← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 145

Sashe 99

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake* [6/30, 7:58 PM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyyah ta amshi wayar da Maheer ke mika mata ta saka numberta sannan ta mika masa tana mamakin wai yau Maheer ne da amsan numberta, is this for real?? Haseenah ta dauke kai daga kallonsu ta karaso parlon ta zauna babu yabo babu fallasa tana kallon TV, Maheer ya juya ya kalli Haseenah yace "Babu Dinner a gidan kenan?" A takaice tace "Breakfast din da nayi maka ma ai baka ci ba..." Yace "Ohk" Daga haka ya mike ya bar masu parlon, Badiyya ta zaro ido ta mike da sauri ta koma kusa da Haseenah ta rike haɓa tace "Kawata ki ji wani sabon salo wai Maheer da amsan numberta, wai nan fa duk so suke Hajja ta fara kula Ammi kamar da, sulhu kawai su ke so da ni fa" Haseenah tace "Atoh nima abun ya daure min kai" Badiyyah ta kyalkyale da dariya tana tafe hannu tace "Ai in dai zuga ne yanzu na fara, in aka ga na daina to babu Mayraah a familyn gaba daya" Da sauri ta ciro wayarta dake ringing tace "Yauwa gashi nan ya zo kawata, bari in tashi in tafi... " Haseenah tace "To sai yaushe kenan?" Badiyyah tace "Gobe asabar zanje Bichi wajen kawuna in masa karya akwai practical da za mu yi na final exams in amso kudi wajensa da zan cika ma malamin nan, kilan in dawo a goben, in kuma ban dawo ba sai Sunday in sha Allah" Haseenah tace "Toh shikenan za mu yi waya, duk yanda kawata suka yi da shi second Malamin zan sanar maki" Badiyyah na murmushi tace "To kawata nagode sosai" Mikewa tayi, Haseenah ma ta tashi ta rakata har bakin gate sannan ta dawo gidan, dakin Maheer ta tafi ta ga baya ciki, dama tun da aka kawota a dakinsa ta tare, nata kuwa sai jefi jefi take shiga ko in tana bukatar wani abu ko in zata yi waya, bata gansa cikin dakin nasa ba, ta leka nata nan ma baya nan, ta fito da mamaki ta tsaya corridor tana kallon kofar dakin Mayraah, babu tantama yana ciki tunda bai fita daga gidan ba, karasawa tayi ta kasa kunne amma bata jin komai, fita tayi daga gidan gaba daya ta zaga ta bayan window din Mayraah nan ma ta kasa kunne, ba abinda take gani kuma bata jin komai saboda window a kulle yake sannan curtains din ba a bude suke ba, nan da nan taji zuciyarta na tafarfasa ta dawo cikin gida, kawai ta nufi kofar dakin ta bude, Mayraah na zaune kan darduma with her handouts, shi kuma yana duke gabanta explaining something to her from the handout, duk suka juya suna kallonta, kallon sama har kasa ta dinga masu kafin ta juya ta bar bakin kofar dakin without saying a word, Maheer ya karasa bayanin da yake ma Mayraah yace "Hope kin gane yanzu?" Ta gyada masa kai, mikewa yayi zai fita ta daga kai ta kallesa, a hankali tace "Yaya dama..." Juyowa yayi ya kalleta yace "Dama me?" Ta sunkuyar da kai, ya dawo ya duka gabanta yace "Talk to me Mimi, dama me?" Ta daga kai tace "Dr Musharraf will be coming" Shiru yayi yana kallonta hakan yasa ta sunkuyar da kanta, can yace "Coming to where?" Murya can kasa tace "Here" Calmly Maheer yace "Me zai zo yayi?" Ta dinga kallonsa ta ki cewa komai, ya girgiza kai yace "I don't think there is any need ki ci gaba da kula mutumin nan Mimi, ba aure za ku yi ba, kawai kuna bata ma kanku lokaci ne, babu amfanin ku ci gaba da wani mu'amala after all that happened, don haka i see no reason da zai zo gidana....." Nan da nan hawaye ya cika idonta tace "To ai ba rabuwa muka yi ba yaya, beside...." Sai kawai ta fashe da kuka tace "Ni ina sonsa" Maheer ya dinga kallonta, mikewa yayi yace "To ki cire sa a ranki don baza ku taɓa aure ba, kamar yanda iyayensa suka ce basa son auren to kema naki iyayen haka, you both should stop deceiving ur selves and face reality" Kuka kawai Mayraah take tana kallonsa, ya hade rai yace "And all this is going to stop after ur final exams" Yana kai wa nan ya fice daga dakin... Mayraah ta kara fashewa da kuka, ta dau wayarta ta kashe gaba daya ta mike ta hau kan gado ta kwanta tana ci gaba da kuka kamar ranta zai fita, ta kai kusan karfe sha biyun dare tana abu daya daga karshe bacci ya dauketa. Washegari da sassafe ta tashi da kumburarrun ido, tayi wanka ta shirya ta dau wayarta ta saka cikin jaka ta fice daga gidan wajen karfe bakwai da rabi.... A hankali ta bude kofar main parlor din gidan ta shiga, kamar ko da yaushe babu kowa parlon ta wuce sama direct fuskarta babu walwala, tana shiga parlon Ammi suka fara ido hudu da Usman dake zaune sai Mama Ladi da ta bararraje tsakar parlon ga tuwo malmala biyu a gabanta tana ci da katon cup cike da shayi, Mayraah na shiga parlon ta fashe da kuka ta zauna kasa ta kife kanta da kujera tana kara sautin kukanta, Mama Ladi ta saki salati ta matsar da kwanon tuwon gabanta da shayi ta mike tace "Ahau dama ba nace maku zamanta daga ita sai Sanisa a gidan nan bazai yiwu ba amma ku ka maida ni er banza mara makabuli, jiya jiyan nan na gama gaya ma Ammi nayi mafarki Sanisa ta ma Mera dukan tsiya, wai kawai matar nan sai ta kira Mashir a gigice tana tambayar Mera shi kuma sai yace mata suna asibiti tare, daga haka ta shashantar da mafarki na, to gashi nan dai ya tabbata dama bana mafarki a banza, kiri kiri aka ki barin inje gidan in sa ido saboda an maida ni tsohuwar banza, to gashi nan dai ta mata tsinannen duka hankalin kowa sai ya kwanta" Tuni Usman ya mike ya nufi Mayraah ya duka gabanta worriedly yace "Mimi me ya faru?? me aka maki??" taki dago kanta balle tace komai sai rusa kuka take kamar ranta zai fita, Mama Ladi ta figi zaninta dake linke ta warware ta yafa a jiki tace "Ai sai mu kama hanyar caji opis don ba mu ga ta zama ba, abinda nake ta gudu kenan aka kasa fahintata dama tunda naji Sanisar kawar Badiyyah ce hankalina ya tashi don ai ance abokin barawo barawo ne, to shi shegen Mashir din yana ina ta maki wannan aika aikan?" Ganin Mayraah taki dagowa balle ta amsa uban tambayoyin da yake jero mata kawai ya kai hannu ya dagota ya zaunar da ita gefen kujera, Mama Ladi ta nufi kofa da gudu tana cewa "Ita kuma wancan da taje ta makale ma miji bari inje in kwankwasa masu su fito ba lafiya, abinda nake ta hangowa gashi ya faru" Usman dake ta kallon Mayraah da ke kuka ya duka gabanta cikin kwantar da murya yace "Calm down Mimi now tell me what happened, me aka maki? Ke da waye?" Ta kallesa tana goge hawayen dake sauka idonta cikin rawan murya tace "Yaya ne" Da mamaki yace "Yaya?? Me ya maki?" Nan da nan expression din fuskarsa ya sauya yace "Gaya min abinda yayi maki?" ta kara fashewa da kuka ta ki cewa komai, mikewa Usman yayi yana kallonta yana jin kukan nata na damunsa, Ammi ce ta shigo parlon da sauri Mama Ladi na biye da ita a baya tana cewa "Gaba daya fuskar ta kumbura, tana dingishi ta shigo mana, dama kuma ba nace maki nayi mafarki ba" Ammi ta nufi Mayraah ta kamo hannunta hankali tashe ta zauna gefenta tana duba duk jikinta tace "What happened daughter? Me aka maki a gidan?" Cikin rawan murya Mayraah tace "Yaya ne" Ammi da Mama Ladi suka hada baki wajen cewa "Yaya???" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Shi Mashir din??" Dai dai nan aka bude kofar parlon duk suka juya, Maheer ya shigo, Mayraah ta turo baki ganinsa ta kara shigewa jikin Ammi, Mama Ladi ta nufesa tace "Mashir daga ka auri er iska sai kai ma ka zama ɗan iska? Fisabilillahi ne ta maka zaka mata wannan duka haka yarinya marainiya??" Maheer ya dinga kallon Mayraah da ta rufe fuskarta jikin Ammi, can kuma ta mike ta shige dakin Ammi tana turo baki, Ammi ta dinga kallon Maheer tana jiran jin abinda zai ce don ita dai tasan bazai kai ma Mayraah hannu ba don bai taɓa ba, Usman ya bi Mayraah cikin dakin, zaune ya sameta kasan carpet fuskar nan nata a murtuke, yace "Me ya maki?" Cikin rawan murya tana goge idonta tace "Wai Dr Musharraf ne zai zo jiya ya hana sa..." Tana kai wa nan ta fashe da wani sabon kuka, Usman ya dinga kallonta babu ko kiftawa, kafa taga ya saita zai haureta ta bar wajen da sauri ta shige bandakin Ammi ta kulle, fita yayi daga dakin ya fice daga part din gaba daya, Mama Ladi ta nemi kujera ta zauna ta saki salati tana kallon Maheer tace "Aa to Mera ta zama abar tsoro, meye hadinta da mutumin da iyayensa suka zo nan suka ci mutuncin iyayenta? Kaca kaca fa mutanen nan suka mana ko furfura basu duba ba, to ko dai baku bata labarin abinda danginsa suka yi ranan da suka zo kwace lefensu bane?? Yanzu ko maza sun kare a duniya ita har zata tsaya ta kalli mutumin nan balle har ta sauraresa, ko don ba iyayen da suka haifeta aka yi ma cin mutunci ba shi yasa ko a jikinta? Kai ma dai Mashir har da naka, ai da shiru zaka yi mata ka bari mutumin sai ya zo har kofar gidanka kayi maza ka kira masa yan sanda su garkame sa, to in ba
Chapter 99 · 0% Book details