← Book details Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 76

Sashe 5

Sanadin Labarina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gudu ya soma yi sosai bayan sun hau babban titi, salati Yaya ta fara yi tana salallami.

"Tariq, rage speed din nan." Baba yace yana kokarin kwantar mata da hankali

"Anya kalou yaran nan yake? Ba zaa kaishi ayi masa rukiya ba kuwa?"

Tace bayan ya rage tafiyar sosai, ta cikin rear mirror ya kalle ta, ya maida kansa gaba ya cigaba da tukin sa yana jin Baba da Fauwaz suna dariya

"Ba abin dariya bane wallahi, dole ma a nemo Malam Na Allah yayi masa rukiya gaskia."

Yana jin su yayi musu shiru tukin sa kawai yake yana fatan su isa lafiya ya tattara ya bar garin gobe dan yasan tunda ta dawo ba zata kyale shi ba sam.
   Har suka isa gida magana daya take, aikuwa yana gama parking yayi saurin fita ya dauki kayanta a booth yayi cikin gidan da sauri. Anty ce a bangaren Yayan tana karasa gyara mata sashen, ya dire jakar yana jan siririn tsaki.

"Ya akayi?" Tace masa cike da kulawa

"Kai na ke ciwo."

"Kaje akwai panadol a kan fridge ka dauka ka sha, sannu."

"Ok." Yace yayi saurin barin wajen dan baya so suzo su tadda shi, part din Antyn ya shiga, babu kowa a falon ya dauki paracetamol din ya nufi kitchen zai dau ruwa marar sanyi dan shi a rayuwar sa baya shan ruwan sanyi sai idan ana tsananin zafi.
    Tana tsaye a jikin drawer din kitchen din tana gyaran kayan miya, kafarta ya kalla a ganta kamar kara, ya dauki ganin sa zuwa wuyanta da yayi masa kama da murkin lema, mamaki ya sake kamashi ganin tana aikin cike da kuzari, a yadda take da ramar nan be yi tunanin ko numfashi tana yin sa daidai ba, gani yake kamar ko kwakkwaran motsi tayi zata iya karyewa. Gyaran murya yayi ta juyo a tsorace, ya dauke ganin sa daga kanta ya dauki ruwan ya fice.

***Da gudun su suka fito jin sallamar Yayan, tana tsaye a tsakar gida suna gaisawa da Anty da su Abu, Amira ce ta rungumeta, tayi kamar zata yar da ita, ta tureta tana dariya

"Ke baki san kin girma bane ba? Ko dan har yanzu baki fara kirgar dangi ba?"

Kunyace duk ta kamasu, Anty tayi kamar zatayi dariya sai kawai tayi gaba tana cewa

"Yaya muje ki huta karki biye musu."

"Ai fa dan na kwaso gajiya, shima Alhaji ya rasa da wanda zai zo daukata sai da wanchan mahaukacin dan naki, ya dinga gudu dani duk yasa dan abincin da naci ya zazzage."

"Wai Tariq?"

"Kina da wani mahaukacin dan bayan shine?"

"Yanayin sa ne haka Yaya."

"Shi kansa wanda ya gado din haka muka sha fama dashi ya buga ya barni, idan zamu kwana be ce min ufffan ba, bana tanka masa haka akayi zaman nan."

"Allah sarki, Allah yasa ya huta."

Anty tace tana ajiye mata flask din ta da aka zuba mata kunu wanda ya zama kullum sai ta shashi, saboda sabo.

"Kunu ne? Kai Allah yayi miki albarka kinji? Allah ya baki kema masu yi miki."

"Amin." Tace tana murmushi, sai kuma ta fita ta bar Amira da Umaima da Yayan

"Welcome back granny, we missed you.!"

"Uwar granny din, na fada miki bana son sunan ko? Sai karyar turanci, toh turancin ma..."

"Ba kyau zagi fa Yaya."

"Anyi, idan ban yi ba ai ban cika bakatsiniyar ba, kuma ko gobe kika sake min turanci sai na zagi turancin, a banza a wofi wayon a zagi mutum ne."

"Bari kiga, amira sai kin taho, ni nayi gaba, Allah ya dawo da mu ai."

Ta mike,

"Idan kin je karki dawo, yar nema kawai."

"Almasifatu."

Tace ta ruga da gudu, tashi Yayan tayi ta jefa mata pillow din kujera

"Yar nema, zaki dawo har in da nake ne."

***Be shigo gidan ba sai wajen takwas na dare, lokacin Mama ta dawo, ya sameta a dakin ta, tana waya da kawarta, zama yayi akan bedside drawer ganin sa yasa ta katse wayar.

"Tariq!

Ta kira sunan sa, amsawa yayi yana kallon ta

"Ya akayi?"

Tace tana zama daga gefen gadon kusa dashi. Tun bayan da ya fara wayo halin sa ya fito sosai, babu wanda yake zama ya fadawa matsalar sa, ya sha yin ciwo a daki shi kadai babu wanda ya sani, baya taba cewa ayi masa abu sai dai ka fuskanta da kanka kayi masa amma ba wai dan ya tambaya ba, da farko halin sa ya fara tsorata ta, amma kuma kasancewar kakansa mahaifin Baban haka yake sak halin sa ya saka kawai ta hakura dan tasan biyu ce ta hadu ita kanta miskila ce. Ganin sa yanzu ya saka tasan akwai muhimmiyar magaanar da zai mata shiyasa ma ta katse wayar dan zai iya chanja shawara cikin kankanin lokaci.

"Ina jinka."

Ta sake maimaita masa tana kallon fuskar sa

"Dama na gama hada kayan tafiyar ne, sakon da kika ce zaki taho dashi daga cikin gida."

"Oh ai ban manta ba Tariq, gashi chan miko ledar chan, karfe nawa ne jirgin naka?"

"9am, amma da asubah zamu fita."

"Ok, Allah ya kaimu, ya bada sa'ar abinda aka je nema."

"Amin." Yace yana rike da ledar, be koma ya zauna ba, hakan yasa ta gane dama abinda ya kawo shi kenan.

"Nagode."

Yace ya juya ya bar dakin, tayi murmushi kawai tana bin bayan sa da kallo.

***Da asubah bayan sun idar da sallah ya shigo cikin gidan, ya wuce shashen Anty ya kwankwasa, suna zaune bayan sun idar da sallah ita da Jidda suna karatun al'qur'ani, ta dauka Baba ne dan shine yake shigowa da asubah ya duba duk wadda ba ita ce da girki ba, tashi tayi ta bude kofar ganin Tariq yasa ta tuna da magaanar tafiyar sa

"Ba dai har kun fito ba?" Tace tana matsa masa ya shigo ciki

Kamshin turaren sa na Versace ne ya gauraye falon, ya zauna a kujerar dake gefen kofar sannan yace

"Barka da Safiya Anty!"

"Barka dai, ka tashi lafiya?"

"Alhamdulillah, yanzu muke shirin fita, jirgin karfe tara ne."

"Ayya, Allah ya kaiku lafiya ya tsare, ya bada sa'ar abinda aka je nema."

"Amin ya Allah."

Yace yana mikewa,

"Ina kwana?"

Ta gaishe shi cikin muryar ta da take kara sashi mamakin yanayin ta, hatta muryar ta kama take da yanayin jikin ta, yar firit muryarta kamar ana busa usur. Be amsa ba sarai kuma yaji sai da Anty tace ana gaishe ka sannan yace.

"Lafiya."

A gajarce, maimakon ya tafin sa kawai ya tsaya yana nazari, wajen minti daya ya dauka yana tsaye yana juya magaanar da take masa yawo akai, kafin yace

"Anty ki kai yarinyar nan asibiti a duba ta, inaga bata da ishashiyar lafiya."

"Jidda?"

Gyada kansa yayi

"Yes, baki ganta ba? Tayi rama da yawa kar ayi iska me karfi ta tafi da ita."

Dariya sosai ya bawa Anty, ta dinga girgiza kanta cike da mamakin sa

"Toh shikenan Tariq, zan kaita."

Ajiyar zuciya ya sauke kamar wanda yayi wani aiki babba yace

"Yawwa. Sai anjima."

"Allah kaddara saduwar mu."

Tace ya fice da sauri yana tuna lokacin da ya rage masa.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: *_Sanadin_*

               *_Labari nah_*

     Free Page ( 5)

©®Hafsat Rano

****Duk da karancin shekarun ta amma maganar sa tayi mata zafi, kuma tsakanin sa da Allah yake maganar, kamar ya kushe halittar ta ne ko wani abu, amma kuma da ta sake kallon kanta sai taga kuma akwai kamshin gaskiya a maganar sa, tabbas tana da rama ta ban mamaki, dan ita kanta wani lokacin sai ta dinga jin kamar zata karye.

"Haka Tariq yake, yanzu akan wannan maganar asibitin ko yaje sai ya sake kira ya jaddada min, da gaske yake daukar ire-iren wadannan abubuwan musamman da ba wani saka baki ya cika yi a abu ba, amma duk abinda kuma ya damu dashi toh fa baya hakura sai ya cim masa."

Shiru tayi bata ce komai ba har Antyn ta gama bayanin da ta lura so take ta wanke shi, tashi tayi kawai ta soma gyara falon ita kuma Anty ta nufi kitchen dan sama musu dan abinda zasu ci kafin hajiyar gidan ta kirasu zuwa karin kumallo dan duk ranar girkin ta sai an sha yunwa a gidan musamman yanzu da Baba zai fita da asubah ba dashi za'a karya ba dan yace daga airport din ma wani wajen zai yi suna da meeting na majlisun su a masallaci.

***Safiyya ce kawai ta fito da zai tafi ita da Mama suka rakashi har mota, dan su Amira ce musu yayi su zauna kar wadda ta fito baya son ire-iren wadannan abubuwan, last da zai tafi suka sha kukan su yana kallon su shi abun ma mamaki ya bashi, shiyasa wannan karon yace kar su fito, har ya shiga mota ya tuna da Yaya, shi shaf ya ma manta da ita, ya kuma san idan har ya tafi be mata sallama ba ya shiga uku, dan maganar ba zata taba karewa ba ta dinga mita kenan, fitowa yayi daga motar ya nufi bangaren ta yana fatan ya sameta ta koma bacci, yana tura kofar falon ya ganta tana shirin fitowa, da sauri yayi baya ta kalle shi

"Na zata ai tafiya zakayi baka zo ba."

"Ban tafi ba." Yace

"Na zata ai nace, wajen ka nake shirin zuwa yanzu haka ma, zauna muyi magana."

Tace tana zama, kamar kar ya zauna sai kuma ya zauna

"Kana ji, nayi magana da wani malamin mu na chan kauye, yace zaa kawo maka rubutu kasha idan abun be sauki ba sai ayi maka rukiyya, bansan yau zaka tafi ba, ba wanda ya fada min sai da babanku ya dawo yake fada min, yanzu sai ku fara biyawa ku karba sai ku wuce."

"Ina?"

"Ban sani ba."

"Allah ya baki hakuri, zamu biya mu karba."

Yace ya mike

"Karka fa tafi baka karba ba, ka kira su ayapot din kace su jira ka."

"Toh, zan kira."

"Yawwa, Allah ya baka lafiya kaji."

"Amin."
Chapter 5 · 0% Book details