma kuma kasancewar tare dashi ne sai taji ta sake sosai har ta soma baccin a jikin sa. Ta jima sosai tana baccin kafin ta farka daidai kusan lokacin da saura kad'an su isa. Gyara mata gefen idon ta yayi da hannun sa ya taimaka mata ta tashi zaune sosai shima ya zauna yana mika mata ruwa tasha kad'an ta maida kanta jikinsa tayi lamo. Bayan wasu mintuna da tashin ta akayi sanarwa isowar su da kuma shirin saukar su. Yanayin fuskar ta ne ya sauya ta nuna farin ciki dan batayi tunanin tayi dogon bacci irin haka ba, ta zata sai ta kara wani zaman sannan zasu iso dan tayi matukar gajiya dan ba akwai comportability a tafiyar amma duk da haka ta jigata sosai amma shi ko kad'an be nuna gajiya ba saboda ba yau ya fara ba.

***Wani irin mugun sanyi taji sanda suka fito waje, dunkulewa tayi tana sake tura hannun ta cikin katotuwar rigar sanyin da ya saka mata. Kafadarta ya kama ya rik'e ta sosai a jikin sa zuwa motar da zasu shiga daga train station din zuwa gida bayan sun bar airport din train suka hau zuwa garin su sannan suka iso. Ko kad'an bata wani ganin gaban ta lafewa tayi kawai a jikin sa sanyin na cigaba da ratsa ta.
Tafiya kad'an suka isa gidan nasu da yake a sama, hannun ta duk ya kankare duk da handsocks din da ta saka har guda biyu, shi ya rike mata jakar hannun ta, da sauran kayan nasu, suna kokarin shiga lift Ishaq ya cimmasu shi da Yasmin da suke ta sauri. Wani kallo Yasmin din tayi ma Jidda itama ta dan kalleta kadan kafin ta yi gaba kawai suka shiga cikin lift din dukka. Ishaq ne ya tayashi da kayan.

"Welcome back Captain" Yasmin tace tana kallon fuskar sa

"Thank you." Yace a gajarce, ya mika wa Tariq hannu alamar ya bashi card din kofar, mika masa yayi yace

"Idan kun huta zamu dawo mu gaida Anty amarya."

Banza Tariq yayi masa dan ba karamin kular dashi yayi ba, akan me zai taho da Yasmin bayan yasan baya so kuma yasan hakan zai yi hurting din Jidda? Tura kofar yayi ya matsa mata ta shiga ciki sannan yatura kayan nasu yana tare kofar ganin kamar Yasmin din neman shiga take yi

"Yasmin muje mu barsu su huta."

"Ok."

Tace tana kada kanta ta juya cike da tunanin wacece suka zo da Tariq din nata tunda ko da wasa Ishaq be gaya mata yayi aure ba.

Suna shiga Jidda tayi saurin hayewa saman gadon ta ja katoton bargo ta lullube har saman kanta saboda yadda take jin kamar ta kankare. Ajiye kayan hannun sa yayi ya karo karfin room heater din nan da nan dakin ya dau dumi sosai a hankali a hankali taji sanyin na barin ta. Zama yayi a gefen ta yasa hannu ya bud'e mata fuskar ta suka kalli juna

"Are you feeling better?" Yace yana taba saman forehead dinta

"Yes I'm ok, wai sanyi kaman mutum zaiyi freezing?"

Dariya yasa

"Haka suke kuma kinzo a lokacin sanyin ne shiyasa, amma zaki saba."

"A hakan? Ba zan iya sabawa ba."

"Zaki saba, baki ga su Ishaq ba? Kamar ma ba sanyin ake ba."

"Matar sa ce dayar?" Ta tambaye shi tana kallon fuskar sa

"Itace Yasmin!"

Yace yana dago kanta ya dora a saman cinyar sa, shiru tayi tana hango haduwar Yasmin din da mugun wayewar ta. kamshin turaren ta har yanzu yana mata yawo a hanci kana ji kasan irin designer perfumes din nan ne masu shegen tsada da kamshi.

"Don't worry zan yima Ishaq magana akai, I don't want any problem."

Bata ce komai ba, tana jinshi yana zare mata scalf din kanta, sannan ya janye kan nata ya dora a saman pillow ya mike ya wuce toilet yaje ya hada ruwa me zafi a cikin tub yazo ya mikar da ita

"Muje ki rage gajiyar nan."

Tashi tayi ya ja hannun ta zuwa toilet din duk tayi sanyi sosai, shi da kansa ya cire mata kayan jikin ta ya bar mata na cikin kawai dan baya so ya kara mata wata gajiyar akan wadda take ciki. Fitowa yayi ya barta a ciki tayi wankan ta fito ta shafa mai ya taimaka mata ta saka kaya masu dumi sosai sannan ya shiga toilet din shima yayi wankan hade da alwala yazo sukayi sallah daidai lokacin da order din da yayi ta iso ya fita ya karbo ya kawo musu suka ci abincin.
Bacci kawai take so tayi dan idon ta har lumshewa yake tana gama cin abincin taje tayi brush tazo ta kwanta ya dan kalleta yana Jona system dinsa dan yana saka sim din sa har ya samu kira amma be daga ba sai ya jona system din ya zauna yana dubawa abubuwan da suka turo masa wanda zai fara gobe as early as 8am.
Cikin bacci taji ana gyara mata kwanciyar ta, ta dan bud'e ido kad'an ya rungume ta yana rufa musu blanket din dukka jikinsu.

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*

*ZAFAFA BIYAR BACTH A*

1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*

2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*

3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*

1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350

2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*

_Duk biyar 1500_

*______________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1... _FARHATAL QALB_ 400
*(mss xoxo)*

2... _GURBIN IDO_ 400
*(Huguma)*

3... _SANADIN LABARINA_ 400
*(Hafsat Rano)*

4... _INAYAH_ 400
*(Mamu gee)*

5... _BABU SO_ 400
*(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 2k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*

_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*

*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*
[11/25, 3:55 PM] Rano2: _SL__**

©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*

              Page (60)

***Tun da sukayi sallar asubah ta koma bacci, be fada mata zai fita ba dan yaga alamar a gajiye take tikis har lokacin sai bin gefen gado take karshe ta haye tana jan duvet ta rufe kanta nan da nan kuwa tayi bacci. A nutse ya shirya cikin shigar farar shirt me layin baki daga saman shoulder din, navy blue dogon wando sai light blue tie. Be saka jacket da cap din ba sai ya ajiye su a gefe ya gyara zaman waist belt dinsa sosai ya shiga dan madaidacin kitchen dinsu ya samo coffee yasha kad'an sannan ya fito ya saka dark blue din sau ciki ya dauki briefcase dinsa ya dora cap din akan sa ya rike jacket din a dayan hannu ya zo daidai kanta ya durkusa kad'an yayi mata peck a gefen kuncin ta, ya ajiye mata note a gefen gadon ya fice da dan sassarfa.
  Cikin bacci taji kamar ana taba kofa, ta bud'e idonta kad'an tana wurwurga idon ta a dakin tana neman sa, baya nan sai ta sakko da sauri ta fito falon nan ma baya nan. Kofar taje ta bud'e a zaton ta ko shine ya dan fita sai taga Yasmin a tsaye taci uban kwalliya rike da basket me kyau a hannun ta.

"Goodmorning." Tace mata tana rabawa ta shiga cikin gidan kai tsaye, sakin kofar Jidda tayi tabi bayan ta tana jin duk ta muzanta dan ko brush batayi ba bare wanka.

"Captain fa?" Tace tana kallon falon

"Oh yau fa dole ya fita da wuri na manta, oops ya akayi na yi late har ya fita? Allah yasa ma yayi breakfast dan nasan yau kam zai zama so busy."

Kallon ta kawai Jidda take bata ce komai ba amma maganganun ta sun dan taba ta, kenan fita yayi amma ta share baki tana bacci babu wanka bare tayi tunanin samar masa abinda zai karya.

"Kanwar sa ce ke amma ko?"

Tace tana zama bayan ta gama karewa falon kallo

"Umm." Jidda tace tana kokarin barin wajen

"Very beautiful kamar shi, amma fa ya fiki kyau."
Chapter 74 · 0% Book details