Sashe 9
Mayrah Complete Hausa Novel · about 4 min read
da yaran makota sun shigo kallon cartoon, Hajja na ganin Usman tace "To duk ku tashi ku tafi jikana ya zo, maza ku tafi" Babu wanda ya motsa cikinsu kamar basu ji ta ba, Usman yace "Kai ba magana ake maku ba" lokaci daya duk suka mike suka fita, Hajja ta marairaice tace "Ni na gaji da wahala gaskiya, kaga da baka sa baki ba wllh baza su tashi ba, ko na koresu basa tafiya sun maida ni wata mara makabuli, kakanninsu na can suna hutawa ni kuma sai a zo nan a dameni a cika min parlor har da almajirai, tunda suka kyallara ido suka ga Badiyya ta fita duk suka shigo" Hajja ta zaro ido ganin Mayraah tace "Dama tare ku ke, sannunku da zuwa, ai ko kin cika alkawari" Mayraah na murmushi ta karasa ta zauna kusa da Hajja ta gaidata, Hajja ta amsa da fara'a tace "Ina Ammin taki" Mayraah tace "Tana gaisheki" Usman ya zauna yace "Ina kwana Hajja" Hajja tace "Lafiya lau ya aiki" Yace "Alhamdulillah" Bude kofar parlon aka yi sai ga Badiyya ta shigo, Usman ya bi ta da ido kamar zata wuce sai kuma tace "Ina kwana yaya Usman" Yace "Lafiya lau" Mayraah na kallonta tace "Ina kwana Aunty Badiyya" Tuni Badiyya har ta shige daki, Hajja ta girgiza kai murya can kasa tace "Na gaji da yarinyar nan, ko sallama fa bata min ba ta fita, yau da asuban fari naga tana ta hada akwatunanta na kasa hakuri na leka daki nace ina kuma zata, wai zata koma gidanku..." Sosai gaban Mayraah ya fadi tana kallon Hajja, Usman yace "Zata koma gidanmu tayi me?" Hajja ta rufe baki da sauri tace "Kul kar ka sake cewa haka, ba fa bare bace, yar uwarka ce ta jini, don tace zata koma gidanku ai ba wani abu bane, nasan babu abinda Mamuda zai ce kuma bazai hana ta zauna masa a gida ba, tun yaushe ake son ta koma can din don ku sa mata ido ta rage abubuwan da take amma fir taki, tunda yanzu Allah ya so mu don kanta ta dawo tace zata sai a bar ta ta tafi kawai, dama anjima nake son kiran Ammi" Usman yace "Karya take yi, akwai wani munafurcin da take kullawa, banda haka bazata ce zata dawo gidanmu ba" a fusace Hajja tace "O'o Allah mu yi mata kyakkyawan zato mana Usman" Usman yace "Allah ya kawo ta lafiya, dama zuwa nayi in gaisheki na kwana biyu ban zo ba, yanzu sauri nake zan tafi Zaria" Hajja tace "Ai ko nagode Allah maka albarka" Dubu goma ya ciro a aljihunsa ya ajiye mata, ta dinga sa masa albarka, ya mike yace "Ni zan tafi saboda ana jirana bani kadai zan je Zarian ba" Hajja tace "To maza kaje Allah ya tsare, ke Mayraah ai kina nan har gobe ko" Usman yace "Aa tare za mu koma gida yanzu" Hajja tace "Tare kuma? Saurin me take" Usman ya kalli Mayraah yace "Tashi mu je" Mikewa tayi tace "Hajja in sha Allahu zan dawo ni kadai" Hajja dai bata ce komai ba, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Wato Ammi ce tace kar ki zauna ko??" Usman yace "Ai ke dama kin iya zarge zarge a ranki" Mayraah tace "Bata ce haka ba Hajja, kawai akwai wani aiki da nake yi na makaranta ne" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Badiyya ta fito da akwatunanta uku tana turasu, Hajja ta mike tace "Tafiyar kenan Badiyya?" Ba tare da Badiyya ta kalleta ba tace "Eh" Hajja tace "To ai kawai sai ki bi su Usman su ma gida za su tafi yanzu" Usman yayi saurin cewa "Wani Usman din?" Hajja ta kallesa baki bude, lokaci daya ta hasala tace "Wai me ku ka dau Badiyyar nan ne? Bare ko me? Er kanwar uwarka ce fa uwa daya uba daya, kwata kwata kun dauki tsangwama kun yafa ma yarinya marainiya ba uwa ba uba" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Usman ya fice daga parlon ita dai Mayraah ta kasa motsawa daga inda take, Usman ya leko parlon ganin Mayraah bata biyosa ba yace "Ke me kike jira Malama" Mayraah ta sauke idonta kasa ta nufi kofa, Hajja ta dau dubu gomansa da sauri cikin kuka tana mika masa tace "Gashi bana so ka kara fetur a hanyar Zaria" ko juyawa shi dai bai yi ba har ya fita, Mayraah dai sai bin sa take don bata son yayi mata masifa.....